Gwamnatin Buhari ta bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan kuskuren bayanin cike sabon fom na banki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Najeriya ta nemi afuwar ƴan kasar kan wani sabon fom din banki da ta fitar kuma ta bukaci su shiga bankunansu su cike.

Gwamnatin ta ce akwai kura-kurai a kan bayanin da tsarin cike fom din don haka ta goge sakon da ta wallafa na neman bukatar cike wannan fom din.

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriyar ta wallafa sanarwar a shafinta na Tuwita inda ta buƙaci ƴan ƙasar da su shiga bankunansu su cike wani sabon fom.

Sannan masu amfani da banki fiye da ɗaya dole sai sun shiga bankunan sun cike sabon fom ɗin. Tsarin kuma ya shafi duk wani mai asusu a banki da suka haɗa da kamfanoni.

Cike sabon fom ɗin na banki wani sabon tsari ne da gwamnati ta ɓullo da shi da ya shafi haraji.

Sai dai a sanarwar da ta sake wallafa ranar Juma'a a Tuwitar gwamnatin ta ce: "Muna bayar da haƙuri kan saƙonnin tuwita da ba daidai ba (an goge su a yanzu) da aka sanya a jiya, kan cike wani fom na banki da bayanan mutane. Saƙon wanda yake shafin @firsNigeria ba kowa ya shafa ba. Hukumar karɓar haraji ta FIRS za ta fitar da bayanan da suke dai dai nan ba da jimawa ba.

Fusatar da ƴan ƙasa tun farkon sanarwar

Gwamnatin Najeriya ga alama ta fusata ƴan ƙasar a shafukan sada zumunta kan wata sanarwa da ta fitar a Tuwita, inda ta tilasta cike wani fom a bankuna.

Da fari gwamnatin ta ce tana buƙatar bayanan ƴan Najeriya a sabon fom ɗin daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi domin aiwatar da ƙa'idojin da suka yi daidai da dokar haraji ta 2019.

Gwamnatin Najeriya a cikin sanarwar, ta yi gargaɗi cewa za ta ɗauki mataki ga duk wanda bai je ya cike sabon fom ɗin ba. Matakin kuma ya shafi cin tara ko kuma toshe asusun ajiyar mutum ko kamfani.

Wannan sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar ba ta yi wa ƴan ƙasar daɗi ba inda suka dinga tsokaci na martani ga sabon matakin.

Wasu ƴan ƙasar na ganin akwai tsoffin tsare-tsare na tantance asusun ajiyar mutum da ya kamata gwamnati a ce ta yi amfani da su, musamman lambar BVN da lambar haraji ta Tin da kuma katin shaidar zama dan ƙasa waɗanda suke ganin duk suna iya sawwaƙe wa gwamnati ba sai ta ɓullo da wata sabuwar hanya ba.

Martanin ƴan Najeriya a Tuwita

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

JJ Omojuwa ya yi shaguɓe cewa: ''BVN = bayanan mutum.Katin shaidar ƴan ƙasa = bayanan mutum.Rijistar layin waya = bayanan mutum. Shaidar katin tuƙi = bayanan mutum.

''Amma ina tabbatar muku cewa wannan sabon "self-certification" din shi ne babansu gaba ɗaya, da zarar an yi shi, to duk abin da aka kasa yi da bayanan waɗancan shi za a iya yi da shi. SMH.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Olusegun Adeniyi ya amsa saƙon gwamnatin da cewa: ''BVN. Shaidar katin tuƙi. Katin shaidar ƴan ƙasa. Rijistar katin zaɓe. Fasfon tafiye-tafiye. Duk ana ɗaukar bayanan mutum. To mene ne amfanin hakan?''

Wasu na ganin sabon matakin zai haifar da cunkosu a bankuna yayin da kuma bankunan suka taƙaita yawan mutanen da ke shiga bankunan saboda tsoron annobar korona.

Ƴan Najeriyar na ganin gwamnati ba ta yi tunani ne ba tilasta zuwa banki domin cike sabon fom ɗin ba tare da fito da wani tsari ba da za a iya cikewa a intanet ba tare da mutum ya shiga banki ba.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Mr. 'Dipo ya rubuta cewa: ''Zuwa banki don bin layin cirar kuɗi a ATM ma kawai ya zama yaƙi a wannan zamanin, ta yaya gwamnati za ta yi tunanin yin wannan abu da ya shafi ɗumbin mutane zai yiwu?''

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Ichie! #Anaedo! ya rubuta cewa: ''Shirme! Shirme! Shirme! Shirme! Shirme! Shirme! A zamanin annobar cuta korona amma gwamnatin Najeriya na son kowa ya je banki don cike fom.

''Me ya sa ba za a sanya fom din a intanet ba a cike a mayar? Mene ne amfanin BVN? HAUKA!

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6

Wasu kuma na kuka ne kan irin yawan kuɗaɗen haraji da gwamnati ke tatsa.

Kauce wa X, 7
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 7

Wasu ƴan Najeriyar kuma sun fusata ne kan hangen irin wahalar da sabon matakin zai jefa su musamman idan suka tuna girman wahalar da aka sha lokacin da gwamnati ta ɓullo da tsarin lambar BVN.

Kauce wa X, 8
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 8