Me ya sa matasa masu yin kwaskwarimar halitta ke ƙaruwa?

Asalin hoton, @hotgirlenhancements
- Marubuci, Ruth Clegg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and wellbeing reporter
- Lokacin karatu: Minti 7
Kwaskwarimar jiki ta samu sabbin kwastomomi.
Bincike mai sauƙi da aka gudanar a shafin sada zumunta ya nuna yadda matasa ƴan tsakanin shekara 20 zuwa 30 ke tattaunawa kan nau'uka daban-daban na kwaskwarimar gyaran fuska.
Lokaci ya wuce da za ka ga tsofaffin masu kudi ne kawai ke yin kwaskwarimar halittar jiki - yanzu matasa da dama sun yanke shawarar zuwa domin samun wannan kwaskwarima.
Wasu sun wallafa fuskukinsu suna kwatanta bambanci tsakanin gabani, da kuma bayan yin kwaskwarima, da kuma fafutikarsu ta warkewa daga kwaskwarimar.
Yanzu ma ba abu ne da ake ɓoyewa ba, ana tattauna irin wannan kwaskwarima a filin Allah. Akwai sanannun mutane da dama da suka fito suka yi bayani kan kwaskwarimar gyaran jiki da suka yi.
Kwaskwarimar ƙarin kyau da ake yi a fuska ana kallon shi a matsayin shawara ta ƙarshe da mutum zai so ya yanke.
Shin yanzu matasa ba su da ƙwarin gwiwa kan halittarsu ne da ya kai ga suna kashe maƙudan kuɗaɗe domin yi musu kwaskwarimar halitta?

Asalin hoton, @hotgirlenhancements
Emily, wadda aka yi wa tiyatar kwaskwarimar fuska tana da shekara 28 a duniya domin gyara mata girmar haɓa da ɗaga ƙashin kumatunta da kuma sauya launin idonta zuwa irin na dila, ta ce wannan tiyata da aka yi mata a ƙasar Turkiyya ya sauya rayuwarta kuma ba ta yi da-na-sani ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A jimilla an yi min tiyata shida ne a lokaci ɗaya," in ji ta. "Wato daidaita fuskata da ƙarin girman leɓɓa da kuma saita hancina."
Lokacin da take bayyana yadda aka yi tiyatar, matar wadda ƴar kasuwa ce daga birnin Toronto na Canada, ta ce likitan ya kunna mata waƙar da ta fi ƙauna gabanin yi mata allurar kashe jiki, daga nan: sai na yi bacci na tashi, na yi amai, kawai sai ga shi ina da sabon hanci da sabuwar fuska."
Lokacin murmurewar na da tsawo - amma zafin da tabban sun rage a cikin makonnin farko, sai dai sai da aka kwashe wata shida kafin jikin Emily ta dawo daidai.
Ko za ki iya sake yin wannan tiyatar? Sai ta yi shiru na wani ɗan lokaci.
"Tun bayan tiyatar da na yi, na sauya rayuwa. Yanzu na fi lafiya, na rage shan barasa, ina kula da fatata, kuma ina yin bacci sosai. Ina ganin inda a baya na san abin da na sani yanzu, ƙila da ban yi tiyatar ba.
"Mahaifiyata ba ta san zan yi ba, sai bayan ƴan kwanaki da yin tiyatar na fada mata."
Daga nan sai ta yi shiru na ɗan lokaci, ta ɗan yi tunani.
"To amma abin da na so shi ne na ƙure kamannin da zan iya samu," in ji Emily, "kuma yanzu ina ganin na ƙure."
Bayanai daga ƙungiyar likitoci masu yin kwaskwarimar halittar jiki ta Birtaniya sun nuna cewa an samu ƙarin yawan masu yin kwaskwarimar halitta da kashi 8% a cikin shekara ɗaya da ta gabata a Birtaniya.
Duk da cewa ba su karkasa waɗanda ake wa tiyatar ba ta hanyar la'akari da shekarunsu, to amma bayanai sun nuna cewa ana samun sauyi.
Irin hakan ne kuma ake samu a wasu sassan duniya, inda ƙungiyar likitoci masu yin tiyatar kwaskwarimar jiki ta ce ana samun ƙaruwar mutane ƴan shekara 45 zuwa 60 masu son a yi musu kwaskwarimar halitta.
Nora Nugent, wadda ita ce shugabar ƙungiyar masu kwaskwarimar halitta a Birtaniya ta ce akwai dalilai da dama da ke haifar da hakan - ciki kuwa har da yawaitar magungunan rage ƙiba.
"Rage ƙiba cikin ƙanƙanin lokaci zai sa fata ta takure. Kwaskwarimar halitta za ta iya magance hakan," in ji ta. "An fito da dabaru masu yawa." In da ta nuna cewa ba a samun matsaloli kamar yadda aka gani a baya.

