Yadda gurbatar muhalli ke janyo matsalar haihuwa tsakanin maza

.

Da alama ƙarfin maniyyi na raguwa a sassan duniya amma batu ne na rashin haihuwa da aka tattauna a kai. Yanzu masana kimiyya sun taƙaita kan abin da ka iya zama silar matsalar.

"Muna iya warware shi. Ba matsala. Za mu iya taimaka maki,: in ji likita Jennifer Hannington. Sai kuma ya koma kan mijinta, Ciaran, inda ya ce: "Amma ba wani gagarin abu ne za mu yi ba,"

Ma'auratan da ke zaune a Yorkshire da ke Ingila, sun shafe shekara biyu suna ta ƙoƙarin samun haihuwa.

Sun san cewa watakila yana iya zama abu mai wahala Jennifer ta ɗauki ciki saboda tana da cutar da ake kira polycystic ovarian syndrome - wata matsala da ke shafar haihuwa.

Abin da ba su yi tsammani ba shi ne akwai matsaloli a ɓangaren mijinta.

Gwaje-gwaje da aka yi sun nuna matsaloli da suka haɗa da rashin fitar da isasshen maniyyi da matsalar haɗuwar maniyyi da ƙwan mace.

Mafi muni shi ne ana tunanin waɗannan matsalolin za su fi wahalar warkarwa a kan na Jennifer - ko ma ba zai yiwu ba.

Har yanzu Hannington na tuna yadda ya karɓi abin: "Kaɗuwa da baƙin ciki. Na kasa yarda da lamarin.

Na yi tunanin likitocin sun yi kuskure," Ya san ya daɗe yana son ya zama uba. "Na ji kamar na gaza a wajen matata."

Tsawon shekaru, lafiyar ƙwaƙalwarsa na raguwa. Sai ya soma zama cikin kaɗaici, ya kuma koma shan barasa domin samun sauƙi. Sai kuma ya soma firgita.

Ya kai matsayin da ya zama matsala," in ji shi.

Matsalar haihuwa a wajen maza na da nasaba da kusan rabin matsalolin haihuwa da ake samu, sannan yana shafar kashi 70 cikin 100 na mazan duniya.

Sai dai, ba a cika magana a kai ba kamar mata, wataƙila saboda yanayin al'ada da ke kewaye da batun.

Ga galibin maza masu matsalar haihuwa , har yanzu matsala ce da ba a yi bayaninta ba - kuma ƙyama na nufin mutane da dama na fama a ɓoye.

Bincike na nuna cewa matsalar wataƙila na ƙaruwa.

Dalilai da suka haɗa da gurɓatar yanayi sun nuna suna shafar haihuwa a ɓangaren maza musamman ingancin maniyyi da kuma gagarumar illa ga mutane da al'umma baki ɗaya.

Ɓoyayyiyar matsalar haihuwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yawan al'ummar duniya ya ƙaru sosai cikin ƙarnin da ya gabata. Shekaru 70 da suka gabata - cikin rayuwar bil adama - akwai mutum biliyan 2.5 a duniya.

A 2022, yawan al'ummar duniya ya kai biliyan takwas.

Sai dai, yawan ƙaruwar al'ummar duniya ya ragu galibi saboda matsaloli na rayuwa da tattalin arziki.

Yawan haihuwa a faɗin duniya na raguwa. Sama da kashi 50 cikin 100 na al'ummar duniya suna rayuwa a ƙasashe da yawan haihuwa zuwa ƴaƴa biyu ga kowace mace - abin da ke janyo raguwa a yawan al'umma musamman idan ba a yin hijra.

Dalilan da ke janyo wannan raguwar a yawan haihuwa sun haɗa da ci gaba mai amfani kamar kasancewar mata masu tsayawa da ƙafarsu da kuma samun iko kan lafiyar ƙwayayensu.

A wani ɓangaren kuma, a ƙasashe da ake samun ƙarancin haihuwa, galibin ma'aurata na son samun ƙarin yara, kamar yadda bincike ya nuna, amma suna iya fasawa saboda dalilai na zamantakewa ko tattalin arziki da rashin samun goyon baya ga iyalai.

.

