Wane adadin sukari mutum ke buƙata a kullum domin guje wa kamuwa da ciwon suga?

Asalin hoton, BBC, Getty Images
- Marubuci, Global Journalism team, World Service
- Marubuci, Near East Visual Journalism team, World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Yana da kyau kowa ya san adadin sukarin da jikinsa yake buƙata. Mutum zai iya cin abinci mai ɗauke da sinadarin sukari fiye da ƙima ba tare da ya ankara ba, kuma idan sinadarin ya yi yawa, mutum zai iya kamuwa da cutar sukari da ciwon zuciya da ma cutar kansa.
A duniya baki ɗaya mutane suna ta yunƙurin kula da yanayin cimakansu a gomman shekarun da suka gabata musamman saboda yadda cutar tsananin ƙiba da cutar sukari suke ƙaruwa.
Ana hasashen nan da shekarar 2050 sama da rabin mutane masu girma, da ɗaya bisa ukun ƙananan yara za su kamu da cutar sukari ko ƙiba da ta wuce ƙima, kamar yadda alƙaluman The Lancet ta bayyana.
Ɗaga daga cikin manyan matsalolin da suke hana mutane kula da yanayin ƙibarsu akwai ɓoyayyen sukari da ke cikin madarar yoghurt da burodi da salad da sauransu.
A daidai lokacin da ake shirin ranar cutar Diebetes ta duniya wanda za a yi ranar 14 ga Nuwamba, mun yi nazari kan adadin sukari da ya kamata mutum ya ci da kuma matakann da za a iya bi domin rage illolin yawaitar sukari.
Me ake nufi da 'free sugars'?
Yogurt da ruwan kayan lambu da sauran maƙulashe da zarar an gansu, za a yi tunanin an samu kayan kari masu kyau. Amma abin da zai ba ku mamaki shi ne idan mutum ya karya da irin waɗannan abincin, kafin rana jikinsa zai samu sinadarin sukari sama da adadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gindaya mutum ya samu a rana.
Ana buƙatar manya su samu adadin giram 30 ne na sinadarin sukarin 'kyauta' wato free sugar a kullum.
Idan aka ce 'free sugar' ana nufin ƙarin sinadarin sukari da aka samu a cikin abinci ko abin sha da aka sarrafa, da kuma waɗanda ake iya samu a cikin zuma da sauransu.
Yadda jiki ke sarrafa sukari ya bambanta, kuma yana da alaƙa da yanayin adadinsa a cikin abincin.
Idan adadin sukari ya riƙa hauhawa a jikin mutum na tsawon lokaci, wata matsalar da za ta iya faruwa ita ce sinadarin insulin zai rage ƙarfi wajen aiki.
Haka kuma yadda abincin gwangwani ya ƙara yawa na taimakawa wajen ƙara yawan sukari a jikin mutane, sama da abin da aka saba gani a shekarun baya.
Yawancin abincin da aka sarrafa, kamar nama da kifi da sauransu, duk ana saka musu abubuwan da za su taimaka musu wajen daɗewa, kuma a yawancin sinadaran adana abinci akwai sukari da gishiri.
Ɗanɗano mai daɗi

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A duniya ana cin na'ukan abinci masu ɗauke da sinadarin sukari sama da yadda ake yi a shekarun baya, duk da ƙaruwar wayar da kai da ake yi game da illolin haka.
Masana kiwon lafiya na duniya sun ce amfani da sinadaran da ke ɗauke da sukari ya fi yawa a ƙasar Amurka, amma lamarin na ƙaruwa a India da China da Pakistan da Indonesia.
Idan yanayin ƙiba da ta wuce ƙima ta ci gaba, ana hasashen masu ƙibar wuce ƙima za su ƙaru zuwa kashi 57.4 a tsakanin maza, da kuma kashi 60.3 a tsakanin mata zuwa 2050 kamar yadda alƙaluman The Lancet suka nuna a watan Maris bayan ƙididdigar da ya gudanar a ƙasashe 200 na duniya.
Nan da shekara 25, ana hasashen China da India da Amurka ne za su wuc gaba wajen ƙasashen da suka fi mutane masu ƙibar wuce ƙima.
A nahiyar Afirka, ana hasashen adadin masu ƙibar wuce ƙima a Najeriya za su ƙaru da kusan kashi nan da wani ɗan lokaci.
Sai dai za mu iya kula da yanayin cimakanmu domin rage wannan adadin da ma kula da lafiyarmu.
Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta bayar da shawarar a rage amfani da na'ukan abinci da suke ɗauke da ƙarin sukari, inda ta ce bai kamata ƙarin sukarin ya haura kashi 10 ba, ko kuma ƙasa da kashi biyar idan so samu ne. Kwatankwacin ƙaramin cokali shida ke nan a kullum.
WHO ta kuma ce a riƙa lura da yanayin nauyi da tsarin mutum BMI, wanda da shi ake iya lissafa yanayin ƙibar mutum.
Shin ana gane haƙiƙanin ƙiba da lambobin BMI?
Likitoci na amfani da lambobin BMI domin fahimtar yanayin ƙibarka ta hanyar amfani da tsawo da nauyinka.
Amma ana ganin ba hanya ba ce da ta fi dacewa, kuma tana da wasu matsalolin. Sannan a tsarin BMI ba a duba nau'in maiƙon da ke jikin mutum, kuma ba a la'akari da shekaru da jinsi.
Wannan ya sa a watan Janairun da ya gabata cibiyar kula da lafiya ta Birtaniya wato NICE ta ƙirƙiro hanyar da take ganin za ta dacewa wajen auna yanayin ƙibar mutum da nauyinsa domin amfani da su wajen gane cututtuka.
Hanyar da ake lissafi
Domin fahimtar yadda lamarin yake da kyau, mun zaɓi wasu na'ukan abinci sannan muka tantance adadin sukarin da ke cikin kowane abinci mai nauyin giram100. Da haka ne muka gane adadin cokalin sukarin da ke cikin kowane nau'in abinci ta hanyar amfani da giram 4 na sukari a duk ƙaramin cokali.
Domin sanin haƙiƙanin hanyoyin da za a bi wajen ƙona sukari, Farfesa Nicholas Sulthopre na Jami'ar West Scotland ya yi amfani da tsarin Atwater wanda ke bayyana yanayin ƙarfin jiki wato energy da mutum ke buƙata a kullum.
A sinadarin carbohydrates, ana buƙatar kcal 4 a kullum.










