Ta yaya ɗaukewar jinin al'ada ke shafar ƙwakwalwar mace?

Mace zaune tana riƙe da ƙanta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata na shafe kashi 25 zuwa 40 na rayuwarsu suna al'ada.
    • Marubuci, Samia Nasr
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • Lokacin karatu: Minti 3

Al'ummomi da dama na ganin ɗaukewar jinin al'ada shi ne karshen ƙarfi ko jin daɗin mace, wanda ke saka mata da yawa su kasance cikin wani hali idan suka kai matakin - inda suke fargaba kan alkalancisu da za a yi idan suka faɗi halin da suke ciki.

Wasu lokuta, saboda rashin wayar da kai da kuma ilimi, mata da yawa ba sa gane cewa akwai alaƙa tsakanin alamomin da suke gani da kuma ɗaukewar al'ada.

Duk da irin yawaitar ganin alamomin ɗaukewar al'ada da kuma jefa lafiyar mata cikin wani hali a wasu lokuta, bincike ya yi kaɗan a wannan ɓangare sakamakon rashin kuɗaɗe kuma ba a lura da batun. Ɗaukewar al'ada ba jikin mace kaɗai yake shafa ba, har ma ƙwakwalwarta.

Mene ne illolinta? Ta yaya suke afkuwa? Akwai hanyoyi na ƙauce wa hakan don inganta lafiyar mata da suka kai matakin?

"Jahannamar mata da mutuwar jima'i"

An fara mayar da hankali kan ɗaukewar al'adar mata ne a ƙarni na 20, sai dai an shafe tsawon lokaci kafin gano yadda yake shafar lafiyar mata.

Menopause mataki ne na manyantar mace da za ta daina yin al'ada.

Kuma mace na shiga wannan mataki ne idan ta yi tsawon watanni 12 ba tare da ganin jinin al'ada ba.

A yayin da mace take girma tana al'ada, yawan jakar miliyoyin kwayayen da ke jikinta na raguwa har zuwa lokacin da za ta shiga matakin da al'adar za ta ɗauke baki daya.

Ɗaukewar jinin al'ada da ake kira Monopause a turance ba cuta ba ce, illa lokaci ne da idan shekarun mace sun kai zai same ta.

Mace kan shiga mataki na menopause da karfinta ba sai ta tsufa ba.

Lokaci ne da mace za ta ji ba ta sha'awar namiji saboda raguwar wasu sinadarai da suke taimakawa jini da ake kira Oestrogen.

Akwai alomomi da dama da mace za ta fuskanta a lokacin da ta shiga mataki na Menopause.

Yadda Menopause ke shafar kwakwalwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bincike ya yi kiyasin cewa aƙalla kashi 10-15 na mata ba sa fuskantar alamomin ɗaukewar al'ada. Sai dai, da yawa daga ciki a fuskantar alamomi daban-daban, ciki har da wanda yake shafar kwakwalwa.

Sai dai hakan ya bambanta daga mace zuwa mace. Alamun da mata da dama ke gani na tsananta sosai har su ji babu abin da yake musu daɗi.

A shekarun 1990 ne masana kimiyya suka gano yadda raguwar sinadaran da ke taimakawa jiki na Oestrogen ke shafar kwakwalwar mace. Masana kimiyya sun gano cewa sinadarin Oestrogen da ke jikin mata yana da muhimmanci ba ga haihuwa kaɗai, har ma ga aikin ƙwakwalwa.

Lisa Mosconi, masaniyya kan kimiyyar ƙwaƙwalwa da laƙa ta fara wallafa a farkon shekarar nan yadda ƙwaƙwalwar mace ke sauyawa lokacin ɗaukewar al'ada.

Mosconi ta faɗa wa BBC cewa "ƙwaƙwalwar wadda al'adarta ta ɗauke" wani abu ne da ake kira a lafiyance kan alamomin da mata da yawa ke fuskanta lokacin ɗaukewar al'adar.... alamomi kamar fitar da gumi da daddare, rashin barci, rashin tuna abu, rashin fahimta, ɓacin rai da kuma fargaba.

Kashi 80 na mata kafin ɗaukewar al'ada da kuma bayan ɗaukewarta sun ruwaito ganin irin aƙalla ɗaya daga cikin waɗannan alamomi.

A cewar Mosconi, Oestrogen "yana taka muhimmiyar rawa a ƙwaƙwalwa da kuma yadda yake aiki. Yana taimakawa sassan ƙwaƙwalwa da ke tuna abu da fahimta. Idan sinadarin Oestrogen ya ci gaba da raguwa lokacin ɗaukewar al'ada, zai shafi waɗannan ɓangarori ainun, abin da ke janyo rashin fahimta da kuma koyon abubuwa.

A cikin littafinta, Mosconi ta bayyana irin alfanun Oestrogen, ciki har da taimakawa garkuwar jiki, inganta lafiyar kashi da kuma samar da sabbin ƙawayoyin ƙwaƙwalwa.

Waɗannan alamomi na ɗaukewar al'ada na ɓacewa gaba-ɗaya bayan wani lokaci, kuma mata da yawa ba sa fuskantar matsaloli na tsawon lokaci.

Mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata na hawa mataki-mataki a rayuwarsu tun haihuwarsu har tsufa

Shin sauya salon rayuwa na rage alamomin Menopause?

Ba shakka zaɓar salon rayuwa mai inganci na taimakawa lafiyarmu a kowane irin matakin shekaru, musamman wajen ƙauce wa kamuwa da cutuka da dama. Sai dai, hakan yana da matukar muhimmanci idan aka kusa shekarun ɗaukewar al'ada, saboda lokaci ne da mace za ta fuskanci raguwar sinadarin jini na Oestrogen da kamuwa da ciwon zuciya da sauransu.

Ƙwararru da dama na ba da shawarar cewa yawaitan shan kayan lambu da ƙauce wa ko rage shan suga da nau'ukan abinci da aka sarrafa. Ya kunshi abincin da ke ɗauke da sinadarin fats da dangin yoghurt da kuma cin abinci mai sinadarin protein domin inganta lafiyar jijiyoyi.

Babu wani nau'in abinci da aka keɓe ko kuma motsa jiki da zai ƙawar da alamomin ɗaukewar al'ada, sai dai cin abincin da ke da sinadarin ƙarawa jiki lafiya," a cewar masaniyar.

Ta ƙara da cewa, "motsa jiki akai-akai, musamman wanda zai sa jiki ya yi aiki, na taimakawa lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma zuciya."