Ku san Malamanku: Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku san malamanku tare da Sheikh Daurawa

Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa:

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata aya a Al-Ƙur'ani.

Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin sabon shirinmu mai taken "Ku San Malamanku".

Ya ce ayar da ta fi ba shi wuya ita ce wata aya da ke cikin Suratul Baqara, wato Iza Tadayantum..., wadda ita ce ayar da ta fi kowace tsawo a littafi mai tsarki.

Sai kuma wata aya da ake magana a kan rabon gado, ita ma malamin ya ce ta ba shi wahala saboda kalmomi iri ɗaya da ake maimaitawa a cikinta.

Malamin ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa ya yi nazarin abubuwa kusan 61 waɗanda suke jawo mace-macen aure a ƙasar Hausa.

Sheikh Aminu Daurawa ya ce hira da tambayoyi da ya yi wa zawarawa da 'yan mata da aurensu ya mutu na tsawon lokaci ne ya sa ya gano waɗannan dalilai.

Wannan layi ne

Tarihin rayuwarsa

A cikin wannan shiri na "Ku San Malamanku", malamin ya bayar da taƙaitaccen tarihin rayuwarsa, da kaɗan daga cikin gwagwarmayar da ya yi wurin neman ilimi na addini da na boko, da malamai daban-daban da ya koyi karatu a wurinsu da sauran abubuwa.

Da farko dai an haifi Malam Aminu Daurawa a ranar 1 ga watan Janairu nshekara ta 1969, a Unguwar Kofar Mazugal, a Ƙaramar Hukumar Dala da ke cikin garin Kano.

Sunan mahaifiyarsa Hajiya Sa'adatu Al-Mustapha, daga Unguwar Bachirawa, Ƙaramar Hukumar Ungogo a jihar ta Kano, mahaifinsa kuwa shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad Mai Tafsiri.

Malamin ya bayyana cewa ya soma karatun Al-Qur'ani mai girma tun yana ɗan karami, kuma ya haddace shi a lokacin yana da shekara 14 zuwa 15.

A ɓangaren karatun Boko kuma, malamin ya ce mahaifinsu ya yarda ya yi firamare, amma bai yadda ya ci gaba da sakandare ba sai ya haddace Al--Qur'ani, kuma hakan aka yi.

Bayan kammala firamare da sakandare, Sheikh Daurawa ya kuma ci gaba da neman ilimi, domin faɗaɗa karatun addini, a wajen waɗansu manyan mashahuran malamai na Kano.

Ya ci gaba da karatu na zamani a Jami'ar Bayero, a ɓangaren aikin jarida, ko da yake wasu dalilai sun tsayar da shi wanda hakan bai sa ya kammala ba., amma ya yi karatun difiloma a computer data processing.

Malamin ya ce wani muƙami da ya taɓa riƙewa na gwamnati shi ne kwamandan Hisbah da ya yi tsawon shekara takwas.

auren zawarawa a Kano
Bayanan hoto, Sheikh Aminu Daurawa na daga cikin gaba-gaba wajen aurar da zawarawa da gwamnatin jihar ta yi a baya lokacin ya shugabancin hukumar Hizbah

Malamin ya bayyana cewa ɗaya daga cikin hukunce-hukunce da ya taɓa rufe ido ya zartar a jihar Kano a lokacin da yake kwamandan Hisbah, shi ne tursasawa da ya yi kan cewa sai an yi doka a Kano na a dinga yin gwaji kafin a yi aure.

Sheikh Daurawa ya ce wannan ya ba shi dama har ya fito da wani shiri na aurar da zawarawa, wanda al'umma da gwamnati suka bayar da haɗin kai har aka aurar da mata kusan dubu shida zuwa dubu bakwai.

Sheik Aminu Daurawa ya bayyana cewa akwai kuma wani abu mafi muni da ya kasa fita daga zuciyarsa na wani mutum da ke neman 'ya'yansa mata guda biyu. Mutumin ya kori mahaifiyar yaran inda ya shafe sama da shekara ɗaya yana zama da 'ya'yansa tamkar matansa na aure. Da abin ya ishe 'ya'yan ne suka kai mahaifin nasu ƙara.

Wannan layi ne

Zogale da ƙuli-ƙuli da koren tattasai

A ɓangaren abinci kuma, malamin ya ce ya fi son zogale da ƙuli-ƙuli da koren tattasai da albasa da tumatiri, malamin ya ce yana matuƙar son wannan haɗin.

Babbar kyautar da malam ya ce ba zai manta da ita ba ita ce kyautar naira 200 da wani mutum ya zo ya kai masa har gida saboda ƙaunar da ya ce yake wa malamin.

A lokacin da yake matashi, ya buga wasan ƙwallon ƙafa sosai.

A cewarsa, shi bahago ne, wanda hakan ya sa ya fi buga lamba uku ko tara ko kuma 11.

Sai kuma ta ɓangaren tafiye-tafiye kuma, malamin ya ce ya fi zuwa ƙasashen Afrika da na Larabawa, amma a kwanakin baya ya yi biza zai je ƙasar Amurka da Turai sai kuma aka samu ɓullar annobar korona.

Malam ya ce babban burinsa a duniya shi ne ya cika da Imani.

Wannan layi ne