Shin rashin tsafta ne ke haifar wa mata ciwon sanyi a al'aura?

Cutukan sanyi fiye da miliyan ɗaya ake kamuwa da su kullum a duniya, kuma mafi yawa larurori ne da ba sa nuna wata alama, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.
Cutuka ne da kan shafi al’aura waɗanda a Turance akan kira su ‘vaginitis'.
Ciwon sanyi, suna ya tara, in ji Dr Yamuna Aminu Ƙani, likitar mata kuma malama a Jami'ar Tarayya ta Dutse da ke jihar Jigawa a Najeriya.
"A shekarun baya, idan ana maganar ciwon sanyi, ana batu ne a kan ciwukan da ake ɗauka sakamakon alaƙar auratayya ko jima'i, amma yanzu kusan duk wani ciwo da ke taɓa matancin mace, ana kiransa da suna ciwon sanyi."
A cewar likitar, idan aka samu wani yanayi garkuwar jikin mutum ta sauka, saboda wata rashin lafiya ko ciwon suga ko wani abu daban, to yakan sanya wasu ƙwayoyin halitta da ke bin wani sashen jiki, su shiga wani sashe.
Sinadaran da ke cikin wasu abubuwan da wasu mata kan shafa a al’aura, kamar man shafawa da turare, kai a wasu lokuta ma har da irin suturar da mace ke sanyawa, suna iya zama sanadin shigar ƙwayoyin cutuka.
Bincike ya nuna cewa kashi 75% na mata kan yi fama da irin waɗannan cutuka aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu, yayin da rabin mata a duniya kan yi fama da su, sau biyu ko fiye.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce wasu daga cikin nau'o'in waɗannan cutuka da aka fi fama da su, akwai ciwon sanyi na chlamydia da gonorrhoea da syphilis da kuma trichomoniasis.
Dr Yamuna Ƙani ta ce cutukan sukan kasance ne, idan an samu akasi, ƙwayoyin cuta da ke bin hanyar bayan gida, suka dawo suka shiga gaban mace.
"Mace za ta iya shiga damuwa ko ta riƙa jin ruwa yana fita daga matancinta, ko kuma wani lokaci, ta samu tsaiko wajen samun juna biyu," in ji likitar.
Abubuwan da ke ƙara hatsarin ɗaukar ciwon sanyi a al'aura?
Wasu abubuwan da ke ƙara hatsarin kamuwa da cutukan al’aura ga mata su ne:
- Yawan amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) ko kuma na hana haihuwa.
- Samun juna-biyu
- Kamuwa da cutuka masu raunana garkuwar jiki
- Ciwon suga idan ba a shan magani.
Ta yaya rashin tsafta ke haifar da cutukan al’aura?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
- Zama a cikin sutura mai danshi
- Rashin sauya kamfai idan an yi gumi
- Rashin kyakkyawan sanin yadda ake tsarki
- Amfani da ƙyallen al’ada wanda aka baɗa masa turare ko kuma shafa wa al’aura turare kai-tsaye.
Wata ƙwararriyar likitar mata a Najeriya, Dakta Hafsat Umar ta ce mata su guji sanya turare a al'aurarsu, saboda yana da illa matuka.
Likitar ta ce al'aurar mace, an halicce ta ne da wasu ƙwayoyin halitta (vaginal flora), waɗanda aikinsu shi ne su kare wajen daga saurin kamuwa da cutuka.
Su kuma waɗannan kwayoyin halitta ba a so a dinga sa musu wani sinadari mai ƙarfi, don kuwa iya zai kashe su. "Da sun mutu kuma, to al'aurar za ta zama ba ta da kariya nan da nan cuta za ta iya shiga," in ji Dr Hafsat.
Dr. Yamuna kuwa ta ja hankali ne game da yawan shan magunguna barkatai na antibiotics.
A cewarta, yawan amfani da magunguna kamar su ja da yalo da filajin na tsawon lokaci, na haddasa mutuwar ƙwayoyin halittu masu yaƙi da cutuka a gaban mace kamar (lactobacilli), kuma idan aka rasa su.
Ƙwayoyin cuta waɗanda a baya ba su da ƙarfin da za su yi wani tasiri a jikin mutum kamar candida, a yanzu sai su samu dama.