Asalin hoton, Getty Images
However, a facelift is still a significant operation that should only be undertaken by a specialist, registered plastic surgeon in a registered facility with proper equipment, she says.
Sai dai, yin tiyatar kwaskwarimar jiki abu ne mai muhimmanci wanda bai kamata wani ya yi ba sai wanda ya ƙware, wanda yake da rajista kuma wanda ke da ƙwararren asibiti da kayan aikin da suka dace, in ji ta.
A asibitinsa da ke Bristol a Birtaniya, ƙwararren likitan kwaskwarimar halitta Simon Lee ya gudanar da ayyukan kwaskwarimar jiki bila adadin - kuma ya nuna wa wakilin BBC bidiyon ɗaya daga cikin wannan tiyata.
Daga farko zuwa ƙarshen tiyatar wadda aka yi mawa tana cikin hayyacinta, bayan da aka yi mata allurar kashe zafi a sama-sama da kuma can ƙasan fatarta.
Ya yi yanka ƙanana a samun fatar fuskarta kafin daga baya ya shiga zuwa ƙarƙashin fata, inda daga can ciki ya sassauya wa wasu tsokokin fuskarta mazauni.
Bayan kammalawa, wadda aka yi wa tiyatar ta tsawon sa'a huɗu, ta yi murmushi don nuna murnar kai ƙarshen tiyatar.
Mista Lee ya ce ɗaya daga cikin abin da ya sa tiyatar kwaskwarimar jiki ke samun karɓuwa shi ne yadda yin aikin ya zama mai sauƙi a yanzu.
A baya akan yi hakan ne kawai a asibitoci na musamman tare da yin allurar kashe zafi na musamman, to amma yanzu yana yin irin wannan aiki a asibitinsa ba tare da yin allurar bacci ba.
Likitan ya ce kwaskwarimar gayaran halittar fuska abu ne da ya fi dacewa da mutane ƴan shekara 40 zuwa sama, domin abin zai zama bambaraƙwai a yi wa ƴan shekara 20 ko 30 irin wannan tiyata.
Akwai haɗurra sosai da ke tattare da irin wannan tiyata, waɗanda suka hada da taruwar jini a wajen jijiya, wanda idan ba a kula da kyau ba zai iya haifar da matsalar fatar da ke zagayen wurin da kuma shigar ƙwayoyin cuta da yin illa ga manyan jijiyoyi da kuma lalurar rashin tsirar gashi.
Kuɗin tiyatar gyara halittar fuska na kamawa ne daga fam 15,000 zuwa fam 45,000 a Birtaniya, sai dai akwai wasu asibitocin da ke yin irin wannan aiki kan kuɗ ƙalilan, kimanin fam 5,000.
Masana sun ce ya kamata mutum ya yi bincike sosai sannan ya zaɓi likitan tiyatar kwaskwarima wanda ya ƙware sosai.

Asalin hoton, Julia Gilando
Julia Gilando, mai shekara 34 a duniya ta yanke shawarar yin kwaskwarimar halittar fuskarta ne domin gyara wata ƴar karkacewa a fuskarta wadda ta faru tun tana yarinya.
Duk da cewa da yawa daga cikin ƙawayenta sun ce su ba su ga wata matsala tattare da fuskarta ba, ita tana jin abin, kawai sai ta yanke shawara, ta hau jirgi ta tafi Turkiyya domin yin tiyatar, wadda aka yi mata a kan kuɗi dala 8,000.
Duk da gargaɗin da ake yi na haɗarin da ke tattare da yin kwakskwarimar halitta a Turkiyya, ana samun ƙaruwar mutane da ke zuwa ƙasar domin yin tiyatar, musamman saboda arharsa a can.
Haka nan kuma akwai damuwa kan ko tiyatar kwaskwarimar halitta na samar wa waɗanda ake yi mawa gamsuwar da suke tunanin za su samu, kamar yadda ake tallatawa.

Asalin hoton, Caroline Stanbury
Caroline Stanbury, mai gabatar da shirye-shieyrn talabijin ta yi tiyatar kwaskwarimar halitta shekara biyu da suka gabata, lokacin tana ƴar shekara 47 a duniya, duk kuwa da cewa mutane da dama sun shawarce ta kada ta yi saboda tana da sauran ƙuruciya.
"Wannan ne abu mafi muhimmanci da na yi," in ji Caroline. "Me zai sa na jira sai na kai shekara 60, duk kuwa da cewa ina so na yi? Ina so na ji daɗi na kuma burge a yanzu."
Wani likita mai yin kwaskwarimar halitta a Belgium, Alexis Verpaele, wanda ke da masu zuwa wajen shi daga sassa daban-daban na duniya, ya ce ya damu kan ƙaruwar yawan matasa da ke zuwa domin yin irin wannan tiyata.
Yakan kwashe lokaci yana bai wa irin waɗannan matasa shawara kan wasu hanyoyin da za su iya bi domin ƙara wa kansu kyau ba tare da sun yi irin wannan tiyata ba.
"Idan aka yi musu tiyatar kwaskwarimar fuska lokacin suna kimanin shekara 20, mun san cewa abin da aka yi zai iya daɗewa zuwa shekara 10 zuwa 15.
"Saboda haka a lokacin da suka kai shekara 60, zai zama ke nan sun yi irin wannan tiyata sau uku," in ji Verpaele.
Wannan ba ƙaramin tashin hankali ne fuska za ta gani ba - kuma haka din ma idan har ba a samu wata matsala ba ke nan."










