Ɗabi'u 6 da za su iya illata mafitsararku da yadda za ku sauya su

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana iya kauce wa mafi yawan matsalolin rayuwa, kuma sun danganci wasu ɗabi'unmu
    • Marubuci, Dipa Kamdar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Conversation*
  • Lokacin karatu: Minti 4

Mafitsara na daga cikin abubuwan da galibi ba a fiya kula da lafiyarsu ba, har sai sun fara samun matsala.

Wata ƴar ƙaramar halitta ce mai siffar jaka da ke ƙarƙashin hanyar fitsari, da ke ajiyewa tare da sakin fitsari, domin taimaka wa jiki fitar da gurɓataccen ruwa.

Kamar dai ziciya ko huhunmu, mafitsara na buƙatar samun kulawa. Watsi da ita zai iya haifar da matsala da ciwon da ya shafi fitsari, sannan a wasu lokutan lamarin kan haifar da mummunan yanayi na kasa riƙe fitsari da rashin fitsarin a wasu lokutanma yakan haifar da cutar kansa.

Sai dai wani babban abin murna shi ne: Duka cutukan mafitsara ana iya magance su, kuma suna da alaƙa da wasu ɗabi'u da muke yi yau da kullum.

Ga wasu ɗabi'u shida da muke yi waɗanda za su iya cutar da mafitsararmu.

1. Riƙe fitsari na tsawon lokaci

Jinkirta yin fitsari na haifar da matsala ga tsakar cikin mafitsara, kuma ci gaba da yin hakan na tsawon lokaci zai iya rage ƙarfin jakar mafitsarar, lamarin da zai sa ta riƙa riƙe fitsarin, koda daga baya kun yi fitsarin ba zai fita duka ba.

Bincike ya nuna cewa riƙe fitsari zai sa wasu ƙwayoyin cutukan da ke cikin mafitsarar su ninninka, lamarin da ke haifar da hatsarin kamuwa da cutukan yoyon fitsari.

..

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Ba a so mutum ya riƙe riƙe fitsari na tsawon lokaci, da zarar ka ji fitsari ka gaggauta ban ɗaki domin yin sa.

Masana sun bayar da shawarar fitar da fitsarin da ya taru cikin mafitsararku a kowane sa'o'i uku zuwa huɗu.

A wasu lokutan mummunan ciwon yoyon fitsari kan lalata ƙoda.

Ka da ku gaggauta tashi bayan kammala fitsari, ku dakata har sai duka fitsarin ya kammala fita.

Masana na bayar da shawarar a tsaya daƙiƙa 10 zuwa 20 bayan kammala fitar fitsari, domin tabbatar da cewa mafitsar ta gama fitar da duka fitsarin da ya taru a cikinta.

2. Rashin shan wadataccen ruwa

Rashin shan wadattaccen ruwa kan haifar da ƙarancin zuwan fitsari cikin mafitsara, lamarin da ka iya haifar da bushewar mafitsarar, wani abu da ke haifar da haɗarin kamuwa da cutar mafitsara.

Masana na bayar da shawarar shan ruwa aƙalla kofi shida zuwa takwas na ruwa a kowace rana.

Suna kuma bayar da shawarar shan fiye da haka ga wanda yake aiki cikin zafin rana.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawaita shan ruwa na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar mafitsara

3. Yawan shan barasa da sinadarin Kafe (caffeine)

Sinadarin kafe (Caffeine) da barasa kan sa mafitsara saurin sakin fitsari da sauri.

Wani bincike ya gano cewa mutanen da ke shan fiye da miligiram 450 na caffeine a kowace rana, sun zarta waɗanda suke shan ƙasa da miligiram 150 hatsarin kamuwa da cutukan mafitsara.

Wani ƙarin binciken ya nuna cewa mazan da ke shan barasa sau shida zuwa 10 a mako na cikin hatsarin samun cutukan mafitsara fiye da waɗanda ba sa sha.

Yawan shan barasa ka iya ƙara haifar da hatsarin kamuwa da cutar kansa.

4. Zuƙar hayaƙi

Zuƙar yahaƙi da naga cikin manyan abubuwan da ke haifar da cutar kansar mafitsara.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kusan rabin masu fama da cutar kansar mafitsara zuƙar yahaƙi ne ya janyo musu.

Masu zuƙar hayaƙi na da hatsarin kamuwa da cutuka kusan sau hudu fiye da waɗanda ba sa zuƙa, kamar yadda bincike ya nuna, musamman ga waɗanda suka fara zuka tun suna ƙanana.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zuƙar sigari ka iya haifar da cutar mafitsa.

5. Rashin tsabtar ban-ɗaki

Rashin tsabtar ban-ɗaki kan haifar da ƙwayoyin cutuka a hanyar mafitsara.

Haka ma rashin iya tsarki kan haifar da matsalar, musaman ga mata.

Bincike ya nuna cewa wankowa daga baya zuwa gaba, (hanyar ba-haya zuwa hanyar fitsari) ka iya haifar da cutukan mafitsara.

Haka ma amfani da sabulai masu zafi ko rashin wanke hannu kan haifar da matsala ga ƙwayoyin halittar jiki, wani abu da ke haifar da hatsarin kamuwa da cutar mafitsara.

Haka kuma jima'i na daga cikin abubuwan da ke yaɗa ƙwayoyin cutuka, daga gaban mace ko na namiji, don haka ake bai wa maza da mata shawarar yin fitsari da zarar sun kammala jima'i domin rage hatsarin kamuwa da cutukan mafitsara.

6. Rashin abinci mai kyau da ƙarancin atisaye

Cin abinci mai kyau da yawaita atisaye na inganta lafiyar mafitsararku fiye da yadda kuke zato.

Yin ƙima fiye da ƙima na da ciki ya dannme mafitsara, lamarin da ke haifar da hatsarin ta riƙa zuibar da fitsari ko ba da ji shi ba.

Don haka yawaita atisaye da cin lafiyayyen abinci kan taimaka wajen rage ƙiba.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Atisaye na da matuƙar muhimmanci wajen rage ƙiba da nauyin jiki.

Wasu nau'ikan abinci da abin sha, kamar su lemukan kwalba, abinci masu yaji, da lemon tsami da kayan zaƙi da aka sarrafa, na iya cuitar da mafitsara kuma su ƙara ta'azzara alamun cutar ga mutanen da ke fuskantar waɗannan matsalolin.

Ku ci abinci mai ɗauke da sinadarin fibre kamar hatsi da 'ya'yan itatuwa, da kayan lambu don taimakawa narkar da abinci domin inganta lafiyar mafitsara

Lafiyar mafitsara na da tasiri ga zaɓin da kake yi na yau da kullun. Ku kasance cikin tsafta a kodayaushe, ku guje wa abubuwan da ke sa ku rasa ruwa a jikinku, haka ma ku kiyaye tsafta, na iya taimakawa wajen hana matsalolin na dogon lokaci.