Mene ne alamomin ciwon sanyi?
Alamomin ciwon sanyi suna kamanceciniya da juna, a wani lokaci ma suna yin kamanceceniya da cutukan da ba na sanyi ba.
Dr Hafsat ta ce a wasu lokutan mace kan yi fama da wani nau’i na ciwon sanyi, amma ba za ta iya ganewa ba, har sai ya kai matakin da zai yi tsanani.
''Kowanne nau'in ciwon sanyi yana da alamunsa misali, wasu matan za su ce suna fama da matsanancin ƙaiƙayi wanda idan suna sosawa har yana fidda jini.
Wasu kuma za su ce wani farin ruwa mai kauri kamar madara yana fita daga matancinsu, yayin da wasu su ce idan ciwon sanyi ya shige su suna jin zafi a lokacin al'ada ko idan ana saduwa da su.''
Ƙaiƙayin gaba shi ne babbar alamar kamuwa da ciwon sanyi, daga nan sai fitar ruwa mai kalar cikwi ko kore ko ruwan ƙasa, ko kuma mace ta dinga jin ƙarnin ƙwai ko kifi yana tashi daga ruwan da yake fita daga matancinta.
Bayyanar ƙurarraji ko wani miki a gaban mace ko namiji na daga ƙarin alamomin cutukan sanyi, cewar Dr Yamuna Ƙani.
"Ko wani ƙanzo-ƙanzo ya yi kamar ya warke. Akwai wasu da ke zuwa da yanayin fitsari da zafi, ko ya riƙa fita da raɗaɗi."
Wasu ma yakan zo musu da toshewar hanyar mahaifa, wanda daga baya za a iya samun matsala wajen ɗaukar ciki."

Alaƙar magungunan ƙarin ni'ima da ciwon sanyi
Wani binciken likitoci ya gano yadda magungunan da mata suke cusawa a gabansu don ƙarin ni’ima ke saurin canza sinadarin PH wanda ake samu a al’aurar mace.
Dr Hafsat ta ja hankalin mata game da muhimmancin tsafta:
''A guji yin tsarki da sabulu maimakon haka a yi amfani da ruwan ɗumi kuma a yawaita canja kamfai da audugar mata musamman a lokacin al`ada, zama a jike yana haifar da ƙaiƙayi.''
Ta ce yana haifar wa mata matsaloli daban-daban da za su iya haddasa musu mummunan lahani a al'aurarsu.
Matakan da mata za su bi wajen tsaftace al'aurarsu
Dakta Hafsat ta ce tsaftace al'aura musamman ta mata tana da muhimmancin gaske saboda za ta kare lafiyarsu.
"Duk abin da kika san zai yi wa jikinki lahani ki guje shi, sannan kuma a nisanci amfani da magungunan ƙarin ni'ima wajen jima'i," in ji likitar matan.
Sau da yawa idan an zo tsarki, wasu sai sun wanke baya, wato dubura ko bayan gida, sannan su koma gaba, in ji Dr. Yamuna.
Hakan ba daidai ba ne. "A fara da gaba, sannan a koma baya."
Akwai kuma waɗanda suka samu ƙari a wajen haihuwa
Amma dai, likitar ta ce ba su cika samun irin wannan matsala da yawa ba, duk da haka tana ɗaya daga cikin hanyoyin haddasa cutukan sanyi, inda ake samun dubura a daf da matancin mace, don haka bayan gida yana haurawa ya shiga cikin gaban mace ya haddasa mata cutukan sanyi.
Ƙwararru a ɓangaren lafiya musamman ma likitoci da ke kula da tsaftar al'aura ta mata sun ce:
- Tsarki da ruwa kawai ba sabulu.
- Idan kina son tsane al'aurarki bayan kin yi tsarki to kada ki yi hakan da toli-fefa, (toilet paper), zai fi kyau ki tanadi ƙyalle mai tsafta ki goge, saboda zai iya sa wa mace ƙwayoyin cuta.
- Kada ki dinga cusa magungunan mata ko turare a al'aurar, idan ma almiski ne zai fi kyau ki shafa a ɗan kamfanki kawai.
- Yawan sa ɗan kamfai (pant) yana da muhimmanci, kada a dinga zama ba suturta al'aura.
- Ki yawaita tsarki da ruwan dumi dss.
Ana iya ganewa idan namiji yana da ciwon sanyi?
Likitar mata Dr Hafsa ta ce ba a cika samun alamomin ciwon sanyi a jikin namiji kamar yadda cutukan ke saurin nunawa a jikin mace ba.
''Akan samu jayayya ko rashin fahimta tsakanin ma’aurata a lokacin da aka gano ciwon sanyi, mace za ta ɗora wa mijinta alhaki yayin da shi kuma ba shi da wata alama da za ta nuna cewar yana da cutar," in ji likita.
Wasu lokutan maza sukan ɗauko cutukan sanyi irin su Gonorrhoea da Syphilis amma jikinsu bai nuna wata alama ba.
Ciwon kan bazu cikin sauri tsakanin mata, shi ya sa ake jan hankali da a riƙa kula sosai a duk lokacin da namiji ke rayuwa da mace fiye da ɗaya.
Ana son da zarar an samu wata daga cikin mata masu miji ɗaya ta nuna alamun kamuwa da ciwon sanyi, ya zama tilas duk sauran matan su je su ga likita.
Dr. Yamuna Ƙani ta ce akwai gwaje-gwaje da ake yi a gano nau'o'in ciwukan sanyi a al'aurar mace, kuma a ba da magani.
Ta ce akwai yalwar magunguna a yanzu, kuma ana warkewa.











