Abinci 7 da za su taimaka muku wajen rage ƙiba

Mace na yanka kayan girki

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Rage ƙiba na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da mutane da yawa ke ƙoƙarin cimmawa a wannan zamani.

Duk da cewa motsa jiki da rage cin abinci mai maiƙo na da muhimmanci, akwai wasu jerin abinci da ke taimaka wa jiki wajen ƙona kitse da rage ƙiba cikin sauƙi.

BBC ta tattauna da Dr Auwal Musa Umar, ƙwararren likita a fannin abinci, kuma shugaban ƙungiyar masana fannin abinci a Najeriya, reshan jihar Kano.

Ya ce ko shakka babu akwai jerin abinci da bincike ya nuna cewa suna iya rage ƙiba bisa la'akari da sanadaran da suke ɗauke da su, wanda hakan zai taimaka wa mutanen da ke neman rage ƙiba.

Gauta/Ɗata

Hoton gauta

Ƙwararren ya ce bincike ya tabbatar da cewa akwai sanadarai kamar na fiber da gauta ke ɗauke da shi da ke taimakawa wajen rage ƙiba duba da yanayin yadda jiki yake markaɗa shi, yake amfani da shi.

Gauta kuma yana cika ciki cikin hanzari, mutumin da ya ci gauta zai ɗauki dogon lokaci bai buƙaci abinci ba, hakan na rage son cin abinci da yawa.

Sinadarin fiber da ke cikin gauta na taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauƙi wanda ke rage kumburi da girman ciki.

Lemun tsami

Hoton lemu

Asalin hoton, Getty Images

Dr Auwal ya ce lemun tsami na ɗauke da sanadaran da ke taimakawa wajen narkar da kitse ko kuma hana kitsen ya ci gaba da taruwa ba bisa ƙai'da ba.

Ya kuma ce "lemun tsami na tsabtace hanji, kuma yana rage sha'awar cin abinci mai yawa."

Haka kuma lemun tsami na taimakawa wajen rage kumburin ciki, da narkewar mai a cikin hanji, sannan yana ƙara yawan ruwa a jiki wanda yake da muhimmanci wajen rage ƙiba, in ji ƙwararren.

Girfa (Cinamon)

Hoton cinamon

Asalin hoton, Getty Images

Girfa, wato Cinamon ita ma tana ɗauke da sanadaran da sukan iya narkar da kitse ko kuma sukan hana ƙiba ta taru fiye da kima, in ji ƙwararren.

Dr Auwal ya kuma ce girfa tana taimakawa wajen daidaita sukarin jini wanda yake hana jiki tara kitse da yawa, tana kuma ƙara yadda jiki ke kona maiƙo, hakan na taimakawa rage kitsen ciki.

Ya ƙara da cewa girfa tana taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauƙi tare da rage kumburin ciki.

Idan aka haɗa girfa a shayi ko shinkafa ko kunu, yana iya sa a ji ciki ya cika da wuri.

Girfa tana kuma ɗauke da sinadarin antioxidants da ke taimaka wa jiki rage kumburi da ke da alaƙa da kiba.

Gurji

Hoton gurji

Asalin hoton, Getty Images

Gurji, in ji Dr Auwal shi ma yana ɗauke da ruwa da tsoka waɗanda ba sa bari kitse ya ci gaba da taruwa, haka nan yana ɗauke da sanadarin fiber da ke taimakawa wajen tsabtace hanji da rage yawan son cin abinci.

Ya ƙara da cewa gurji ba ya ɗauke da sanadarin kalori sosai. Idan mutum ya ci shi, zai ji cikinsa ya cika, sannan ya ƙara da cewa yana taimakawa wajen rage sha'awar cin abinci

"Saboda ruwan da yake dauke da shi, idan ka ci gurji kafin abinci, kana jin ka koshi da wuri."

Citta

Hoton citta

Asalin hoton, Getty Images

Ƙwararren ya bayyana cewa citta, musamman ɗanya tana da sanadarai waɗanda ke hana kitse taruwa a jikin ɗan'adam ko kuma su ƙonar da kitsen ko narkar da shi.

"Citta na taimakawa wajen rage kiba saboda tana ƙara haɓɓaka yadda jiki ke sarrafa abinci.

Tana taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauri, sannan tana rage kumburin ciki wanda yake sa ciki ya yi girma," in ji shi.

Ya kuma ce citta tana iya rage sha'awar cin abinci sosai, musamman cin abubuwan zaƙi.

Citta tana ɗauke da sanadarai masu amfani kamar 'gingerol' da 'shogaol' da wasu sinadaran da ke kashe guba a jikin ɗan'adam.

Kanumfari

Hoton kanumfari

Asalin hoton, Getty Images

Kanumfari yana da matuƙar muhimmanci, in ji Dr Auwal saboda bincike ya tabbatar da cewa wannan kayan abinci yakan iya hana kitse taruwa ko kuma ya taimaka wajen narkar da kitse.

Ya ce wannan kayan abinci na taimakawa ƙwarai wajen rage ƙiba da ingata lafiya.

Ya shawarci mutane su dage da yawan amfani da shi a cikin abincinsu ko abin shansu.

Zogale

Hoton zogale

Asalin hoton, Getty Images

Ƙwararren ya ce zogale na ɗauke da sanadarin da ka iya hana kitse yaɗuwa a jiki, ko rage yawan kitsen da ke cikin abinci.

Zogale na da sinadarin fiber mai yawa wanda ke cika ciki da wuri, hakan yana rage yawan abincin da mutum ke ci, in ji shi.

Haka kuma, zogale na taimakawa wajen daidaita sukarin da ke cikin jini.

Zogale na ɗauke da sinadarin vitamin C da vitamin A da calcium da iron da potassium, da wasu sanadaran da ke taimaka wa jiki wajen narkar da kitse da abinci da rage kumburi, da kiyaye lafiya gaba ɗaya.

Ita ma Dr Fatima Usman, ƙwararriya a fanni abinci ta lissafo wasu ƙarin abinci da za su iya taimakawa wajen rage ƙiba da suka haɗa da;

  • Kayan lambu ko ganyayyaki kamar alayyahu da ganyen salad saboda suna ɗauke da sanadaran fibre, da kuma ƙaranci sanadarin kalori, kuma suna sa wa mutum ya ji cikinsa a cike.
  • Ƴaƴan itatuwa kamar su tuffa da inabi da ƴaƴan yazawa da na almond, da kankana da avocado suna ɗauke da sanadaran fibre da ruwa waɗanda yake cika ciki da kuma ya rage yawan cin abinci.