Yadda ake samun karuwar yin lalata da cin zarafin mata a gidajen nishadantarwa a Saudiyya

Mahalarta taron MDL Beast a Riyadh (18/12/21)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sama da 'yan kallo 700,000 ne suka halarci bikin kalankuwar mawaka na MDLBeast Soundstorm a wajen birnin Riyadh
    • Marubuci, Daga Sebastian Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arab affairs editor

Yayin da aka shiga kwanaki da fara bikin kalankuwar mawaka mafi girma a yankin Gabas Ta Tsakiya da ake yi a kasar Saudiyya, masu shirya bikin sun yi alkawarin daukar karin matakan kare cin zarafi ta hanyar lalata da dangoginsu a inda ake gudanar da bikin a wajen birnin Riyadh.

A yanzu taruwar jama'a domin gudanar da wani abin nishadi ba wani bakon lamari ba ne a kasar, sai dai ana samun rahotanni nan da can daga matan kasar da na kasashen waje, kan yadda aka ci zarafinsu, wasu daga ciki ma an dauka a bidiyo.

Har yanzu wasu 'yan Saudiyya na mamakin yadda kunnuwansu ke jiyo karar kade-kade da raye-raye a kasar da a shekarun baya ba ka isa sanya kida ba.

Kwanaki hudu mawakan MDLBeast's Soundstorm za su kwashe suna cashewa kuma dubban 'yan kallo ne suka tiki rawa daga makadan da ke tashe a duniyar mawaka.

Mata da maza sun gwamutsa wuri guda, ana ta hada-hada fiye da tunanin dan adam.

'Yan kallo a wajen bikin kalankuwar mawaka a birnin Riyadh (19/12/21)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An bar mata da maza sun gwamutsa wuri guda a lokacion, wanda a baya haramun ne aikata hakan

Fitattun mawaka daga sassa daban-daban na duniya ne suka yi nazari kan zargin take hakkin dan adam da ake yi a Saudiyya kafin yanke hukuncin halartar bikin, yayin da masu fafutuka ke cewa wadanda suka halarta suak ce sun yi ne domin wanke bakin fentin da gwamnatin kasar ta yi a idon duniya kan take hakkin dan adam.

Sai dai ba su kadai ne suka sake yin tunani kafin yanke hukuncin zuwan ba, an samu rahotannin cin zarafin mata a wurare daban-daban musamnman kusa da wuraren da ake gudanar da bikin a Riyadh da wasu wuraren. Bidiyo da dama sun yi ta yawo a shafukan sada zumunta a shekarun da suka gabata yadda maza ke cin zarafin mata.

MDLBeast sun kaddamar da gangamin mai taken Amutunta a kuma dauki matakin domin bai wa mata kariya a irin wadannan wuraren, tare da daukar matakin ba-sani-ba-sabo ga wadanda aka samu da laifin cin zarafin mata.

Bikin kalankuwar MDL Beast a Riyadh (18/12/21)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, MDLBeast sun ce bikin kalankuwar Sandstorm shi ne irin sa mafi girma a yankin

Sai dai yawancin matan Saudiyya sun tuntubi BBC domin shaida mana ba su yadda da matakin da hukumomin suka ce suna dauka ba. Babu wata daga cikin matan da ta amince mu ambaci sunanta.

Sun ce ko dai sun fuskanci cin zarafin ko kuma wata da suka sani an ci zarafinta a irin wannan wuraren na bukukuwan nishadantarwa.

Wata daga cikinsu ta ce an yi ta dora laifin yawancin hotuna da bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta a kan matan, sannan akwai yiwuwar a a hukunta su karkashin dokokin Saudiyya.

Wata ta daban kuma, ta ce hukumomin su na daukar mataki ne idan lamarin ya hada da 'yar kasar waje. Ka kara da cewa ana yi wa batun rikon sakainar kashi idan lamarin ya hada da matan Saudiyya, sai dai an yi ana daukar matakin mummunan hukunci da tara mai tsanani idan macen

Mace ta ukun ta ce ba a bai wa mata wata kariya ta zahiri, lamarin da ya sa su ke jin da ma ba su je ba, da ba su je din ba hakan ba za ta faru da ta ba. Idan mace ta kai rahoton an ci zarafin ta, tana fuskantar tsangwama ko ma allawadai daga 'yan uwa da sauran al'umma.

'Sauyi a zahiri'

Makusantan yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman da a fakaice shi ke jagorantar kasar, da kuma abokansa sun ce wadannan lamaura na faruwa ne sakamakon yadda kasar ke kokarin sauya wasu dabi'u da al'adun da akai shekaru aru-aru ana bin tsarinsu, musamman wadanda masu tsaurin addi nin Islama suka shimfida.

Tsarin sauye-sauyen da kasar ke dauka na tafiya da sauri domin fatan ganin an cimma muradun Vision 2030 na sauya Saudiyyar ba ki dayanta, ta hanyar dauke hankali da dogaro ga man fetur, tare da bai wa matasa dama a dama da su a fagen rayuwa daban-daban.

Wata mace na tuka mota a birnin Riyadh (24/06/18)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matan Saudiyya sun samu 'yancin tuka mota karkashin jagorancin yarima Muhammad bin Salma

Magoya bayan yariman sun ce duk wadannan abubuwan na faruwa ne a matakin farko, sun yi kiran a kara yin hakuri domin ana shirin daukar matakan da suka fi wadanda ake gani a yanzu.

Amma matan Saudiyya da suka tuntubi BBC, sun dasa ayar tambaya kan sahihancin haka, tare da nanata cewa matan sun dade suna fatan ganin ana tattauna matsalolinsu da magance su, amma babu abin da aka yi.

Sun ce batutuwan cin zarafi na daga cikin abin da ya tsaya a zukatan matan Saudiyya, kama daga halartar manyan tarukan da maza da mata za su cudanya da sauransu, wanda ana yi ne da nufin a bude kofar kasar da sauran kasashe ba wai ta fannin yawon shakatawa ko bude ido kadai ba, har ma da karawa 'yan kasa walwala da jin dadi.