Haɗurra biyar game da shan magungunan tayar da komaɗa

Asalin hoton, Getty Images
Ana samun magungunan gyara jiki wato 'supplements a ko'ina'; a shagunan sayar da magunguna, asibitoci, kasuwanni, har ma a shafukan sada zumunta.
Ana tallata su a matsayin abubuwan da za a iya amfani da su wajen magance magance matsalolin lafiya inda ake cewa suna cewa suna taimakawa wajen samun bacci mai kyau da ƙyallin fata da ƙarin natsuwa da tsawon rai da dai sauransu.
A matsayina na masanin abinci, ana yawan tambayata ko waɗannan magungunan gyaran jiki sun cancanci kuɗin da ake kashewa a kansu. Amsa ita ce ya danganta da mutum da kuma yanayi. Idan ana amfani da iƙirarin da ake yi kan supplements a intanet, mutum zai yi tunanin suna iya warkar da komai.
Duk da cewa wasu magungunan gyaran jiki suna da amfani a wasu lokuta na musamman, mutane da yawa suna fahimtar su ba daidai ba.
Har yanzu, da dama ba su san haɗari da dabarun tallace-tallace da ake ɓoyewa ba a bayan waɗannan kayayyaki.
Ga abubuwa biyar da nake so mutane su sani kafin su saya magungunan gyaran jiki wato supplements.
1. Fara da abinci ba maganin gyara jiki ba
Idan kana iya samun sinadaran da suka kamata daga abincinka na yau da kullum, hakan shi ne mafi alheri koyaushe.
Hukumar tsare-tsaren Abinci ta Birtaniya ta fayyace magungunan gyaran jiki a matsayin kaya "da aka ƙerawa don gyara rashin sinadaran da ba a samu a abinci da kiyaye shigar da isassun sinadaran da ake bukata a jiki, ko kuma tallafawa wasu ayyukan jiki na musamman."
A taƙaice, magungunan gyaran jiki suna nan ne don tallafawa wajen samar da sinadaran da babu a abincin da muke ci ba don maye gurbin abinci ba.
Abinci gaba ɗaya yana samar da fiye da kawai sinadaran da aka ware. Misali, kifi mai mai kamar **salmon** baya bayar da **mai omega-3** kawai, har ma yana dauke da **furotin, bitamin D, selenium**, da sauran sinadaran amfani ga jiki.

Asalin hoton, Getty Images
Masana kimiyya sun yi ƙoƙarin ware "sinadaran" da ke cikin 'ya'yan itatuwa da kayan lambu don kwaikwayon amfanin su a cikin ƙwaya amma ba su samu nasarar yin hakan ba. Amfanin sinadaran suna fitowa ne daga abinci gaba ɗaya, ba daga ƙwaya guda ba.
Duk da haka, akwai lokuta da magungunan gyaran jiki suke da muhimmanci. Misali, ana ba da shawarar amfani da maganin folic acid kafin da bayan juna biyu don rage haɗarin lahani ga jaririn da ba a haifa ba.
Haka kuma, maganin gyaran jiki na bitamin D ana ba da shawarar amfani da shi a lokacin sanyi.
2. Wataƙila ba ka san cewa kana shan magungunan gyaran jiki fiye da kima ba
Yana da sauƙi a sha fiye da kima cikin gajeren lokaci, wanda hakan zai iya haifar da illoli kamar amai ko gudawa.
Amma amfani da maganin gyara jiki na dogon lokaci na iya kawo mummunan sakamako ga lafiya.
Mutane da yawa suna shan na tsawon shekaru ba tare da sanin ko suna bukatarsu ba ko kuma yawan da ya wuce kima ba.
Bitamin masu narkewa a cikin mai kamar A da D da E, da K suna kasancewa ne a cikin jiki a maimakon a kashiyar da su.
Alal misali, shan sinadarin bitamin D fiye da kima na iya haddasa taruwar sinadarin calcium, wanda zai iya lalata ƙoda da zuciya, sannan ya raunana ƙasusuwa.
Shan sinadarin bitamin A dayawa na iya kawo lalacewar hanta da lahani ga jariri a lokacin ciki, da rage ƙarfin ƙasusuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ko bitamin ɗin da ke narkewa a ruwa na iya haifar da matsala, saboda amfani da bitamin B6 na dogon lokaci an danganta shi da lalacewar jijiyoyi.
Mutane da yawa ba sa duba matakan sinadaran nan a jiki da jini akai-akai ba, dalilin da ya sa sau da yawa ba sa gane cewa yanayin yadda suke amfani da su ba daidai ba ne sai alamomi sun bayyana.
3. Kada a yarda da shawarwari a kafafen sada zumunta.
Idan ka yi 'yan mintuna kan shafukan sada zumunta, za ka ga ana tallar wasu kayan maganin gyara jiki a matsayin "masu ƙarfafa garkuwar jiki, ko na tsabtace jiki." Waɗannan kalmomi suna iya zama masu jan hankali, amma ba su da tushe a kimiyya, kalmomi ne kawai na talla.
Masu talla, waɗanda sau da yawa ba su da horo na likita ko kimiyya, suna inganta kayayyakin ne da labaransune kawai ba bisa hujja ba.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa akwai wasu dokoki kan tallata kayan maganin gyara jiki, masu talla ba su cika bin su koyaushe ba.
4. Kasuwar sayar da maganin gyara jiki ta fi mai da hankali kan sayarwa fiye da kimiyya.
Kasuwar magungunar gyara jiki ta duniya tana da darajar fiye da dala biliyan 100.
Kamar kowace babbar masana'anta, burinta shine haɓaka da riba, wanda ke shafar yadda ake ƙera da sayar da kayayyaki.
Idan maganin gyara jiki yana da tasiri, likitoci ne ya kamata su ba da shawara, ba masu tasiri a kafafen sada zumunta ba.
Wasu sinadarai suna da hujjar kimiyya, kamar bitamin D, amma yawancinsu babu bayani sosai a kansu.
Da yawa ana tallatasu ne da iƙirarin ƙarya da sau da yawa mutanen da ba su da horo a harkar abinci ko kiwon lafiya ke tallatawa.

Asalin hoton, Getty Images
5. Ba kowa ne ya kamata ya sha maganin gyara jiki ba
Samun su a kasuwa ba yana nufin kowa ne ya kamata ya sha ba saboda suna haifa da illa ga waɗansu mutanen.
Misali, maganin St. John's wort na iya haifar da matsaloli idan an sha tare da wasu magungunan rage damuwa, ko ƙwai ko magungunan hawan jini.
Bitamin K na iya shafar magungunan rage jini kamar warfarin, yayin da sinadarin Iron dayawa zai iya kawo matsalolin narkewar abinci da rage tasirin wasu antibiotics.

Asalin hoton, Getty Images
Yawancin maganin gyara jiki ba a gwada lafiyarsu ga masu ciki ba. Wasu, kamar bitamin A, suna da haɗari ga ciki kuma na shafar nono.
Idan mace na da ciki ko kuma kuma tana shayarwa kuma sai ta ji ba ta da lafiya toh ta tuntuɓi likita ko ƙwararre a fannin abinci kafin amfani da kayan maganin gyara jiki.
Kayan gyara jiki na iya taimakawa idan akwai buƙata ta musamman, amma ba maganin komai bane.
Kafin kashe kudi, ya kamata mutum ya tambayi kansa; 'Ina buƙata ne ko zai fi kyau in kashe kudin a abinci mai gina jiki kawai?











