Twitter: Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin Twitter a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Shafin Tuwita ya daina aiki a Najeriya bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da shafin a ranar Juma'a.
An lura shafin ya daina aiki ne a tsakiyar daren Juma'a wato wayewar garin ranar Asabar.
Hakan na faruwa ne sa'o'i kadan bayan gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin na Tuwita.
Wata sanar da ma'aikatar yada labarai da al'adu ta fitar, ta ce Minista Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a Abuja a ranar Juma'a.
Sanarwar ta ce Minista Mohammed ya ce ana amfani da shafin wajen raba kawunan ƴan ƙasar.
Lai Mohammed ya kuma ce ya bai wa hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.
Sai dai gwamnatin Najeriyar ba ta fayyace abin da take nufi da wannan mataki ba ya zuwa yanzu.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shafin Tuwita ya goge wani saƙo cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa yana gargaɗin ƴan awaren IPOB.
Tun bayan cire saƙon shugaban ƙasar fadar Shugaba Buhari ta ce tana sane da matakin da Tuwita ya ɗauka, kuma ta aika da buƙatar neman jin dalilin da ya sa kamfanin ya goge saƙon.
Tuni dai kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce za ta kalubalanci matakin gwamnatin a kotu, a wani sako da ta wallafa a Tuwita din.

Asalin hoton, Twitter
Shafin ya daina aiki
Bayanai sun nuna cewa shafin na Tuwita ya daina aiki a kasar ta Najeriya tun daga tsakar daren Juma'a.
'Yan kasar da ke amfani da shafin sun kasa bude shi ta hanyar da aka saba, ko da yake akwai wata dabara da ake amfani da ita ta hanyar VPN domin iya bude shafin.
Sai dai ba kowa ne ya san yadda ake yin hakan ba.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Jim kaɗan da fitar da wannan sanarwa sai ƴan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta musamman Tuwitar.
Tuni aka ƙaddamar da maudu'ai har huɗu a shafin na Tuwita don tattaunawa kan batun, da suka haɗa da #So Twitter da aka yi amfani da shi kusan sau miliyan ɗaya a ƙasa da ɗaya da #Twitter in Nigeria 100,000, da #Using Twitter da aka yi amfani da shi sau 239,000.
Sannan akwai maudu'in #Federal Government mai 36,000 da kuma #TwitterBan mai saƙonni 1,384. AKwia kuma irin su #Jack da #Lai Mohammed da #Twitter in Nigeria da #Suspending Twitter da dai sauran su.
Ƴan ƙasar da dama ne suka dinga bayyana ra'ayoyi daban-daban kamar haka:
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a 2019 Alhaji Atiku ya wallafa cewa: "Ina fatan kar wannan ya zama saƙona naƙarshe a Tuwita."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Jibrin Ibrahim tsohon shugaban Cibiyar Binciken Harkokin Dimokraɗiyya CDD shi ma ya rubta: "Ministan Yada Labarai da Al'adu Lai Mohammed, ya dakatar da Tuwita a Najeriya saboda a cewarsa ana amfani da kafar wajen raba kan ƴan ƙasar. To hakan yana nufin idan babu Tuwita ana da tabbacin kan ƴan ƙasar zai haɗu ne?"
Tsohon sanatan yankin Kaduna Ta Arewa Sanata Shehu Sani ma cewa ya yi: "Dakatar da Tuwita, jawowa kai abin faɗa ne."
Arewa Twittér kuwa cewa ya yi: "Ina goyon bayan wannan dakatarwa duk kuwa da cewa ina samun kuɗ a Tuwita, amma wannan ne mataki mai kyau da gwamnatin tarayya ta dauka da ya birge ni."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2












