Yadda tsohuwar jarumar Kannywood ke gwagwarmaya da cutar kansa

Halisa Muhammad ta kasance ɗaya daga cikin manyan fitattun jarumai a shekarun farko-farko na Kannywood
Bayanan hoto, Halisa Muhammad ta kasance ɗaya daga cikin manyan fitattun jarumai a shekarun farko-farko na Kannywood
Lokacin karatu: Minti 4

Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da bayanai game da cuta, waɗanda za su iya sosa rai.

A lokacin da take tashe a tsakiyar shekarun 1990, Halisa Muhammad ta kasance mai tarin masoya sanadiyyar rawar da ta riƙa takawa a finafinan Hausa.

Bayan shekaru tana taka rawa a fim, sai aka daina jin ɗuriyarta, inda ta ɓace daga harkar, amma daga baya sai sunanta ya sake karaɗe yankin arewacin Najeriya, sai dai wannan karon ba domin rawar da take takawa a finafinai ba.

Sake bayyanar ta a shafukan sada zumunta da sauran kafafen yaɗa labarai ya faru ne sanadiyyar shekaru da ta kwashe tana dama da cutar kansar mama.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce kansar mama ita ce cutar dajin da aka fi ganowa a jikin mata a faɗin duniya, inda a 2022 cutar ta yi sanadin mutuwar mata dubu 670.

An ware watan Oktoba a matsayin lokacin wayar da kai game da cutar kansa a duniya, BBC ta tattauna da tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa Muhammad, wadda ta kamu da cutar, don ji irin ƙalubalen da ta fuskanta.

''Na fara ne da kumburin hammata, tun haihuwata ta farko, fiye da shekara 25, daga baya sai ya canza kamanni, ya fara ƙaiƙayi har ya isa kan nonona'', in ji ta.

'Alamomin da na fara gani'

Fitacciyar tauraruwar, wadda ta yi tashe a shekarun farko-farkon Kannywood ta ce ba a jima ba sai wasu alamomi suka riƙa bayyana a kan maman nata, da suka haɗa da kumburi da zubar da ruwa.

''Haka muka ci gaba da yin maganin Hausa a gida, kuma dama galibi idan irin haka ta kasance, mutane za su riƙa bayar da shawarwarin gwada wannan magani, kowa da irin tasa shawarar'', in ji ta.

Ta shaida wa BBC cewa daga ƙarshe dai ta yanke shawarar zuwa asibiti domin ganin likita.

''Amma mun je asibiti ne bayan abubuwa sun lalace, domin kuwa a lokacin ma maman nawa ya riga ya fashe', in ji tsohuwar jarumar.

'Rashin wayar da kai na ƙara dagula matsalar'

Tsohuwar jarumar ta ce ɗaya daga cikin matsalolin da masu lalurar kansa ke shiga a Najeriya shi ne rashin wayar da kai.

''Farkon tashin hankalin da muka shiga, shi ne ba mu san mece ce cutar kansa ba, ba mau san yadda take da irin haɗarinta ba'', in ji ta.

Hasila Muhammad ta kuma zargi likitocin Najeriya da rashin bayyana wa marasa lafiya ainihin cutar ba.

''Sannan ba sa gaya maka adadin shekarun da za ka ɗauka kana shan maganinta ba, sai dai kawai su riƙa yi maka magani, daga wannan sai wannan.''

'Mun shiga tashin hankali mai girma'

Tsohuwar jarumar ta Kannywood ta kuma koka kan irin tsadar da maganin cutar ke da shi.

''Mun shiga tashin hankali mai girma, da farko na fara sayar da gidan da nake ciki domin yi min magani a asibiti, ina ganin kamar na gama da wannan, ashe ban ga komai ba'', in ji ta.

Ta ci gaba da cewa a tsawon shekara uku zuwa huɗun da ta yi tana maganin wannan cuta ta kashe kuɗi fiye da naira miliyan 40.

''Na fara da allurai na naira 180,000 kowace guda ɗaya ta tsawon mako uku, bayan nan an rubuta min maganin da zan sha na tsawo mako uku, kuma alluran za ka yi kamar wata shida ka na yi'', in ji ta.

Tsohuwar jarumar ta ce bayan nan aka yi mata aiki, sannan aka rubuta mata wata allura da kowace guda ɗaya ana sayar da ita naira 520,000.

"Kuma wannan allura likitoci suka ce sai an yi min ita sau 18, muka fara bayan yin guda biyar kuɗi suka ƙare'', in ji ta.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon tattaunawar BBC da Halisa Muhammad

'Ƴan Kannywood sun tallafa min'

Tsohuwar Jarumar ta ce abokan sana'arta ƴan Kannywood sun tallafa mata a lokacin da aka ce za a yi mata aiki.

''Sun yi ƙoƙari sosai, domin sun tara min kuɗi wajen naira miliyan bakwai domin yi min magani'', kamar yadda ta bayyana.

'Cuta ba mutuwa ba'

Halisa Muhammad - wadda ta shafe fiye da shekara uku da rabi tana fama da cutar - ta ce abin da ya kamata masu ɗauke da cuita su sani shi ne cuta ba ta kawo mutuwa, kamar yadda Hausawa ke faɗi.

''Ciwon kansa ba ƙarshen rayuwa ba ne, ba a karaya, domin kuwa kina karaya kin rasa ƙwarin gwiwa'', in ji ta.

Ta ƙara da cewa abin da kawai mai lalurar ke buƙata shi ne samun ƙwarin gwiwa daga shi kansa da kuma mutanen da ke kewaye da shi.

''Abin da ake so shi ne ƙarfin imani, da sanin ƙaddara, komai ya faru da kai muƙaddari ne'', in ji ta.

'A yanzu na buɗe gidauniyar yaƙi da kansa'

Tsohuwar jarumar ta Kannywood ta zama jarumar yaƙi da cutar kansa, inda take kiraye-kiraye ga yan'uwanta mata su riƙa yawaita yin gwajin cutar a kai - a kai.

''Sankarar mama, babban ciwo ne, don haka kowane wata bayan ƙarewar al'adarki yana da kyau, ki tsaya gaban madubi, ki duba nonuwanki tun daga hammatarki, idan kika fahimci wani baƙon al'amari a jiki to ki gaggauta zuwa asibiti a yi miki gwaji'', in ji ta.

Halisa Muhammad ta ce gano ciwon kansa da wuri na daga cikin abubuwan da ke taimaka wa warkar da ita.

Alamomin cutar kansar mama

Hukumar lafiyar Birtaniya, NHS ta bayyana wasu alamomin da ta ce na cutar kansar mama ne da suka haɗa da:

  • Ganin kumburi ko kaurin nama a kan mamanki, wanda a baya babu shi.
  • Canjin girma ko yanayin mamanki ɗaya ko duka biyun.
  • Fitar da jini daga kan mama.
  • Kumburi ko ƙuraje a cikin ɗaya ko duka hammatarku.
  • Ƙuraje a kan fatar mama.
  • Ƙuraje a ɗan kan mama.
  • Canjin kamannin nononku, kamar ci gaba da raguwar girmansu.