Yadda likitoci mata ke fuskantar barazanar lalata a lokacin tiyata

Asalin hoton, Getty Images
Likitocin fiɗa mata na yawan ƙorafin cewa ana muzguna musu domin yin lalata da su, har ma wani sa'ilin abokan aikinsu maza kan yi musu fyaɗe.
Wannan ya zama babban batu da wani jami'in hukumar lafiya a Ingila ya gano.
BBC ta tattauna da wasu matan da suka samu kansu a wannan yanayin da suka fuskanci cin zarafi a ɗakunan tiyata da ke asibitin.
Waɗanda suka gudanar da binciken sun ce akwai mata da yawa da ke neman ƙwarewa da su ma suka gamu da cin zarafi daga manyan takwarorinsu maza, kuma abin da ke ci gaba da aukuwa ke nan a halin yanzu, musamman a wannan asibitin.
Likitocin fiɗa na asibitin Royal College sun bayyana binciken da cewa yana da matuƙar "tayar da hankali".
Cin zarafi ta hanyar lalata da fyaɗe wani baƙon lamari ne da za kira da abin ɓoye da ya fito sarari a wannan ɓangare.
Akwai labaran da ba a faye jin su ba game da mata likitoci da ke cikin irin wannan damuwa da inda ake samun likitocin maza na rungumar matan tare da shafa sassan jikinsu.
Har ma akwai waɗanda ake yi wa tayin ƙarin matsayi idan suka amince aka yi lalata da su.
Sashen Ingilishi na BBC news ya samu wannan rahoton bincike da aka bankaɗo da Jami'ar Exeter da Jami'ar Surrey da kuma wata ƙungiya mai yaƙi da cin zarafin ma'akatan fiɗa ta hanyar lalata suka gudanar.
Kusan kashi biyu cikin uku na likitocin fiɗa mata da suka tattauna da masu gudanar da binciken sun ce ana harararsu da manufar a yi lalata da su yayin da sauran suka ce cikin shekaru biyar da suka wuce takwarorinsu maza sun ma taɓa yin lalatar da su.
Matan na cewa suna fargabar fallasa abubuwan da suka faru da su gudun kada hakan ya shafi kimar aikinsu kuma ba su da yaƙinin cewa asibitin na zai ɗauki mataki kan lamarin.
'Me ya sa yake ƙulle da ni duk na gan shi?'
Babu kwanciyar hankalin a yi wannan magana a gaban jama'a. Judith ta nemi mu sakaya sunanta. A yanzu ita ƙwararriyar likitar fiɗa ce.

Asalin hoton, CREDIT: JONATHAN SUMBERG
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta sha samun kanta a cikin tsaka-mai-wuya tun lokacin da ta fara aiki, kuma a lokacin ita ƙaramar likita ce a ɗakin tiyatar.
Ta ce "Haka kawai likitan da ke gaba da ni a wancan lokaci, ya faɗo jikina ya soma goga fuskarsa saman ƙirjina. Daga baya na lura yana share zufar da ke fuskarsa a jikina.
"Kawai za ka sandare saboda tsoro, 'me ya sa fuskarsa ke zamar min barazana?'"
Lokacin da ya sake irin haka a karo na biyu sai Judith ta ba shi tawul. Sai kawai ya ba ta amsa, "A'a ke kuma ai an fi morewa a wannan". A cewarta, "na tsani wannan, gaba ɗaya na ji an ci zarafina.
Me ma ake nufi da cin zarafi ta hanyar lalata a wurin aiki sannan mene ne ma hakkin mutum?"
Ma'aikatar lafiya ta Birtaniya, NHS na buƙatar MeToo ya kula, in ji wani tsohon likitan fiɗa.
Abin da ma ya fi damun ta shi ne rashin damar yin magana da abokan aikinta.
"Shi ba ma wani babba ne ba a wurin aikin, ya dai san wannan ɗabi'a ba ta dace ba.
Hakan ya auku gare ta a cikin ɗakin fiɗa amma duk da haka batun da ya shafi lalata da kuma cin zarafi lamurra ne da ba a wannan asibitin kawai ake samun sa ba.
'Na yarda da shi'
Anne - ba za mu iya bayyana sunanta na asali ba saboda dalilai na shari'a - tana son magana da BBC ne saboda ta yi imanin canji na samuwa ne kawai idan mutum ya bayyana damuwarsa.
Ba ta zaɓi ta bayyana abin da ya faru gare ta a matsayin fyaɗe ba, sai dai a zahiri take cewa lalatar da aka yi da ita ba a son ranta ba ne.
Hakan ya wakana a wani wajen taruwa mai alaƙa da wurin tarukan likitoci masu horo iri ɗaya.
"Na yarda da shi ina ba shi girma," in ji ta.
Ya yi amfani da wannan damar ta yarda ba ta san wasu mutanen da ke wajen kuma su ba ta amince da su ba.
"Sai ya ja ni a bayan wurin da nake zaune, na yi tsammanin wata magana zai gaya min amma kawai sai ya afka min inda ya yi lalata da ni"
Ta ce "lokacin da yake hakan jikina ya mutu na kasa dakatar da shi.
Al'amarin kan zauna a zuciyar mutun tsawon lokaci, da farko ta shiga damuwa sannan bayan 'yan shekaru 'sai abin ya dawo min a rai kamar wani abin tsoro ko mummunan mafarki" a wurin aiki ko da kuwa tana shirin yi wa maras lafiya aiki.
"Ba haka na so ba ban kuma taɓa tunanin faruwar haka ba, abu ne da ya zo babu tsammani"
Ta ce lokacin da ta haɗu da shi a rana ta biyu "gaba ɗaya sai na sha jinin jikina na tsorata".
