Fyade a Kano: Mutumin da 'ya yi wa mata 40 fyade' ya amsa laifinsa a gaban kotu

- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Kano
Mutumin nan da rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kama a watan da ya gabata kan zargin yi wa fiye da mata 40 fyade ya amsa laifinsa a gaban kotu a ranar Laraba.
Mohammed Zulfara'u wanda ake zarginsa da yi wa matan fyade cikin shekara daya a Kwanar Dangora ya shaida wa kotu cewa shi ''ya yi wa matan fyade kuma yana da na sanin hakan.
An fara sauraron karar ne da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba a wata Kotun Majistare da ke birnin Kanon.
Mai shari'a ya ba da umarni a ci gaba da tsare mutumin da aka fi sani da 'Mai Siket'.
An karantowa wanda ake tuhumar abinda ake zarginsa da shi kamar haka, ''Kai Mohammed Zulfarau mai shekara 32 ana zargin ka da yi wa wata mata 'mai shekara 75 fyade da kuma kokarin yi wa wasu matan biyu fyade a Kwanar Dangora, me za ka ce kan hakan?''
Sai mai shari'ar ya sake tambayar Mai Siketa ko ya fahimci abin da muhutin kotun ya karanto masa.
Sai ya ce: ''Eh na gane kuma na yarda na aikata duk abin da aka karanto amma ina neman afuwa.''
Mijin daya daga matan da ake zargin ya yi wa fyaden ya shaida wa BBC bayan zaman kotun cewa, ba zai kyale zancen ba har sai ya tabbatar an yi adalci don ya yi wa mata da dama hakan.
Shi ma Mai Siket ya shaida wa 'yan jarida cewa yana neman matan su masa afuwa, kuma ba zai sake ba idan aka sake shi.
''Ina rokon dukkan matan nan da su yafe min kuma ba zan sake ba idan aka sake ni.''
Za a ci gaba da sauraron karar ranar 20 ga watan Yulin 2020 a kotun.











