Ku San Malamanku tare da babban limamin Jigawa, Dr Abubakar Sani Birnin Kudu

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku da Dr Abubakar Sani Birnin Kudu

Babban limamin Masallacin Juma'a na Dutse da ke jihar Jigawa a arewacin Najeriya Dr Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu ya ce mutane da yawa ba su fahimci Sheikh Ibn Taimiyyah ba kan aƙidunsa.

Dr Abubakar ya faɗi hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirin Ku San Malamanku, inda ya jaddada cewa Sheikh Ibn Taimiyya mutum ne mai son zaman lafiya.

Yana wannan magana ce bayan da aka yi masa tambaya kan ko wane malami ne ya fi tasirantuwa da shi a rayuwarsa, sai ya ce Ibn Taimiyyah.

"Malami ne da ya iya bibiyar mas'ala tare da warware ta ta hanyar bin Al-Ƙur'ani da Sunnah.

"Ana koyon tausayin al'umma da haƙuri da wanda ya saɓa maka a wajen Ibn taimiyya, saɓanin yadda aka fi yaɗa wa a duniya cewa tunaninsa ne ya jawo abubuwan tashin hankalin da ke faruwa a duniya."

Dr Abubakar ya ƙara da cewa "da an fahimce shi za a gane babu mai yi wa abokan gabarsa adalci irin Ibn Taimiyyah. Wadanda suka yi masa karatu daga nesa ko na siyasa ne suke masa wancan kallon," a cewar babban malamin.

Da aka yi wa malam tambaya kan ko kyautar da ta fi ba shi mamaki sai ya ce ita ce wacce ɗaya daga malamansa a Madina Malam Muhammad Bin Abdullah Zarban al-Gamidi ya yi masa ta gaba daya litattafan ɗakin karantunsa.

A cewar Malam Abubakar, malamin nasu wanda tsohon limamin Masallacin Ƙuba ne a Madina ya aiko masa da litattafan wadanda sun kai manyan kwalaye 133.

Wannan layi ne

Wane ne Dr Abubakar Birnin Kudu?

An haifi Dr Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu ranar 7 ga watan Janairun 1965.

Ya yi makarantar firamare a Birnin Kudu daga shekarar 1971 zuwa 1978, daga nan ya je makarantar sakandare ta Government College da ke Kaduna daga shekarar 1978 zuwa 1983.

Bayan kammala sakandare sai ya fara aiki a makarantar haɓaka aikin noma da rayuwar al'umma daga 1983 zuwa 1984 a matsayin mai buga tafireta.

Bayan wani lokaci sai ya samu damar ci gaba da karatun difloma a Zaria a fannin akanta daga 1984 zuwa 1986.

A zamansa na Zariya ne ya samu damar yin karatun addini a wajen malaman zaure irin su Malam Muhammad Sani Gummi, limamin Masallacin Juma'a na Ɗan Ja a Kongo wanda ya yi karatun Risala a wajensa.

Sannan ya karanta Ahalari da Iziyya a wajen Malam Muhammadu Bazamfare a Gyallesu. Tun a lokacin ya fara jan mutane sallah inda malam ke ƙaddama shi.

Ya koma birnin kudu a 1987 sannan daga baya ya koma ya samu aiki a KNARDA a matsayin book keeper har tsawon shekara hudu.

Daga baya ya samu gurbin yin digiri a Jami'ar Bayero ta Kano, sai dai shekararsa ɗaya kawai sai ya samu gurbin karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina a shekarar 1992.

Hakan ya faru ne bayan zuwan Malaman Daura daga Madina zuwa Kano a 1991 inda aka yi musu jarrabawa ya kuma ci.

Malam ya ce wannan ne lokaci mafi farin ciki a rayuwarsa saboda irin ingancin karatun da Jami'ar Madina ke da shi, sannan kuma a birnin da Manzon Allah SAW ya rayu, ga kuma malamai masu ilimi.

''Farin cikin hakika ba na wasa ba ne,'' in ji malam.

Malam ya ce ba zai manta da Kuruciyarsa ba don ta kasance mai cike da neman ilimi da wasanni irin na yara kamar ƙwallo.

Ya ƙware ne a fannin shari'a a Saudiyya tsawon shekara hudu na digiri. Ya karancin fannin da'awa da aƙida a digiri na biyu da digirin-digirgir.

Malam ya ce a Madina ya koyi Larabci sosai idan aka ɗauke karatun Nahawu da ya yi na zaure a Birnin Kudu. Sannan a Madina ya yi haddar Al-Ƙur'ani.

Bayan dawowarsa daga Madina a 2010 ya yi aiki a matsayin mataimakin darakta a hukumar kula da harkokin addinin Musulunci ta jihar Jigawa, sannan Sarkin Dutse ya ba shi limanci a babban masallacin garin.

Daga baya ya samu aiki a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya tun daga 2011 zuwa yanzu a sashen ilimin addinin Musulunci. Sai dai a bara ne gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya ba shi babban sakatare na ma'aikatar ilimi ta jihar a matsayin aro.

Har yanzu kuma shi ne babban limamin Masallacin Juma'a na Dutse.

Yana da mata uku da yara 15, babban ɗansa ma ya kammala karatun digiri na biyu a Madina.

Wannan layi ne