Instagram ya kashe maɓallin ɓoye sirri, me hakan ke nufi ga saƙonnin sirrinku?

A smartphone being read, held in the hands of a woman with long, wavy, red hair and wearing a brown, orange, white and red-patterned shirt.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Joe Tidy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Cyber correspondent, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Instagram ya sanar da cewa masu amfani da manhajar ba za su ƙara iya aika saƙonnin sirri na musamman da ake ɓoye su gaba ɗaya ba, bayan da kamfanin ya kashe tsarin maɓallin sirrin manhajar a faɗin duniya.

Wannan mataki na kashe maɓallin sirri na nufin babban sauyi daga matsayar babban kamfanin da Instagram ke ƙarƙashi wato Meta, wanda a baya yake bayyana wannan fasaha a matsayin mafi ingancin kariya ga sirrin masu amfani.

Maɓallin ɓoye saƙonni da ake kira end-to-end encryption (E2EE) wata fasaha ce da ke tabbatar da cewa mutum biyu kaɗai, wato wanda ya aika saƙo da wanda aka tura wa, ne za su iya ganin abin da ke cikin saƙon. Ko kamfanin da ya samar da manhajar ba zai iya karanta saƙonnin ba.

Sai dai masu fafutukar kare yara da jami'an tsaro sun daɗe suna adawa da irin wannan kariya, suna cewa tana bai wa masu yaɗa munanan abubuwa damar amfani da manhajojin ba tare da hukumomi sun gano su ba.

Saboda haka, wasu ƙungiyoyin kare yara sun yi maraba da matakin da Meta ya ɗauka, suna ganin hakan zai taimaka wajen daƙile yaɗuwar abubuwa masu haɗari a intanet. Amma masu kare haƙƙin sirri kuwa sun soki matakin, suna cewa hakan zai rage kariyar bayanan masu amfani da kuma 'yancin sadarwa cikin sirri.

Marks Zuckerberg 2019

Asalin hoton, Meta

Ta hanyar kashe tsarin maɓallin ɓoye saƙonni, manhajar Instagram yanzu za ta iya samun damar ganin duk abin da ke cikin saƙonnin sirri na masu amfani, ciki har da hotuna, bidiyo da saƙonnin murya.

A shekarar 2019, kamfanin Meta ya yi alƙawarin samar da wannan fasaha a dukkan manhajojinsa na saƙonni da suka haɗa da Facebook da Instagram, inda ya ce "makomar kafar ita ce sirri."

Kamfanin ya kammala saka tsarin a manhajar aika saƙo ta Facebook wato Messenger a shekarar 2023, sannan daga baya ya sanya shi a matsayin zaɓi a Instagram tare da shirin mayar da shi tsarin da zai kasance ga kowa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai bayan shekaru bakwai, Meta ya yanke shawarar dakatar da faɗaɗa amfani da tsarin a Instagram, inda yanzu manhajar za ta ci gaba da amfani da tsarin kariya na gama gari kawai.

Hakan na nufin masu kamfanonin na intanet za su iya samun damar ganin bayanan sirri idan buƙata ta taso. Wannan shi ne tsarin da yawancin manyan manhajojin intanet irin su Gmail ke amfani da shi.

Ƙungiyoyin kare yara, ciki har da NSPCC, sun yi maraba da wannan mataki. Ƙungiyar ta daɗe tana gargaɗin cewa irin wannan fasahar na iya jefa yara cikin haɗari.

"Mun yi farin ciki sosai," in ji Rani Govender daga ƙungiyar, inda ta ƙara da cewa maɓallin ɓoye sirri E2EE "na iya bai wa masu aikata laifuka damar ɓoye kansu daga ganowa, lamarin da ke ba su damar cin zarafi da yaudarar yara ba tare da an gano su ba."

Sai dai masu fafutukar kare sirri sun bayyana matakin a matsayin koma baya.