Asalin hoton, Yuichi Yamazaki/AFP/Getty Images)

Akwai kuma wataƙila raguwa a wani tsarin haihuwa na daban da ake kira 'fecundity' a Turancin Ingilishi - ma'ana, ikon mutum na samun ɗa ko ƴa.

Bincike ya nuna cewa matsalolin haihuwa a tsakanin maza na ƙaruwa ciki har da yawan maniyyi da raguwar sinadaran halitta na maza wato testosterone da kuma ƙaruwar matsalar miƙewar gaba da kansar da ke shafar maraina.

Ƙwayoyin halittu masu motsi

"Maniyyi muhimmin tantanin halitta ne," in ji Sarah Martins Da Silva, wata masaniya a fannin haihuwa a Jami'ar Dundee kuma likitar mata.

"Ƙananu ne, suna yawo, suna kuma iya rayuwa a waje bayan fitar da shi. Babu wata ƙwayar halitta da ke iya yin haka."

Ƙananun sauye-sauye na iya haifar da gagarumin tasiri kan waɗannan ƙwayoyin halittu musamman ikon da suke da shi na ƙyanƙyashe ƙwai.

Muhimman al'amuran da suka shafi haihuwa shi ne ikonsu na motsawa, da surarsu da kuma girmansu da kuma yawansu cikin maniyyi. Sune abubuwan da ake dubawa idan namiji ya je gwajin haihuwa.

"Idan ka samu maniyyi ƙasa da miliyan 40 kan kowane milimita na maniyyin, za ka fara ganin matsalolin haihuwa," in ji Hagai Levine, Farfesa kan nazarin cututtuka a Jami'ar Hebrew ta Birnin Ƙudus.

Levine ya yi bayani cewa yawan maniyyi na da alaƙa ta ƙut da ƙut da damar haihuwa. Sai dai samun yawan maniyyi ba shi ke tabbatar da yiwuwar samun haihuwa ba.

A 2022, Levine da abokan aikinsa sun wallafa wani nazari kan yawan maniyyi. Ya nuna cewa yawansa na kasancewa da kashi 1.2 cikin 100 a kowace shekara tsakanin 1973 zuwa 2018 daga miliyan 104 zuwa 49 kowace milimita.

Daga shekarar 2000, raguwar ta ƙaru zuwa fiye da kashi 2.6 cikin 100 duk shekara.

Levine ya ƙara da cewa wataƙila ƙaruwar na iya kasancewa sanadin sauye-sauyen da suka shafi muhalli da ɗabi'a, ma'ana, gyare-gyare kan yadda halittun gado ke aiki, sakamakon muhalli da ɗabi'un tafiyar da rayuwa.

Wani nazari na daban ya nuna halittun gado na iya taka rawa a sauyin da za a gani a maniyyi da matsalar rashin haihuwa a tsakanin maza.

Bincike ya nuna cewa matsalar rashin haihuwa a maza na iya bayyana wasu matsalolin lafiya a gaba duk da cewa har yanzu ba a kai ga fahimtar alaƙar ba.

Abu mai yiwuwa shi ne tsarin rayuwar mutum na iya janyo rashin haihuwa da wasu matsalolin da suka shafi lafiya.

"Yayin da kasancewar neman haihuwa da rashin samun juna biyu ke da matuƙar tayar da hankali, wannan babbar matsala ce," in ji Da Silva.

Gurɓacewar muhalli

Rebecca Blanchard, wata mai nazari a Jami'ar Nottingham da ke Birtaniya tana binciken tasirin sinadaran da ake gani a cikin gida kan lafiyar maza. Tana amfani da karnuka a matsayin gwaji - wata ankararwa ga lafiyar bil’adama.

"Karen na rayuwa a muhallinmu," in ji ta. "Yana zama a gida ɗaya kuma yana shaƙar sinadarai kamar mu.

Idan muka duba karen, za mu iya ganin abin da ke faruwa ga bil’adama."

Bincikenta ya mayar da hankali kan sinadaran da ake gani a robobi da abin kashe gobara da sauran abubuwan da ake samu a gida.

An haramta amfani da wasu daga cikin sinadaran amma har yanzu ana ganinsu a muhalli ko abubuwan da suka tsufa.

