BBC ta bankaɗo kamfanin India da ke yaɗa miyagun ƙwayoyi a Afirka ta Yamma

- Marubuci, BBC Eye Investigations
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 8
Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC ya gano yadda wani kamfanin magunguna na India yake yi da kuma sayar da miyagun ƙwayoyi a ɓoye zuwa yankin Afirka ta Yamma, inda hakan ke ƙara jefa rayuwar al'umma cikin mummunan yanayi.
Kamfanin Aveo Pharmaceuticals, wanda ke birnin Mumbai, yana yin ƙwayoyin magunguna daban-daban sannan ya sanya musu suna iri-iri ya haɗa su kamar yadda ake yi wa magunguna na gaske masu amfani. To amma duka waɗannan magunguna masu suna daban-daban an yi haka ne domin ɓad da sawu - abubuwa iri ɗaya suke ɗauke da su kuma masu cutarwa - muguwar ƙwaya ce da aka haramta a Turai.
A duniya babu inda aka amince da haɗin wannan maganin wanda yana iya haddasa matsalar numfashi da kuma shiɗewa. Idan ma mutum ya sha shi da yawa zai iya mutuwa. Duk da haɗarin da ke tattare da wannan magani, yanzu ya zama ruwan-dare a ƙasashe da dama na Afirka ta Yamma, saboda yana da arawa da kuma sauƙin samu.
BBC ta gano fakiti-fakitin wannan magani da tambarin kamfanin Aveo ana sayarwa a titunan Ghana da Najeriya da kuma Ivory Coast.
Bayan gano inda ake yin maganin a wannan kamfani na India, BBC ta tura wani mutum kamfanin inda ya yi ɓad da kama a matsayin ɗankasuwa daga Afirka da yake son sayen maganin ya kai Najeriya.
Ta hanyar amfani da na'urar ɗaukar hoto ta sirri, a yayin tattaunawar BBC ta ɗauki bidiyon ɗaya daga cikin manyan shugabannin kamfanin na Aveo, Vinod Sahrma, inda ya nuna wannan muguwar ƙwaya da BBC ta gano a ƙasashen Afirka ta Yamma.
A hoton bidiyon ɓoye da aka ɗauka na wannan ganawa wakilin BBC da ya yi shigar-burtu ya gaya wa darektan shirinsa na kai wannan magani Najeriya domin sayar wa matasa, waɗanda ya ce suna son ƙwayar sosai.
Sharma ya ji daɗin wannan magana, sannan ya gaya masa cewa idan mutum ya sha wannan magani, ƙwaya biyu ko uku a lokaci ɗaya zai ji daɗi kuma ya bugu. A can wajen ƙarshen ganawar Sharma ya fito da maganar fili : ''Wannan ba ƙaramar illa yake yi ga lafiya ba,'' amma ya ƙara da cewa, '' ka san yanzu a zamanin nan, wannan harka ce ta kasuwanci.''
Kasuwanci ne da ke yin illa ga lafiya da kuma ɓata rayuwar miliyoyin matasa a faɗin Afirka ta Yamma.
A birnin Tamale da ke arewacin Ghana matasa da dama na shan miyagun ƙwayoyi, lamarin da ya sa ɗaya daga cikin shugabannin garin, Alhassan Maham, ya kafa wata ƙungiya ta 'yan-sa-kai mai kusan mutum 100, da ke dirar mikiya a kan diloli masu sayar da ƙwayoyin suna ƙwacewa.
maham ya sheda wa BBC cewa ƙwayar ya cutar da mai shanta da yawa kamar yadda kalanzir ke yi da wuta. ''Wani mai ta'ammali da ƙwayar a Tamale, ya fito da abin fili inda ya ce ƙwayar ta, ''lalata mana rayuwa.''
Ayarin BBC ya bi waɗannan 'yan-sa-kai na Tamale aiki bayan da aka tsegunta musu wani labari na cinikin ƙwayoyin, inda nan da nan suka hau babura suka yi dirara-mikiya a wasu unguwannin talakawa. A kan hanya sun ga wani matashi yashe a titi bai san inda yake ba, inda mazauna unguwar suka gaya musu cewa ya sha ƙwaya ne.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lokacin da aka kama dilan, yana ɗauke da wata jakar leda cike da korayen ƙwayoyin da aka rubuta sunan Tafrodol a jikinsu. Haka kuma fakitin maganin na ɗauke da tambari da sunan kamfanin magani na Aveo Pharmaceuticals.
