Lokuta bakwai da Elon Musk ya janyo ce-ce-ku-ce a shafin Twitter

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yunkurin Elon Musk na sayen shafin Tuwita ya janyo zazzafar muhawara kan makomar shafin - gwamnatin Amurka ma ta nuna damuwa kan tasirin da kafofin sada zumunta ke da shi.

Sai dai bukatar Musk ta sayen Tuwita kan $44bn ya ci gaba da jan hankali musamman kan tarihin irin wallafe-wallafe da hamshakin mai kudin yake yi.

Tun bayan soma amfani da shafin a 2009, Musk ya rika jefa kansa cikin matsala, inda so tari yake fuskantar tuhuma sakamakon hakan.

Mun duba wasu daga cikin wallafe-wallafe da Musk ya yi wadanda kuma suka janyo ce-ce-ku-ce a shafin na Tuwita.

Wallafa rubutu kan ceto yaran kogon Thailand

.

Asalin hoton, Getty Images

A 2019, Elon Musk ya fuskanci tuhuma kan zargin bata suna bayan da ya kira wani kwararre wajen fito da mutane daga kogo dan Birtaniya, Vernon Unsworth da wani suna mara kyau a shafin Tuwita – tuni aka goge rubutun.

Unsworth ya zama sananne a fadin duniya shekara guda bayan jagorantar kokarin ceto matasa 12 lokacin da suka makale a wani kogo na karkashin kasa a Thailand.

Musk ya yi kokarin taimaka wa aikin da kuma son ba da gudunmawar ƙwararrun jami’ai na ruwa.

Maimakon haka, ya shiga cacar baki da Unsworth a kafar sada zumunta bayan da ya yi watsi da bukatar, inda ya kira hakan da cewa Musk yana son janyo hankalin duniya ne kawai.

Bayan kalaman da Elon Musk ya yi, Unsworth ya yi karar sa saboda zargin bata masa suna, inda ya nemi Musk din ya biya shi dala miliyan 190, sai dai, wata kotu a Los Angelese, ta yi watsi da karar.

A lokacin, lauyan Mista Unsworth, Lin Wood, ya ce "hukuncin ya nuna cewa za ka iya yin kowane irin zargi da kake so, ko da hakan ba gaskiya ba ne, ba abin da za a yi wa mutum kan haka."

Martani kan cutar korona

Elon Musk

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Elon Musk ya kasance mai yawan janyo ce-ce-ku-ce a shafin Tuwita

Lokacin da aka ayyana cutar korona a matsayin annoba a 2020, Elon Musk bai yi taka-tsantsan ba wajen yin suka ga matakai da aka sanya na kare kai daga cutar kamar dokar kulle – inda ya kira dokokin a matsayin shirme.

A wani daga cikin rubutu da ya yi wanda kuma aka fi sani a shafin na Tuwita, wadda ya wallafa a ranar 30 ga watan Yuni a shekarar, ya soki matakan da aka dauka na tantance wanda cutar ta kashe.

Duk da cewa an yi wa Mista Musk rigakafin korona, ya fito fili ya nuna adawa da rigakafin da kuma nuna bacin ransa kan kwatanta firaiministan Canada, Justin Trudeau da Adolph Hitler da kungiyoyin Yahudawa suka yi lokacin da suka yi zanga-zangar adawa da yunkurin tilasta yin rigakafin korona.

Kalubalantar Putin

Putin

Asalin hoton, Getty Images

Elon Musk ya kasance daya daga cikin manya masu fada a ji a fadin duniya da suka yi ta mayar da martani kan mamayar Ukraine da Rasha ta yi.

A ranar 14 ga watan Maris, Musk ya je shafin Tuwita, inda ya kalubalanci Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

"Ina kalubalantar Putin a kan mamayar Ukraine. Ya jefa kasar cikin barazana.’’

Daga baya ya aika sako ga shafin Tuwita na Shugaba Putin, inda ya kara nanata cewa Putin ya fito ya yi bayani kan mamayar.

Sai dai Putin din bai mayar da martani ba.

Bata ran shugaban Amurka

President Joe Biden

Asalin hoton, Getty Images

Elon Musk ya samu tagomashin rayuwa ne ta hanyar shiga kasuwanci da dama da ya hada da samar da kamfanin kera motocin latironi na Tesla, wanda ya kasance sahun gaba a kasuwancin motoci.

A watan Janairun da ya wuce, hamshakin mai kudin ya harzuka da kalaman da shugaban Amurka Joe Biden ya yi kan kera motoci a Amurka, inda Biden ya ambaci wasu kamfanoni ba tare da ambatar kamfanin Tesla ba.

Musk ya wallafa wani rubutu ran 27 ga Janairu da ke cewa "Biden mutum ne mara hankali da bai san me yake yi ba.

Wallafa rubutu a Tuwita da ya bata kimar kamfanin Tesla

Elon Musk near a Tesla electric vehicle

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wallafa rubutu da Musk ya yi a kan Tesla a shafin twita ya yi tasiri wajen shafar darajar kamfanin

Elon Musk ya jefa kansa cikin matsala da masu zuba jari a kamfaninsa na Tesla so da dama bayan jerin martani da ya yi a twita, wanda ya janyo wa kamfanin asarar kudade.

A watan Nuwamban bara, hannayen jarin Tesla ya yi kasa da kashi 5 bayan da shi Musk ya gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a a shafin twita kan ko ya sayar da wani bangare na kamfanin – inda kashi 58 wanda ya kunshi mutum miliyan 3.5 suka kada kuri’ar cewa ya sayar.

A watan Maris din 2020, Elon Musk ya janyo ce-ce-ku-ce bayan da ya wallafa cewa ya dauka hannayen jarin kamfanin sun yi sama.

Kalaman sun janyo faduwar darajar Tesla a kasuwa da ya kai $14bn.

Barkwanci na kamfanin Coca-Cola

Coca leaves

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Elon Musk ya janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan a shafin twita, bayan da ya yi wani rubutu a ranar 28 ga watan Afrilu, inda ya sanar da cewa yana son sayan kamfanin Coca-cola, domin kara hodar iblis cikin ruwan lemun da ya yi fice a duniya.

Lemun na Coca-cola da wani masanin magani dan kasar Amurka, John Pemberton ya samar a shekarun 1885, na dauke da ganyen coca, inda a wancan lokaci aka amince da amfani da hodar iblis da kuma matsayin sinadari na magani, a cewar cibiyar kula da amfani da magunguna na Amurka.

Sai dai, daga baya an cire sinadarin daga cikin lemon na coca-cola da kuma daina amfani da shi tun shekarar 1929.

Yayin da wasu mabiya bayan Elon Musk sama da miliyan 87 suka yi na’am da kalaman hamshakin attajirin na duniya, wasu kuma sun soki batun da suka kira na dabbaka amfani da muggan kwayoyi.

Wannan ba shi ne karon farko ba da Musk ke janyo ce-ce-ku-ce kan batun amfani da kwayoyi.

An gano mista Musk na shan tabar wiwi a cikin wani hoton bidiyo yayin tattaunawa da wani dan jarida Joe Rogan a 2018.

An nadi hoton bidiyon ne a jihar California da ke Amurka, inda aka amince da amfani da maganin, sai dai masu suka sun kalubalanci cewa hakan ba abu ba ne mai kyau.