Alamomi 8 na gane kuna da ciwon suga

Asalin hoton, Getty Images
Ciwon suga cuta ce ta mutu-ka-raba da ke sanadin mutuwar mutum miliyan ɗaya a kowace shekara kuma kowa zai iya kamuwa da ita.
Abin da ke haifar da wannan ciwo shi ne idan jiki ya kasa sarrafa dukkanin sinadarin sukarin (sinadarin glucose) da ke cikin jini;.
Hakan na iya haifar da bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki da makanta da ciwon ƙoda da kuma yanke wa mutum gaɓɓai.
Kuma matsala ce da ke ci gaba da ƙaruwa, inda aka yi ƙiyasin mutane miliyan 422 suna fama da ciwon suga a faɗin duniya-ninki huɗu a kan yadda yake shekaru 40 da suka gabata, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Duk da hatsarinsa, rabin mutanen da ke ɗauke da ciwon suga ba su san suna da shi ba.
Alamomin cutar
Akwai wasu alamomi da mutum zai iya gani a yanayin jikinsa, inda da zarar ya ga alamun to ya kamata a ce ya garzaya asibiti domin a duba a tantance shi ko ya kamu da wannan cuta ta suga.
Wasu daga cikin waɗannan alamu sun haɗa da:
- Yawan ƙishirwa: Mutum zai ji yana jin ƙishirwa sosai akai-akai - wannan kuwa na kasancewa duk da yadda mutum yake yawan shan ruwa domin yana fitar da wannan ruwa da yake ta sha ta hanyar yawan fitasari.
- Yawan fitsari mai yawa: Mutum zai riƙa yawan jin fitsari, inda za ka ga da zarar ka yi fitsari zuwa wani lokaci ba mai daɗewa ba ka sake buƙatar ka sake zuwa ka yi fitsarin musamman da daddare.
- Yawan jin gajiya: Mutum ya riƙa jin gajiya sosai kuma ba lalle ya yi wani aiki ko wani abu da ya kamata ya ji wannan gajiya ba.
- Rama ta babu gaira babu dalili - idan ka ga kana ramewa haka kawai ba tare da kana fama da wata larura ba, ko wani yanayi da kake ciki na rashin cin abinci ba, to yana da kyau ka je a duba ka a asibiti.
- Saurin jin yunwa: Saurin jin yunwa sosai na iya kasancewa wata alama ta kamuwa da ciwon suga - ta yadda za ka ga duk da cewa kana cin abinci akai-akai amma kuma zai riƙa jin yunwa sosai.
- Gani dishi-dishi: idan ka ga sauyi a yadda idonka yake, yadda a baya idonka yake garau kana iya gani sosai, sai ya kasance ba ka gani kamar yadda ka saba sai dishi-dishi, ko a kan wannan ma ya kamata ga hanzarta ganin likita.
- Rashin warkewar rauni: Raunin da ba ya warkewa ko kuma ya ɗauki tsawon lokaci ƙi warkewa shi ma alama ce da ka iya haifar da ciwon suga.
- Ciwon baki mai nacin tsiya: Ciwon baki da ake kira da "mouth ulcers" wanda zai iya kasancewa ka kamu da ciwo a bakinka yayi ta tsananta, duk da matakan da kake ɗauka na maganinsa.
Waɗannan na daga cikin fitattu ko manyan alamomi na cutar suga, saboda haka da zarar ka ga wata alama daga cikinsu a tattare da kai to sai ka hanzarta zuwa asibiti inda za a yi ma gwajin wannan cuta.
Hanyoyin kauce wa kamuwa da ciwon suga
Likitoci na cewa kamuwa da ciwon suga ya danganta ne da ƙwayoyin gado da kuma wasu abubuwa masu nasaba da yanayin rayuwa da muhalli, amma za ka taimaka ka kula da yawan suga da ke shiga cikin jininka ta hanyoyi da dama kamar haka:
- Cin abinci mai gina jiki da kuma gudanar da rayuwar da ba ganganci a cikinta.
- Kauce wa abincin gwangwani da kayan ƙwalama da lemon kwalba da komawa cin abinci dangin alkama a maimakon cin na fulawa da taliya wannan matakin farko da ya dace.
- Suga da hatsi da aka sarrafa suna da ƙarancin abubuwa masu gina jiki saboda an raba su da wasu abubuwa masu amfani a cikinsu - waɗannan irin abubuwa sun haɗa da burodin fulawa da shinkafa da taliya da danginta da kayan zaƙi da alawa da kayan karin kumallo da ake ƙara musu sukari.
- Abinci mara lahani ya ƙunshi kayan ganye da ƴaƴan itatuwa da wake da kuma dangin alkama.
- Har wa yau, ya ƙunshi duk dangin mai marasa lahani da kifin gwangwani da danginsa.
- Yana da muhimmanci a dinga cin abinci lokaci bayan lokaci kuma ka dakata da cin abinci idan ka ƙoshi.
- Shi ma motsa jiki zai taimaka wajen rage yawan suga da ke cikin jininka.
- Motsa jiki: Hukumar Lafiya ta Burtaniya (NHS) ta bayar da shawarar a dinga motsa jiki na tsawon sa'a biyu da rabi a mako ɗaya, wanda ya haɗa da sassarfa da hawa matattakala da sauransu.
- Kamewa daga shan taba: Yana kuma da muhimmanci kar ka sha taba sannan ka kula da yawan kitse ko maiƙon da ke jininka domin rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya.
Waɗannan hanyoyi na daga cikin waɗanda mutum zai bi domin kare kansa daga kamuwa ko idan ta riga ta kama ka, ka samu sauƙin wannan cuta ta mutu-ka-raba ta suga.











