An kama mutumin da ya 'sayar' wa BBC kodin

Rudunar 'yan sandan Najeriya ta kama Chukwunonye Madubike, tsohon ma'aikacin kamfanin hada magunguna na Emzor Pharmaceuticals a kan hanyarsa ta tserewa zuwa jamhuriyar Benin.
Chukwunoye Madubike ya sayar wa wadansu 'yan jaridan BBC wadanda suka badda kama maganin tari mai dauke da sinadarin kodin lokacin da suke binciken yadda matasa ke amfani da shi ba bisa ka'ida ba a kasar.
Mai magana da yawun rudunar 'yan sandan a jihar Legas, Chike Oti, ya shaida wa BBC cewa, an kama shi ne a iyakar Idiroko, yayin da ya ke neman tserewa zuwa babban birnin kasar Benin, Cotonou.
Ya kuma kara da cewa yanzu abin da zai biyo baya shi ne a gurfanar da shi a kotu.
Chukwunonye Madubuike yana daya daga cikin mutanen da BBC ta tona asirin yadda suke amfani da sinadarin kodin ba bisa ka'ida ba a Najeriya, a watan Mayun bana.
Gwamnatin Najeriya ta haramta shigo da kodin kasar bayan BBC ta wallafa labarin.








