Me Sarkin Ingila zai iya yi kan zargin lalata da ake yi wa ƙaninsa?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Sean Coughlan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Royal correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
Kimar Yarima Andrew wato kanin Sarkin Ingila ta sake gamuwa da wata matsalar inda jaridu ke ta bayyana wata wasikar imel da ke nuna cewa yana da alaka ta kut da kut da attajirin nan da aka kama da laifin lalata a Amurka Jeffrey Epstein, wanda ya kashe kansa a kurkuku.
Bayanan cikin wasikar sun nuna cewa Yarima ya ci gaba da alaka da Epstein fiye da tsaewon lokacin da ya ce ya katse hulda da shi.
Wasikar ta saba da bayanan da Yariman ya yi wa BBC a wata hira da kafar ta yi da shi, inda ya ce ya katse alaka da Epstein bayan da ya hadu da shi a New York a watan Disamba na 2010, inda aka dauki mutanen biyu a hoto.

Asalin hoton, EPA
Batun badakala ba wani sabon abu ba ne ga Yarima Andrew, wato kanin Sarkin na Ingila.
Wasikar wadda jaridar Sun da Mail suka ruwaito ranar Lahadi an ce an rubuta ta ne daga watan Fabarairu na 2011, kuma a farkon wannan shekara ta 2025 an samu wasu wasikun da su ma aka rubuta su kusan a wannan lokacin, wanda hakan ke nuna cewa Yarima Andrew ya ci gaba da alaka da Epstein watanni da dama fiye da yadda ya yi ikirari.
Wannan ne ya janyo jaridu ke bayar da labarin wanda ke kara shafar kimar Yariman.
To amma me hakan zai iya haifarwa? Kowace badakala da ta bayyana a kan Yariman na sa a rika kira ga Masarautar ta dauki mataki a kansa.
To dangane da hakan wane mataki Sarkin na Ingila da Iyalan Masarautar za su iya dauka? Ta yaya za su iya nesanta kansu?
Wani babban taro da iyalan za su hadu a nan gaba shi ne na Kirsimeti a Sandringham.
Kuma bisa ga dukkan alamu da wuya a gayyaci Yarima Andrew da tsohuwar matarsa Sarah Ferguson.
Sannan da wuya a ga hotonsa na bidiyo a sakon gaiisuwar Kirsimeti da Sarkin Ingila zai yi.
Ko a bara ma ba a sanya Yariman a cikin sakon Masarautar na Kirsimeti ba saboda zargin alakarsa da wani mai leken asiri na China, kuma wannan mataki na ware shi bisa ga dukkan alamu zai ci gaba a wannan shekarar (2025) ma.
Ita ma tsohuwar matar Yariman Sarah Ferguson, tana da irin tata badakalar ta alaka da Epsteim - inda a dalilin haka bakwai daga cikin kungiyoyinta na taimako suka yanke hulda da ita.
Akwai kiran da ake ta yi na fitar da Yariman daga Masaukin Masarautar - inda yake zaune a masaukin na kasaita na dakuna 30 a Windsor.
To amma kuma Yariman yana da kwantiragin zama a wannan masauki har zuwa shekara ta 2078, domin ya biya yawancin kudin tun a 2003, saboda haka abu ne mawuyaci a iya fitar da shi daga masaukin a yanzu.
Idan har Andrew zai iya biyan kudin zamansa a masaukin na Sarauta to abu ne mawuyaci a iya fitar da shi dagfa masaukin.
Wasu kafofi na Masarautar sun ce Sarkin na jarraba hanyoyi da dama na daukar mataki a kan kanin nasa, kamar daina biya wa Yariman kudaden wasu harkokinsa a shekarar da ta wuce.
To amma kuma bisa ga dukkan alamu Yariman ya tanadi hanyoyin samun kudinsa, daga harkokin kasuwanci a China da kasashen Larabawa da sauransu.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai kiraye-kiraye da ake ta yi na neman a tube mukaman sarautar da aka ba Yariman, inda kuma wannan kira ya samu goyon bayan jama'a da dama - inda kashi 67 cikin dari na wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi a kan hakan ta nuna jama'a na goyon baya a cire masa mukaman da suka rage.
Wannan dai na bukatar sahalewar Majalisar Dokokin Birtaniya, amma duk da haka akwai mataki na doka da za a iya yin hakan, kamar yadda aka yi a lokacin Yakin Duniya na Daya, inda aka cire mukaman sarautar da aka bai wa 'yan sarautar da suke da mukamai na girmamawa na Birtaniya amma kuma suna yaki a rundunar sojin Jamus.
Saboda haka za a iya cewa wannan abu da ba za a iya kawar da yuwuwarsa ba - a ce an tube masa wasu daga cikin mukaman na sarauta idan badakar ta ci gaba da bayyana haka.
Wasu daga cikin fitattun da irin wannan mataki ya shafa na tube musu matsayi ko lambar girmamawa ta Birtaniya saboda kasancewarsu masu adawa da Birtaniya a Yakin Duniya na biyu sun hada da Wilhelm II na Jamus da Franz Joseph na Austria da Hungary.
Akwai kuma Benito Mussolini da Robert Mugabe da kuma Nicolae Ceausescu, wadanda duka an kwace lambar girmamawar da aka ba su ta Birtaniya.

Asalin hoton, PA Media
Tuni dai daman Yarima Andrew ya rasa mukaminsa na Mai Martaba (HRH ) da kuma mukamansa na girmamawa na soji na kasancewar dan gidan Sarautar Birtaniya.
Kuma tun da a yanzu ba ya wani aiki a matsayin Dan Sarauta - babu wani aiki na Masarautar da ke kansa.
Haka kuma wannan na nufin Fadar Birtaniyar ta daina daukar alhakin duk wani abu da ake zarginsa da aikatawa.
Akwai ma shawarar da ake bayarwa ta cewa Iyalan Masarautar, su kara daukar mataki a kansa na abin da aka kira kawar da shi daga bainar jama'a.
Tuni dai a yanzu an hana shi halartar duk wani taron jama'a da ya shafi Masarautar.
Maimakon haka bayyanarsa a taro ta takaita ne a kan taruka na daban haka wadanda ba na jama'a ba, da taro na iyali kamar jana'iza ko zaman makoki ko taron tunawa da wani mamaci.
Kusan wannan shi ne abin da zai ci gaba da amfana. Ba don komai ba, kasancewar yayansa a matsayin shugaban Cocin Ingila, abu ne mawuyaci a ce a ya hana kaninsa halartar addu'o'i a coci.
To amma kuma dole ne Masarautar ta damu da irin wadannan abubuwa na badakala da suka shafi kanin Sarki da suke ta kara bayyana.
Abin da zai iya yin barazana ga kimar ita kanta Masarautar.
Kuma yanzu ba a san irin abin da zai kara bayyana ba daga bayanan da suka shafi alakar shi Yariman da Epstein.
Masu adawa da Masarautar na kira da a fadada bincike a kan abin da Masarautar ta sani a kan alakar Yarima Andrew din da Epstein.











