Ku San Malamanku tare da Sheikh Nur Muhammad Arzai

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Nur Arzai

Ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya Sheikh Muhammad Nur Muhammad Arzai, ya ce babu abin da ya fi farin ciki da shi a rayuwarsa fiye da kasancewarsa shi da ƴaƴansa har da wasu jikokinsa koyarwa suke yi.

Sheikh Nur Arzai shi ne limamin Masallacin Juma'a na Sunusi Dantata da ke Kofar Ruwa a Kano, ya ce ya buɗe makarantu da dama musamman don koyar da yara ƙanana, kuma a yanzu ma yana da burin buɗe wasu ƙarin makarantun a wasu jihohin Najeriya inda za a ringa karantar da yara addinin Musulunci.

"Ni gidana kowa koyarwa yake, ni da ƴyaƴana, duk muna koyarwa. Har sun tafi gidajen mazajensu, duk muna koyarwa a makarantun nan gaba ɗaya. " in ji malamin,

Sheikh Nur Arzai wanda yana ɗaya daga cikin manyan jigogin ɗariƙar Tijjaniya a Kano, ya bayyana haka ne a cikin shirin Kusan Malamanku na BBC Hausa, lokacin da yake bayani kan iyalensa.

Malamin da iyalansa dai suna koyarwa ne a makarantarsa da ke Kwaciri a karamar Hukuma Fagge cikin birnin Kano, sannan suna da rassa a Ungogo da Abuja da Aujara jihar Jigawa.

Wannan layi ne

Asalin Malamin

Sheikh Muhammd Nur Arzai asalinsa mutumin Aujara ne da ke kasar Ringim a jihar Jigawa. An haife shi a 1957 a garin Taura karamar Hukumar Rngim da ke lardin Kano a lokacin.

"An haife ni ne a wajen yawon wa'azi, saboda mahaifina mai yawan yawon wa'azi ne," in ji shi.

Neman Ilimi

Mahaifinsa shi ne Malam Muhammadu Aujara, wani babban malami a lokacinsa kuma daya daga manyan malaman ɗariƙar Tijjaniyya.

Sheikh Nur Arzai ya taso a unguwar ƴar Magaji a cikin birnin Kano, ya fara karatu a wajen mahaifiyarsa Sayyada Hajara da Mahaifinsa, sannan ya halarci wajen malaman a Kano inda ya yi karatu a wajensu.

Yana ɗan shekara 10 mahaifinsa ya kai shi karatu wata shahararriyar makarantar allo a Kano ta Sheikh Manzo Arzai, inda ya shafe shekaru da dama yana karatu a makarantar har zuwa girmansa.

Kuma ya samu sunan Arzai ne daga zamansa a makarantar Malam Manzo dake unguwar Arzai.

Yayin zamansa a wannan makaranta ta Arzai ne ya yi karatun wasu ɓangarorin ilimi na addinin Musulunci a wajen ƴaƴan Malam Manzo da kuma wasu malaman.

Sheikh Nur Arzai ya yi karatu wajen Malam Ƙarami Uwaisu Madabo, sannan bayan rasuwarsa ya koma wajen ɗan uwansa Sheikh Abdullahi Uwais Madabo.

"Wannan har izuwa yanzu muna zaunawa a wajensa muna karatu, don shi wannan ba ƙarewa yake ba," Inji Sheikh Nur.

A bangaren karatun zamani ya shiga makarantar firamare ta Nahdatul Islam dake unguwar Gwammaja a 1977, sannan ya halarci makarantar sikandare ta Warure, da makarantar Koyon Harshen Larabci SAS inda ya kammala a 1982.

Sheikh Nur Arzai

Asalin hoton, Sheikh Nur Arzai

Ya halarci kwalejin shari'a ta Malam Aminu da aka fi sani Legal inda ya yi difiloma, sannan ya halarci Jami'ar Musulunci da Kungiyar Ƙasashen Musulmi OIC ta kafa a garin Yame na Jamhuriyyar Nijar inda ya kammala a 1997.

Malam Nur ya ce ya fi sha'awar bangaren ilimin hadisi, don haka ya fi karkata ga wannan ɓangare.

Baya ga karatun addinin, malamin ya ce ya kuma yi difiloma, kan gyaran lantarki. "Yanzu haka da za a haɗa min kaya, to zan iya yin hita ta dafa ruwa, zan iya naɗa kwayal, zan iya gyaran fanka zan iya gyaran rediyo, duk da zan shiga ina ga duk zan iya gyara su."

Abincin da ya fi so

Sheikh Nur Arzai ya ce da yake shi almajiri ne ba shi da zabin abinci, amma da safe ya fi son shayi fiye da komai, in kuma ba shayi ba to a samu kunu," da rana kuma ko me ya samu da daddare kuma ba shi da abin sha'awa irin tuwo," in ji shi.

Wannan layi ne

Wasanni na ƙuruciya

"Wayyo ni na samu wani irin yanayi da muka tashi a makarantarmu," inji Sheikh Nur Arzai da aka tambaye shi ko ya samu damar wasanni irin na yara.

Yace "Malamanmu ina daga cikin wadansu suka bi abin da suka faɗa. An takura lokacin zuwa irin su ball ɗin nan, su sauran wasanni, ni Allah bai ƙaddara ina da rabo a cikin komai nasu ba."

Surar da ya fi so a Alkur'ani

Da BBC ta tambayi Malamin ko wace sura ya fi so a Alkur'ani, sai ya ce ya fi son Suratul Bakara, saboda tana yi wa mutum savice (Garen-bawul) dangane da hukunce-hukunce da rukunan Musulunci.

Sannan ya ce Surorin Alam Nashrah da ƙulhuwallahu su ma suna burge shi "ƙwarai da gaske."

Tambayoyin da aka fi yi masa

Sheikh Nur Arzai ya ce mafi yawa tambayoyin da aka fi yi masa tambayoyi ne a kan tarbiyya sai kuma hukunce-hukuncen aure.

Alaƙa da wasu malamai masu bambancin fahimta

Sheikh Nur Arzai na daga cikin manyan malaman ɗariƙar Tijjaniyya a Kano, matsayin da ya gada daga mahaifinsa. Sai dai ya ce hakan bai hana shi yin mu'amala da wasu malaman da suke da sabanin fahimta ta addini ba.

Ya ce "ba ni da duhun kan ba za mu yi mu'amala da wanda ya saɓawa fahimtata ba. Yadda yake kallona a wasu abubuwa ba daidai nake ba, ni kuma ina da dalilan yi, to shi kuma ina kallonsa shi ma ba daidai yake ba a wasu wurare."

"Wannan kuma bai hana mu haɗu ko a majalisar Sarkin Kano, don ina daga cikin ƴan majalisar masu ba da fatawowi akan harkar addini, sannan majalisar malamai ta Kano ta haɗa kowa da kowa, kuma duk muna haɗuwa ba wani abu," in ji Sheikh Nur Arzai.

Iyalin Malamin

Sheikh Nur Arzai yana da mata uku, da ƴaƴa masu rai 25 a jikoki 36.

Wannan layi ne