Yadda za ku tantance gurɓataccen lemo da sauran abubuwan sha a Najeriya

Wani mutum na shan abin sha

Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta bukaci 'yan kasar su dinga sanya ido sosai wajen tabbatar da ingancin abubuwan da suke saye don kauce wa kayan jabu.

Hukumar ta bayyana cewa yana da kyau mutane su dinga la'akari da abubuwa hudu kafin su sayi abin sha, kamar lemo, da barasa, da sauransu.

Wadannan abubuwa su ne wurin da mutum zai sayi abin, da farashinsa, da yadda aka kunshe shi, da kuma shi kansa abin da zai saya, don tabbatar da cewa na gaske ne ba jabu ba.

Ta yi karin haske kan wadannan muhimman matakai hudu kamar haka:

  • Wuri: A tabbatar an sayi kayan da NAFDAC ta yi wa rajista a wurare nagartattu da ke da lasisi da manyan shaguna da masu bayar da sari.
  • Farashi: Akula da cewa farashin bai gaza yadda aka saba sayar da kayan ba. Saboa idan ya cika sauki to akwai ayar tambaya.
  • Kunshewa: Yadda aka kunshe ko mazubin abin da za a saya ya zamanto ba maras kyau ba ne. A duba ko akwai kuskure a rubutun da yadda mazubi ko kunshin yake idan akwai abin da ba daidai ba. A tabbatar akwai bayanan kamfanin da ya sarrafa da suka hada da yadda za a tuntube su da adireshinsu a jikin mazubin abin shan ko makunshin. A duba ko akwai zane ko alamun tantance sahihanci a jikin mazubin ko kwalbar. Idan kana da manhajar tantance wannan alamar yana da kyau a duba ko abin da za ka saya mai kyau ne.
  • Abin saye: Ka tabbatar abin shan ba ya wari.
Abubuwan sha a kofuna

Asalin hoton, Reuters

Kiran da hukumar ta yi ya zo ne bayan wani samame da jami'anta da hadin gwiwar jami'an tsaro suka kai a wata kasuwa da ke garin Aba a jihar Abia a kudancin kasar.

An kai samamen ne kan shaguna fiye da 240 a kasuwar, wadanda suka kwashe shekaru suna sarrafa gurbatattun abubuwan sha da suka hada da nau'uka daban-daban na giya.

Haka kuma shagunan wadanda aka mayar da su tamkar masana'antu a kasuwar, na sabunta kwanan watan abubuwan da suka lalace, kamar madarar Peak, da madarar gari, da tumarin Ketchup, da kindirmo na kwali, da kuma lemukan Coca-Cola.

Kwalaben na madara

NAFDAC ta kuma yi bayani kan matsalolin da ke tattare da shan abubuwan sha gurbatattu ga lafiya. Sun hada da:

  • Tashin zuciya
  • Amai
  • Ciwon mara
  • Jiri
  • Sauyi a launin fata: zuwa shudi ko fari fat
  • Numfashi sama-sama ko a hankali
  • Raguwar dumin jiki ko suma
  • Shan gurbatattun abubuwa na iya kai wa ga samun matsalar koda da hanta, ko mutuwa baki daya