Ku San Malamanku Tare da Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku Tare da Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon hirarsa da BBC

Idan ana maganar malaman addinin Musulunci a Najeriya wadanda ke da tasiri a wajen mabiyansu ake kuma sauraron maganganunsu sannan suke da ƙima a wajen 'yan uwansu malamai, to tabbas ba za a tsallake Dakta Bashir Aliyu Umar ba.

Babban limamin Masallacin Juma'a na Al-Furƙan da ke unguwar Nasarawa a Kano na daga cikin malaman da ke da ilimin zamani kuma suke amfani da shi wajen karantarwar addinin Musulunci.

Malamin wanda ya riƙe mukamai da dama a gwamnati da kuma jami'a inda yake koyarwa, yana amfani sosai da kafafen sa da zumunta wajen karatuttukansa, ciki har da wadanda ake watsawa kai tsaye a Facebook.

Idan ana gadon ilimi da shugabanci a iya cewa Dakta Bashir ya gaji gidansu, domin ya fito ne daga shahararriyar zuriyar Gwani Zara a Kano, wadanda suka shafe fiye da shekara 100 suna limanci da alƙalanci a Kano.

Sarkin Kano na biyu bayan jihadi Malam Ibrahim Dabo ne ya naɗa kakansa Malam Muhammad Zara Limamin Kano, kuma limamin Kano na yanzu ma Farfesa Emiratus Muhammad Sani Zahraddeen daga zuriyar yake.

Sannan sun fara alƙalanci bayan zuwan Turawa, kamar yadda masanin tarihi Malam Ibrahim Ado Kurawa ya bayyana.

A bangaren sarauta, mahaifinsa Alhaji Aliyu Harazumi Umar shi ne Dan Amar din Kano kuma hakimin Doguwa a yanzu. Ta ɓangaren uwa kuma kakarsa da ta haifi babarsa ƙanwa ce ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Wannan layi ne

Tarihinsa da karatunsa

An haifi Dakta Bashir Aliyu Umar a Unguwar Yola a cikin birnin Kano ranar 27 ga watan Yuli 1961.

Ya yi karatun allo har zuwa sauka a makarantar Malam Kabiru Khalil da ke Kofar Ƙwaru cikin gidan Sarkin Kano.

Ya yi karatun ilimin addini da harshen Larabci a wajen malamai da dama a Kano, ciki har da wan mahaifinsa Marigayi Alƙali Idris Ƙuliya, tsohon alƙalin alƙalan Kano kuma tsohon limamin Kano, da Malam Gali na Malam Shamsu na Magangara da Malam Baba na bayan gidan Wazirin Kano da Shehu Muhammadu Barnoma.

A bangaren karatun boko ya yi makarantar firamare ta Jar Kasa, sannan ya yi sakandare a kwalejin gwamnatin tarayya Federal Government Collage Kano.

Ya yi karatun share fagen shiga jami'a a ƙarƙashin Jami'ar Ahmadu Bello a Zariya, sannan ya fara karatun injiniyan lataroni a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria.

Sai dai an kore shi tare da wasu ɗalibai daga jami'ar, saboda yunƙurin da Kungiyar Dalibai Musulmai MSSN ta jami'ar ta yi na hana shan giya a jami'ar ta ABU duk da hukumomin makarantar sun ba da damar shan giyar.

A tattaunawar da ya yi da BBC ya ce har yanzu ba ya nadamar ɗaukar wannan mataki da ya yi, haka kuma ya ce ba ya nadamar fara karatun injiniya.

"Saboda na ga karatun ya amfane ni, domin ɓangaren kimiyya yana daga cikin ilimin da yake taimakawa wajen fahimtar ayoyin Allah a cikin halitta, wanda Kura'ani kullum yake kiranmu mu ringa la'akari da su, mu ringa izina da su," in ji Dokta Bashir.

Bayan ya bar jami'ar ABU ya samu damar tafiya Jami'ar Pennsylvania a Amurka don ci gaba da karatun injiyancin.

To amma bai karɓi damar ba, "domin ni a lokacin sha'awata samun ilimin hadisi, don a lokacin ne na mai da hankali na yi haddar Alkur'ani, in ji Malamin.

