'Dalilin da ya sa nake gayyatar Kiristoci masallaci wurin tafsiri da Ramadan'

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheik Nuru Khalid

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An haifi Sheikh Muhammad Nuru Khalid a ranar 1 ga watan Oktoban 1960, wato ranar ɗaya da aka bai wa Najeriya ƴancin kai kenan.

An haifi malamin a cikin garin Jos, jihar Filato, kuma a garin na Jos ɗin ne malamin ya tashi kuma ya yi rayuwarsa.

A tattaunawar da BBC ta yi da malamin, ya bayyana cewa zai yi wuya ya iya tantance lokacin da ya fara karatu, domin mahaifinsa malami ne, don haka ya tsinci kansa ne cikin karatu.

Sheikh Nuru ya bayyana cewa ya haddace Al-Qur'ani tun yana ɗan ƙaramin yaro a gaban mahaifinsa.