Ba a Tamale ba ne kaɗai ƙwayoyin suke illa da ta'annati ba. BBC ta gano irin ƙwayoyin da 'yansanda suka ƙwace a wasu wuraren a Ghana.
Haka kuma BBC ta gano ana sayar da waɗannan ƙwayoyi a tituna da unguwannin Najeriya da Ivory Coast, inda matasa ke zuba su a cikin giyar gwangwani mai ƙara kuzari domin ƙara wa ƙwayar ƙarfi.
Bayanai sun nuna cewa kamfanin Aveo Pharmaceuticals, da wani kamfanin da suke da alaƙa tare da ake kira Westfin International suna kai miliyoyin wannan ƙwayar Ghana da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.
Najeriya mai yawan al'umma miliyan 225, ta kasance inda aka fi hada-hadar ƙwayoyin - alkaluman hukumar ƙididdiga ta ƙasar sun nuna cewa kusan mutum miliyan huɗu ne a ƙasar ke ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.
Shugaban hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a ƙasar, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ya gaya wa BBC cewa miyagun ƙwayoyi na lalata rayuwar matasa da iyalai a kowace al'umma a Najeriya.

A 2018, bayan da Sashen Binciken ƙwaƙwaf na BBC ( BBC Africa Eye ) ya yi wani rahoto bayan bincike a kan sayar da miyagun ƙwayoyi a titunan Najeriya, hukumomin ƙasar sun yi ƙoƙarin ɗaukar matakin yaƙi da wani maganin kashe ciwo (na tramadol).
Gwamnati ta haramta sayar da maganin (tramadol) ba tare da umarnin likita ba, sannan ta sanya doka a kan yawan da mutum zai iya sha tare kuma da ɗaukar mataki kan shigar da maganin ba bisa ƙa'ida ba. Haka su ma a ɓangarensu hukumomin India sun tsaurara matakai a kan fitar da maganin na tramadol.
Ba a daɗe da ɗaukar wannana mataki ba sai kamfanin Aveo Pharmaceuticals ya fara fitar da wannan sabuwar ƙwaya wadda ma ta fi waccan da aka ɗauki matakan daƙile ta, ƙarfi.
Jami'an ƙasashen Afirka ta Yamma na gargaɗi cewa masu kasuwancin fitar da wannan ƙwaya wadda ta maye waccan da aka ɗauki mataki a kanta sun ɓullo da sabuwar dabara ne domin kauce wa kamu.
A wannan ma'aikata ta India ta Aveo akwai katan-katan cike da ɗakuna. Wannan babban jami'i na kamfanin, Vinod Sharma ya zube, ƙwayoyin iri-iri a kan teburinsa, da suna daban-daban, kamar, Tafrodol, wanda ya fi fice da TimaKing da kuma Super Royal-225.
Ya gaya wa wakilin BBC da ya yi shigar-burtun cewa masana kimiyya na kamfanin na iya haɗa abubuwa daban-daban su samar da wata sabuwar ƙwaya.
Sabuwar ƙwayar da kamfanin na Aveo ya yi ta ma fi wadda aka haramta ta turamadol illa in ji Dr Lekhansh Shukla, mataimakin farfesa a cibiyar nazarin lafiyar ƙwaƙwalta ta India da ke Bengaluru (National Institute of Mental Health and Neuro Sciences in Bengaluru)
"Ƙwayar za ta iya hana mutum numfashi idan aka sha ta da yawa, ka ga wannan ta'ammali ne da miyagun ƙwayoyi..."
Wannan magani (Carisoprodol) an haramta amfani da shi a Turai saboda yana zame wa mutum jiki, ya kamu da jarabar shanshi. A Amurka an yarda a yi amfani da shi amma tsawon mako uku kawai.
Alamu da abubuwan da mutum kan gamu da su a sanadiyyar dakatar da amfani da ƙwayar sun haɗa da fargaba da damuwa da rashin bacci da kuma jiye-jiye da gani-gani.