Maya Thomas daga Big Brother Watch ta ce ta "yi takaici" da matakin, tana mai cewa E2EE "na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da yara ke iya kare bayanansu a intanet, saboda haka muna fargabar cewa Meta na miƙa wuya ne ga matsin lambar gwamnati."

Abin da aka daɗe ana jira

Tun daga shekarar 2019, kamfanin Meta yana kare shirinsa na samar da tsarin maɓallin ɓoye saƙonni duk da sukar da ake yi masa, yayin da yake ƙoƙarin saka tsarin a manhajojin Facebook da Instagram.

Sai dai kamfanin bai fito fili ya sanar da janye shirin saka tsarin gaba ɗaya a Instagram ba. Maimakon haka, ya yi shiru ya sabunta ƙa'idojin amfani da manhajar a watan Maris.

"Saƙonnin da ake karewa da tsarin E2EE a Instagram ba za su ƙara aiki ba daga ranar 8 ga Mayun 2026.

"Idan wannan sauyi ya shafi tattaunawarku, za ku ga umarnin yadda za ku sauke hotuna ko saƙonnin da kuke son adanawa," in ji sanarwar.

Meta ya shaida wa manema labarai cewa an ɗauki matakin ne saboda ƙarancin masu amfani da suka zaɓi amfani da fasahar.

Wasu masana, ciki har da ƙwararriyar harkar tsaron intanet Victoria Baines, na ganin matakin na nuna yadda Meta ke kallon batun sirri.

"Kamfanonin sada zumunta suna samun kuɗi ne ta hanyar amfani da bayanan sadarwarmu, kamar wallafe-wallafe, abubuwan da muke so da kuma saƙonninmu, domin nuna tallace-tallacen da suka dace da mu," in ji ta.

"Yanzu kuma kamfanoni irin su Meta suna ƙara mayar da hankali wajen horas da tsarin basirar AI, inda bayanan saƙonni ke da matuƙar amfani."

A baya, Instagram ya taɓa cewa ba ya amfani da saƙonnin kai tsaye wajen horas da tsarin AI.

Kamfanin ya ƙi yin ƙarin bayani kan dalilin sauya matsayinsa game da kariyar sirri, yayin da shugaban Instagram Adam Mosseri ma ya ƙi amincewa da yin wata tattaunawa kan batun.

....

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Instagram, Adam Mosseri

A watan da ya gabata, Meta ya sanar da ma'aikatansa cewa zai fara tattara bayanan yadda suke amfani da na'urorin aiki domin horas da tsarin ƙirƙirarriyar basira AI ta wucin gadi.

Ƙungiyoyi masu fafutukar kare sirri irin su Big Brother Watch sun ce matakin Meta na iya yin tasiri ga sauran kamfanonin sada zumunta.

A baya, ana kallon tsarin maɓallin ɓoye saƙonni E2EE a matsayin hanyar da fasahar sadarwa ke dosa. Yanzu haka manhajojin Signal, WhatsApp, Facebook Messenger, iMessage da Google Messages suna amfani da tsarin.

Sai dai Telegram na bayar da shi ne a matsayin zaɓi kawai, ba kai tsaye ba. Haka kuma X yana da makamancin tsarin, amma masu suka na cewa bai cika ƙa'ida ba.

Snapchat na amfani da tsarin wajen hotuna da bidiyo da aka aika ta hanyar saƙonni, kuma ya ce yana shirin faɗaɗa shi zuwa rubutattun saƙonni. Ita kuwa Discord na shirin mayar da tsarin kariya ga kiraye-kirayen murya da bidiyo.

Sai dai a watan Maris, TikTok ya shaida wa BBC cewa ba shi da shirin saka tsarin a saƙonni. Bayan kwana 14, Instagram ma ya sabunta ƙa'idojinsa yana tabbatar da cewa ba zai ci gaba da saka tsarin ba.

Masana irin su Victoria Baines na ganin irin waɗannan matakai za su rage yaɗuwar tsarin E2EE ne kawai.