Twitter zai zaftare ma'aikatansa

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin shafin Twitter ya ce zai sanar da ma’aikatansa ranar Juma’a kan ko zai sallame su daga aiki bayan da Elon Musk ya sayi kamfanin.
A wata wasiƙa da ya aika masu, kamfanin ya ce zai ɗauki matakin ne domin tabbatar da shi a kan tsarin ci gaba da ya dace.
Kamfanin ya ƙara da cewa ofisoshinsa za su kasance a rufe na ɗan wani lokaci, kuma za a dakatar da amfani da katin da ma’aikata ke amfani da shi a matsayin mukulli har zuwa lokacin da zai yanke hukunci.
Hamshaƙin attajirin zai kasance babban shugaban kamfanin bayan da ya saye shi a makon da ya gabata a kan dala biliyan 44 (kwatankwacin fan biliyan 39.3).
"Za mu ɗauki mataki mai wahalar gaske na rage yawan ma’aikatanmu na duniya a ranar Juma’a,’’ in ji kamfanin a wasiƙar da ya fitar.
Bayanin ya ƙara da cewa, ‘’Mun san cewa wannan zai shafi ɗaiɗaikun mutane da yawa, waɗanda suka bai wa Twitter gudunmawa, to amma abin takaicin wannan mataki ne da ya zama dole domin tabbatar da nasarar ci-gaban kamfanin.’’
Kamfanin ya ce ba tare da ɓata wani lokaci ba za a taƙaita shiga ofisoshinsa domin tabbatar da kare lafiyar kowane ma’aikaci da kayayyakin kamfanin da kuma bayanan masu mu’amulla da shi.
An sanar da ma’aikatan cewa kowa zai samu wasiƙa ta intanet zuwa ƙarfe huɗu na yamma agogon GMT, ranar Juma’a, wadda za ta bayyana matsayin aikinsa, wato ko an sallame shi ko kuma ba a sallame shi ba.
Ƙaurar kwararrun ma’aikata
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai jita-jitar da ake yi cewa kusan rabin ma’aikatan kamfanin na Twitter 8,000 za su rasa aikinsu.
Kamfanin dai yana faman gaske wajen samun riba. Kuma ana ganin hanya ɗaya da zai magance wannan matsala ita ce ta rage yawan kuɗin da yake kashewa wajen biyan albashi.
Wani babban jami’in kamfanin na Twitter a Birtaniya, Simon Balmain, ya faɗa wa BBC cewa yana ganin an sallame shi ne saboda ya yi ƙoƙarin buɗe kwamfutarsa ta aiki da kamfanin ya ba shi ta hannu, ya shiga amma ya ga ba shi da hanya.
Jami’in ya ce, kowa ya samu wasika, wadda a ciki ake gaya masa cewa za a rage ma’aikata da yawa, kuma bayan sa’a ɗaya daga nan sai kuma mutane suka fara ganin ana share bayanan da ke cikin kwamfutocinsu can daga kamfanin, sannan an soke damarsu ta ganin wasikun Gmail.
Ya ƙara da cewa, ‘’yawancin abokan aiki na Birtaniya wataƙila suna barci ba su san me ake ciki ba. Ni ina aiki ne da lokacin Los Angeles saboda yanayin aikina, don haka idona biyu lokacin da abin ya faru.
Wani ma’aikacin na Twitter shi kuwa cewa ya yi yana nan yana zaman jiran wasiƙar, ya san ko aikinsa na nan ko kuma an sallame shi.
‘’Ƙaurar ƙwararrun ma’aikata daga wannan sallama da za a yi za ta sauya fasalin harkar fasaha, ba kamar yadda muka san fannin ba a yau.
Dukkaninmu muna ta tattaunawa da tuntuɓar juna kuma irin ƙauna da muke nuna wa juna a yanzu abin ba magana," in ji Mr Balmain.
Bloomberg, ba tare da ya bayyana inda ya samu labarin ba ya nuna cewa, kamfanin na Twitter ya buƙaci wasu daga cikin manyan jami’an da su bayar da jerin sunayen ma’aikatan da za a sallama.
Kamfanin Binance na tsarin kuɗin intanet na Cryptocurrency ya sanya jarinsa a Twitter a matsayin wani mataki na sayen kamfanin da Mr Musk ya yi.
Tun da farko shugaban kamfanin na Binance, Changpeng Zhao, ya ce rage yawan ma’akatan zai yi amfani sosai.
Mr Zhao, wanda ke jawabi a wurin taron koli na harkokin intanet (Web Summit) a Lisbon, shi ma ya soki kamfanin na Twitter na rashin fitar da sabbin tsare-tsare da abubuwa, idan aka yi la’akari da yawan ma’aikatan kamfanin.
Biyan kuɗi domin tantancewa
Rage yawan ma’aikatan ya biyo bayan matakin kamfanin na Twitter na ɓullo da tsarin yadda masu amfani da shafin za su ruka biyan dala 8 (fan 7) a duk wata domin tantance su (shuɗin maki ko Blue Mark kamar yadda kamfanin ke kiran tsarin).
Bayan amfanin samun wannan matsayi na tantancewa kamfanin na Twitter zai kuma riƙa yaɗa saƙonnin waɗanda suka biya fiye da na sauran waɗanda ba su biya ba, sannan ba za a riƙa turo masu tallace-tallace na ba gaira ba dalili ba.
Daman Mr Musk ya bayyana wannan shiri nasa da cewa: "Akwai buƙatar mu biya kuɗin ko ta yaya."
Shekaru da dama Twitter bai samu riba ba kuma yawan masu amfani da shafin kusan yana nan yadda yake kusan miliyan 300 a wata.
Ƙwararru da dama na nuna alamun cewa Mr Musk, wanda shi ne attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya, ya sayi kamfanin da tsada, idan aka yi la’akari da halin da tattalin arziƙin duniya yake ciki, da kuma raguwar darajar yawancin kamfanonin sadarwa a yanzu.
To amma tsohon jami’in sadarwa da duniya na kamfanin na Twitter Brandon Borrman, a wata hira da BBC ya nuna shakkunsa kan yadda kamfanin zai iya fayyace dalilinsa na sa a rinƙa biyansa wannan kuɗi dala 8 a duk wata, domin yi masu raba-daidai da sauran masu amfani da shafin.

Asalin hoton, MICHAEL GONZALEZ/GETTY IMAGES
Zuwa yanzu ba a san takamaimai yadda rage yawan ma’aikatan zai shafi tsarin aikin kamfanin ba.
Amma Mr Musk mutum ne da ya yi ƙaurin suna wajen takura wa ma’aikata, wajen nuna babu sani ba sabo.
Kafofin yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa tuni ma'aikata da dama suna aiki tsawon lokaci domin cimma muradun Mr Musk tun bayan da ya sayi kamfanin.
Rushe hukumar daraktoci
A matsayin wani fanni na sayen kamfanin mutane tara daga cikin manyan daraktocinsa sun bar aiki, suka bar Mr Musk, me iya yi, a matsayin darekta shi kaɗai.
Ana ganin hakan a matsayin wani mataki na tabbatar da ikon Mr Musk a kamfanin.
Daga cikin waɗanda suka bari akwai shugabansa Bret Taylor da babban shugaban Parag Agrawal. Akwai kuma wasu manyan jami’an da suka rubuta cewa suna shirin ficewa ko kuma sun fice, ciki har da babban jami’in kuɗin kamfanin Ned Segal.
Yayin da manyan ma’aikatan kamfanin ke ficewa kafofin yaɗa labarai na Amurka na cewa abokan tafiyar Mr Musk su kuma suna shiga.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