Dakta Shukla ya ce bai san inda aka taɓa wani gwaji na amfani da wannan haɗi ba, ba kamar turamadol wanda shi magani ne da aka yarda a yi amfani da shi zuwa wata iyaka - ''amma shi wannan sabon ba amagani ba ne da aka amince da amfani da shi ba a ƙasar mu.''
Kamfanonin magunguna a India ba su da dama a hukumance su yi wani magani su fitar waje ba tare da lasisi ba, har sai sun kai matsayin na ƙasar da za a kai su.
Hukumomin Ghana sun tabbatar da cewa wannan sabuwar ƙwayar da kamfanin Aveo ke shigarwa ƙasar ta saɓa wa dokokin India.
Da muka nuna wa Vinod Sharma da kamfanin na Aveo Pharmaceuticals zargin wannan keta doka ba su ce komai ba.
Hukumar da ke sa ido da kula da harkokin samar da magani ta India (CDSCO) ta gaya wa BBC cewa gwamnatin ƙasar na ɗaukar batun lafiyar jama'a a ƙasashen duniya da muhimmanci saboda haka tana ƙoƙarin tabbatar da bin doka ga kamafonin magunguna a ƙasar.
Hukumar ta ce ko a baya-bayan nan ta tsaurara matakai a kan kamfanonin tare da yin kira ga ƙasashen da ake kai magungunan India su haɗa hannu da ita wajen ɗaukar tsauraran matakai na hana algus ko saɓa wa doka.
Hukumar ta kuma ce a yanzu ta ɗauki wannan magana tare da ƙasashen da ake kai wa na Afirka ta Yamma domin gudanar da bincike. Kuma ta ce za ta ɗauki matakin gaggawa na ba sani ba sabo a kan duk kamfanin da aka gano yana da hannu wajen aikata ba-daidai.

Aveo ba shi kaɗai ba ne kamfanin India da ke yin ƙwayoyin da doka ba ta bayar da izinin yi tare da fitar da su ƙasashe ba. Bayanai sun nuna cewa akwai wasu kamfanonin da su ma suke yin irin waɗannan ƙwayoyi da wani sunan daban, waɗanda su ma suna na watse a Afirka ta Yamma.
Waɗannan kamafanoni suna ɓata sunan ƙasar ta India wadda aka san ta yi fice wajen yin magunguna masu inganci da duniya ke amfani da su. Magunguna da suka ceto rayuwar miliyoyin mutane.
Fannin magungunan na India na fitar da magunguna zuwa waje da suka kai na aƙalla dala biliyan 28 a shekara.
Da yake yi wa BBC bayani a kan ganawar da ya yi da wannan jami'in kamfanin maganin na India, wakilin na BBC da ya yi shigar-burtu wanda muka sakaya sunansa don kare lafiyarsa ya ce, '''yanjarida sun daɗe suna bayar da rahoto a kan wannan magana ta wannan ƙwaya tsawon sama da shekara 20.
Ya ce, a ƙarshe ya yi nasarar yin gaba da gaba da ɗaya daga cikin mutanen da ke da hannu dumu-dumu a harkar miyagun ƙwayoyin a Afirka, wanda ke yi da kuma fitar da su zuwa ƙasashenmu a sunduƙai ko kwantaina-kwantaina.
Mutumin ya san illar da ke tattare da harkar amma bai damu ba yana mai cewa, ''to ai kasuwanci ne kawai."
Idan muka koma Tamale, Ghana, ayarin BBC ya bi 'yan-sa-kai a wani farmaki da suka kai inda suka kama ƙwayoyin kamfanin na Aveo (Tafrodol).
A wannan yamma 'yan-sa-kan sun tara ƙwayoyin suka kama inda suka ƙona su a fili bainar jama'a, domin zama gargaɗi ga masu ta'ammali da su.
To amma duk da wutar da 'yan ɗaruruwan fakiti-fakitin ƙwayoyin na Tafrodol ke ci a lokacin, manyan masu sayarwa da safararsu a can ƙasar India suna ci gaba da samar da miliyoyin ƙwayoyin kuma suna ƙara kuɗancewa da wannan baƙara kadara.








