Mai kamfanin Twitter ya tsananta wa ma'aikatansa

Elon Musk

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Elon Musk

Elon Musk ya fada wa ma’aikatan Twitter cewa dole su jajirce wajen yin aikin “ tsawon sa’oi ko kuma su bar kamfanin, a cewar rahotanni.

A cikin wani sakon imel da ya aike wa ma’aikatansa sabon shugaban kamfanin sada zumunta ya nemi ma’aikata da su amince da matakin idan suna son su ci gaba da aikinsu kamar yadda jaridar Washington ta ruwaito.

Wadanda suka ki sa hannu har ranar Alhamis za a ba su albashin sallama na watanni uku, in ji Mista Musk.

BBC ta ta tuntubi Twitter a kan alamarin

A sakon da ya aikewa ma’aikatansa ta imel wanda ita ma jaridar The Guadian ta gani , Mr Musk ya ce sai kamfanin ya ‘’tashi tsaye haikan’’ idan yana son ya cimma nasara.

" Wannan na nufin za su shafe tsawon sa’oi suna aiki ba ji ba gani. Za a kyautatawa wadanda suka nuna kwazo ," in ji shi

An fada wa ma’aikatan cewa ana son su amince da wannan sako kafin yammacin ranar Alhamis idan suna son su kasance a cikin sabon Twitter.

Ya kara da cewa: " Duk shawarar da kuka yanke ina godiya ga kokarinkin da kuka rika yi domin kamfanin ya ci gaba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun farko attajirin da ya fi kowa kudi a duniya ya sanar da sallamar rabin ma’aikatan Twitter bayan ya sayi kamfanin a kan dala biliyan 44.

Mista Musk ya ce "ba shi da wani zabi" a kan korar yayin da kamfanin ke asarar dala miliyan 4 a kowace rana. Ya dora alhakin wannan komabaya a kan " kungiyoyi masu fafutuka da ke matsawa kamfanonin masu talace talace " game da matukar raguwa a kudaden shigarsa".

Haka kuma an samu wasu manyan shugabannin kamfanin da suka sauka daga mukamansa bayan da ya sayi kamfani.

A makon daya gabata dan kasuwan ya fadawa ma’aikatansa cewa za a daina amfani da tsarin nan na aiki a gida kuma za a shiga cikin wani “”hali na matsi" nan gaba a cewar rahotani.

A sakon imel din da ya turawa ma'aikatamsa,mamalakin kamfanin sada zumunta ya ce ma’aikatan za su rika aikin ofis na tsawon saoi 40 a kowani mako a cewar kafar yada labarai ta Bloomberg

Mista Musk ya kara da cewa "ranar wanka ba a boyan cibi" kuma tafiyar hawainiyyar da tattalin arzikin duniya ke yi zai shafi kudin da kamfanin yake samu

Sai dai Sarah Kunst wadda kwarariyar ce a harkar fasaha ta ce dailin da yasa Twitter ke fusnkantar matsaloli shi ne cewa tsarin da Mista Musk ya bi wajan sayen kamfanin ya bar kamfanin da bashi

Ta kuma ce dabi'arsa tun bayan da ya sayi kamfani ta wasu masu tala -talace sun dakatar da kudadensu.

"A yanzu yana neman ya huce haushinsa a kan ma'iakatan ta hanyar sanya musu fargaba ta rashin tabbas a aiki da kamfanin.," in ji ta

Ta kuma kara da cewa akwai alamar tambaya a kan yada za a aiwatar da wannan tsari na tsawon sa'oin da ma’aikata za su rika aiki.

" Shin za ka iya aika da imel kawai ga ma’aikata da ke maka aiki kuma kawai sai ka sauya kwantiragin aikinsu ba tare da izinin wasu ba? Wannan abin a jira a gani ne