Bincikenta ya bayyana cewa waɗannan sinadaran suna iya ruguza tsarin sinadaran ƙarfafa haihuwa ya kuma illata yiwuwar haihuwar karnuka da maza.

"Mun gano raguwa a motsawar maniyyi a tsakanin bil’adama da kare," in ji Blanchard."

.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Tsarin dashen kwai mai suna IVF na samar wa ma'auratan da ke da matsalar haihuwa fata sai dai yana da tsada kuma ba kowa ake iya yi wa ba

Binciken ya yi daidai da sauran nazarce-nazarce da ke nuna illar da yake yi wa haihuwa sakamakon sinadaran da aka gano a jikin robobi da magungunan kula da cututtuka da abinci da kuma iska.

Ya shafi maza da mata da ma jarirai. Iskar carbon da sinadarai duk an gano suna iya kai wa ga jarirai a ciki.

Sauyin yanayi na iya yin mummunan tasiri kan ikon maza na iya haihuwa inda bincike da dama da aka yi kan dabbobi suka nuna maniyyi na da rauni kan tasirin ɗumamar yanayi.

An bayyana zafi yana yin illa ga maniyyi a ƙwari sannan an lura da makamancin wannan tasirin ga bil adama.

Wani bincike da aka yi a 2022 ya gano yanayin zafi sakamakon ɗumamar yanayi ko ma aiki a cikin yanayin zafi, na yin mummunan tasiri kan ƙarfin maniyyi.

Rashin abinci mai gina jiki da gajiya da barasa

Baya ga waɗannan matsaloli da suka shafi muhalli, matsalolin da suka keɓanta ga mutum na iya janyo matsala ga maza a ɓangaren haihuwa kamar rashin abinci mai gina jiki da rashin motsa jiki da gajiya da barasa da amfani da ƙwayoyi.

A shekarun baya-bayan nan, an samu sauyi game da mutanen da ke zama iyaye a rayuwa - kuma yayin da mata ake yawan tuna musu batun ƙurewar shekaru, ana ganin shekaru ba su da wani illa ga haihuwa a tsakanin maza. Yanzu, lamarin na sauyawa.

Ana ganin ƙaruwar shekarun iyaye maza na da alaƙa da rashin ƙarfin maniyyi da raguwar haihuwa.

Akwai ƙaruwar kiraye-kiraye kan a fahimci matsalar haihuwa a tsakanin maza da kuma sabbin hanyoyin magance ta da gano ta da kuma warkar da ita - da kuma ƙaruwar faɗakarwa kan buƙatar magance matsalar gurɓatar muhalli.

Shin akwai wani abu da mutum zai iya yi domin karewa ko inganta ƙarfin maniyyinsu?

Motsa jiki da samun abinci mai inganci na iya zama mafari mai kyau tun da an alaƙanta hakan ga ingantuwar ƙarfin maniyyi.

Blanchard ta bayar da shawarar a yi amfani da abincin da ba a sarrafa da sinadarai ba da kuma kayayyaki marasa BPA (Bisphenol A), wani sinadari da ake dangantawa ga matsalolin haihuwa tsakanin maza da mata.

"Akwai ƙananan abubuwa da za ka iya yi," in ji ta.

Hannington kuma ya ce kar mutum ya yi gum da bakinsa.

Bayan shekara biyar yana samun kulawa da kuma yin allurar ICSI (Intracytoplasmic Sperm Injection) har sau uku, wani tsarin dashe ne da ake yin allurar maniyyin namiji a tsakiyar kwan mace, shi da matarsa suna da yara biyu.

Ga mutanen da sai sun biya da kansu a yi musu maganin haihuwa, irin wannan tsarin ba shi da sauƙin kuɗi.

A Amurka, yin tsarin IVF sau ɗaya kawai na iya kaiwa dala 30,000 sannan samun inshora da ya ɗauke tsarin IVF ya danganta ga jihar da mutum ke zaune ko kuma wurin da kake aiki.

Sannan Hannington ya ce har yanzu yana jin irin wahalar da ya sha.

"Ina godiya ga ƴaƴana a kowace rana, amma kar ku manta," in ji shi. "Zai ci gaba da zama wani ɓangare na rayuwata."