Likitoci dubu 54 ne kacal suka rage a Najeriya - Ƙungiyar Likitoci
Latsa hoto domin kallon bidiyo
Ƙungiyar Likitocin Najeriya, NMA ta ce a yanzu haka likitoci dubu 54 ne kacal suka rage domin kula da lafiyar ƴan ƙasar fiye da miliyan 218.
Ƙungiyar ta NMA ta ƙara da cewa daga cikin likitocin dubu 54, dubu 18 ne kawai ƙwararru da ke cikin aikin duk da cewa wasu daga cikin dubu 18 ɗin tuni su ma sun bar kasar.
A shekarar da ta gabata ne dai fiye da likitocin 2000 suka bar Najeriya zuwa kasashen Turai.
Akwai fargabar cewa fiye da likitocin 4000 ka iya barin kasar a sabuwar shekarar nan ta 2023.
Da alama kuma yankin arewa ya fi fama da karancin likitoci bisa alkaluman da kungiyar likitocin ta Najeriya ta fitar.

Alkaluman dai na nuna cewa yanzu haka akwai likitoci 425 kacal da ke aiki a kafatanin yankin arewa maso yammaci da ke kunshe da mutane kimanin miliyan 50, kusan kaso daya bisa hudu na yawan jama’ar Najeriya.
A watan Yuli, alkaluman kungiyar likitocin ta Najeriya sun sake nuna cewa kimanin likitoci 200 'yan asalin kasar sun samu lasisin zama likitoci a Burtaniya.
Wani rahoto a Mujallar British Medical Journal a 2020 ya nuna cewa da ma akwai karancin likitoci miliyan 2.8 a fadin duniya kuma matsalar ta fi shafar kasashe masu tasowa irin su Najeriya.
Yanzu tambayar da jama’a da dama ke yi ita ce shin adalci ne ace manyan kasashen duniya su rinka kwashe likitocin ƙananan kasashen da dama tsarin lafiyarsu ke cikin wani hali?