Dokta Bashir ya ce "Saboda haka na tafi Jami'ar Musulunci ta Madina don samun wannan ilimi na hadisi."

Burinsa ya cika, domin kuwa ya yi digiri na farko da na biyu da na uku a bangaren Hadisi a jami'ar.

A lokacin da yake Madina, Dakta Bashir ya samu damar yin karatu a wajen manyan malamai a birnin na Madina baya ga karatun jami'a.

Daga cikin malaman akwai malamin fikihun Malikiyya Sheikh Mahmoud Wulzidan, da Shaikh Abdulmuhsinul Abbad, da Sheikh Muhammad Mukhtar As-Shankidi, da Dokta Muhammad Madar Az-Zaharani.

Wannan layi ne

Haddar Alkur'ani

Dr Bashir

Asalin hoton, Facebook

Dakta Bashir mahaddacin alkur'ani ne, to sai dai ya ce bai kai ga zama gangaran ba. Ya haddace Alkur'ani bayan ya bar Jam'iar Ahmadu Bello.

Sannan ya ringa zuwa wuraren da ake musaffar Alkur'rni a gidan malaminsa Sheikh Muhammadu Barnoma, tun kafin ya tafi karatu Saudiyya.

A kasa mai tsarki kuma lokacin da suke karatu, sun yi sauka ta tilawa da dama tare da Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam. Ya ce har yanzu haddarsa tana nan.

Wasu labaran masu alaƙa da za ku so

BBC: Wadane surori ne suka fi ba ka wahala wajen hadda?

Dokta Bashir: A Gaskıya surorin da suka fi ba ni wahała su ne Suratuz Zumar da Suratu Hud.

"Surorin da na fi so kuma Suratus-Saffat da Suratu Mulk," in ji malamin.

Tambayoyin da aka fi yi masa

Da BBC ta tambayi malamin ko wadanne tambayoyi aka fi yi masa sai ya ce, an fi yi masa tambaya a kan kasuwancin zamani. Ya ce hakan ba zai rasa nasaba da aikin da ya yi a Babban Bankin Najeriya ba, CBN musamman wajen tsara ƙa'idojin yadda bankin Musulunci zai yi aiki.

"Fage na biyu da ake yi min yawan tambaya shi ne harkar auratayya," a cewar Dokta Bashir.

Wannan layi ne

Kasashen da yake son zuwa

australia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Malam na son zuwa Australiya wacce ke can kudancin duniya

Babban limamin na Masallacin Al-Furƙan ya ce ƙasahen da yake fatan zuwa biyu ne. "Australiya, saboda tana can kudancin duniya. Yanayın yana zamowa wani iri daban."

Dakta Bashir ya ce "To sai kuma can arewa ko Norway ko Finland. Saboda abin da nane sha'awa in gani shi ne wannan abin da suke cewa Midnight Sun. Tsakar dare karfe 12 ka ga rana tana nan."

Ya kara da cewa yana kuma so ya ga hasken taurarin da ake cewa Auroro Lights, wadanda ba a ganinsu sai a kasashen yankin.

Manyan burikansa

Manyan burikan malamin ya ce uku ne

1. Kammala rubutun litattafan da ya fara

2. Saukar Tafsirin Alkur'ani da yake yi kowane mako da kuma wanda yake yi da azumi

3. Kafa makarantar koyar da ilimin hadisi da za ta iya zama jami'a nan gaba.

Wannan layi ne

Rai dangin goro

Lokacin da yana da ƙuruciya, Dokta Bashir ya ce ya yi wasanni irin na yara, musamman Hasan Bago da kuma kwallon kafa.

A yanzu malamin yana da mata biyu da 'ya'ya 12 da jikoki takwas.

Matarsa ta farko 'yar Zariya ce ta biyu kuma 'yar Kenya ce.

A cewar malamin babban abin da yake sa shi farin ciki shi ne ya ga ya yi wani abu da iyayensa za su ji dadi.

Yace "Duk ran da na yi abu na ga na faranta musu, farin cikin ya bayyana a fuska da kuma kalamansu, to zan dade wannan abin yana tasiri tare da ni, yana sanya min nishadi da annashuwa da kuma jin cewa hakika Allah ya yi min baiwa."

Wannan layi ne