An gano dajin da ya fi shekara miliyan huɗu a duniya

Man walking on a cliff with fossils

Asalin hoton, Neil Davies

Masana kimiyya sun gano wani wuri da suka yi amannar shi ne daji mafi daɗewa a duniya, mai ɗauke da wasu bishiyoyi a kudu Maso Yammacin Ingila.

An gano shi ne a saman wani tsauni kusa da Minehead, Somerset da ke kusa da wani sansannin Butlin da ake zuwa hutu.

Masu bincike daga jami'ar Cambridge da Cardiff sun ce bishiyoyin da aka gano su ne mafi daɗewa a Burtaniya kuma su aka sani mafi daɗewa a yanzu a duniya.

An fi sanin bishiyoyin da Calamophyton tana kama da bishiyar kwakwar manja.

An kwatanta ta da bishiya mafi tsayi a duniyarmu ta yau, inda ta kai tsayin mita biyu zuwa hudu.

Kazalika sun bayyana bishiyoyin da tsayin jijiyoyi da kuma tsari na daban.

Sun fito da bayanan yadda bishiyoyin suka taimaka wajen riƙe kasa, suka kuma fitar da zanen gaɓar tekun na tsayin daruruwan shekaru da suka gabata.

"Lokacin da na fara ganin hoton bishiyoyin nan da nan na gano yadda suke, saboda kwashe shekara 30 da na yi ina karantar irin waɗannan bishiyoyin a faɗin duniya," in ji Dr Christopher Berry na makarantar nazarin ƙasa da kimiyyar muhalli a Cardiff.

"Abin birgewa ne ganin irin waɗannan bishiyoyin a kusa da gida. Amma abin ba da labarin shi ne yadda ake kallon su idan an ɗaga kai sama, kuma sun girma a wuri mai kyau."

Fossil marks in the cliff with a tape measure to indicate the scale

Asalin hoton, Chris Berry

Dr Paul Kenrick wanda kwararre ne a gidan tarihi na Natural History, amma ba ya cikin binciken, ya ce wannan ya bayar da haske kan yadda tsirrai ke girma tare na tsayin lokaci.

Masu binciken sun ce dajin ya girmi na New York da a baya ya fi kowanne tsufa da wajen shekara biliyan huɗu.

Masu binciken sun ce yankin da aka gano dajin a baya yana yawan bushewa amma akwai hanyoyin ruwa a tare da shi, amma ba ya tare da Ingila, amma wani sashen shi na Jamus da Belgium, inda aka fi samun irin waɗannan bishiyoyi.

Cliffs jutting out into the sea

Asalin hoton, Neil Davies

"Wannan daji ne mai ƙayatarwa, ba kamar kowanne irin daji da muke gani ba a yau," in ji Farfesa Neil Davies na sashen kimiyyar ƙasa da ke Cambridge, wanda shi ne marubucin binciken na farko.

"Babu wata ciyawa ko wani tsiro da za mu yi magana a kan shi wanda bai bayyana ba yanzu, amma akwai wasu tsirrai da dama da suke da matuƙar tasiri ga kwarin ƙasa."

Dr Kenrick ya ce bishiyoyin na da banbanci daga waɗanda muke gani a yau. Wacce za a ce suna yanayi ita ce Dicksonia da ake samu a yankin antarctica, wata ƙalar bishiya da aka riƙa samu a Australiya, amma an fi ganin ta a Birtaniya.

Dicksonia antarctica ferns growing

Asalin hoton, Getty Images