"Na ji ba zan iya tayar da kowace hayaniya ba, na ji kamar akwai wata al'ada da ta shafi abin da aka yi maka"?
Rashin natsuwa ga likitocin fiɗa
Sanannen abu ne akwai wata al'ada ta yin shiru kuma samun horo a ɓangaren likitancin fiɗa na buƙatar dogara ga manyan likitoci a ɗakunan tiyata sannan matan sun faɗa mana akwai haɗari sosai idan mutum ya kuskura ya yi magana a kan waɗanda ke da iko game da makomar aikinsu a rayuwa.
Rahoton da aka wallafa shi a Mujallar Aikin Fiɗa ta Birtaniya, yunƙurin farko na ƙoƙarin gano zaren lamarin.
An gayyaci likitocin da suka yi rajista - mata da maza - su shiga binciken ba tare da bayyana sunayensu ba, inda 1,434 ne suka bayar da amsa. Rabinsu mata ne:
Kashi 63 cikin ɗari na matan na magana a kan cin zarafin lalata da suka fuskanta daga abokan aiki.
Kashi 30 cikin ɗari kuwa na matan abokan abokinsu maza sun yi lalata da su ba tare da son ransu ba.
Sai kashi 11 cikin ɗari kuma na matan sun yi ƙorafin an yi musu fyaɗe.
Kazalika, kashi 90 cikin ɗari na mata da kashi 81 cikin ɗari na maza sun haɗu da hare-haren cin zarafi ta hanyar lalata da su
Yayin da rahoton ya nuna maza ma na fuskantar makamancin haka (kashi 24 cikin ɗari sun taɓa fuskantar cin zarafin lalata), daga ƙarshe dai akwai bambanci tsakanin likitoci maza da mata.
"Bincikenmu zai girgiza waɗanda ke aiki a fannin likitancin fiɗa", in ji Christopher Begeny na Jami'ar Exter.
Yayin da na rahoto na biyu kuma - da aka yi wa laƙabi da Fallasa Abin Ɓoye: Kawo Ƙarshen Matsalar Cin Zarafin Ma'akatan Lafiya - kamar matakin shawara ne domin sauya abin da ke buƙatar sauyi.
Rahotannin biyu sun yi hasashen kasshi 28 cikin ɗari na likitoci mata ya ƙarfafa gwiwar maza abin da ke dagula lamarin ya kuma sa yanayin aiki a waɗannan wurare ke da matsala.
"Wannan ya kai ga mutane na yin abun da ke ƙara zube ba tare da an gudanar da bincike ba." A cewar Farfesa Carrie Newlands, ƙwararriyar likitar fiɗa ta Jami'ar Surrey.
Abin da ya ja hankalinta take son kawo ƙarshen wannan ɗabi'a lokacin da ta ji bayanan likitocin da ke ƙasa da ita.
Ta shaida wa BBC cewa : "Abin da ke wakana shi ne ƙaramar likita na shan ukuba ƙarƙashin manyan likitoci maza, waɗanda su ne masu aikata wannan badala.
"Wannan kuma ya sa al'ada ta shiga suka kasa magana inda hakan na da nasaba ne da fargabar da mutane ke da ita ga makomar aikinsu.
'Damuwar da ta wuce misali'
Wani sabon batu ma da ya taso shi ne yadda hukumar lafiya ta Birtaniya da kuma Babbar Hukumar Lafiya (mai alhakin yi wa likitocin Birtaniya rajista) da Royal College (wadda ke wakiltar wani sashe na fannin lafiyar ƙasar) - ke ɗari-ɗari da kuma sakaci wurin magance matsalar.
"Muna buƙatar gagarumin sauyi da yadda za a fito da komai a sarari, kuma binciken ya zama mai zaman kansa, kuma wanda za iya yarda da shi har ta kai an tsarkake fannin kiwon lafiyar, ya zama wurin da ke da tsaro a aiki" in ji Farfesa Newlands.
Tim Mitchell, shi ne shugaban Sashen Koyon Fiɗa na Royal College da ke Ingila, ya shaida wa BBC cewa binciken "ya bankaɗo abubuwan firgitarwa kuma tushen abubuwan kunya da aka aikata a fannin kiwon lafiyar ƙasar".
Ya amince cewa, "a zahiri take matsala ce gama-gari" da aka kasa yi wa tufka hanci.
Dakta Binta Sultan ta wani asibitin gwamnati da ke Ingila ta ce, "dole muna buƙatar kawo sauyin da za mu ba mutanen da aka zalunta damar matsowa gaba-gaba domin su faɗi damuwarsu da kuma za a ɗauka da muhimmanci".
Ta ce: "Mun riga mun yi nisa a wannan, ciki kuwa har da samar da taimako da hanyoyin samar da rahoto domin amfanin waɗanda aka ci zarafinsu".
A watan da ya gabata Babbar Hukumar Kiwon Lafiya ta sabunta tsare-tsarenta da za su yi daidai da likitoci.
Shugabanta, Charlie Massey ya bayyana cewa, "aikata cin zarafin yin lalata da marasa lafiya ko abokan aiki likitoci abu ne da ba za a lamunta da shi ba" kuma "aikata babban laifi ne da ba za a jitu da shi ba" in dai za a ci gaba da aikin kiwon lafiya a Birtaniya.
Shin ko aikin likitancin fiɗa ya dace da mata a wannan zamani?
"Ba a ko yaushe ba. Sannan lamari ne mai matuƙar ban tsoro da kuma dole a amince da shi." in ji Judith.










