Sunan Yarima Andrew da na Bill Clinton sun fito a cikin abokan mai 'lalata yara'

Wata kotu a birnin New York ta fitar da ɗaruruwan takardu da ke ɗauke da sunayen mutane masu alaka da mutumin nan Jeffrey Epstein wanda kotu ta kama da laifin lalata da ƙananan yara.
Sun haɗa da abokan aiki da na masu hulda da biloniyan dan kasuwar, wanda ya kashe kansa a kurkuku shekara biyar a baya.
Ya kasance babban abokin masu kuɗi da dama a duniya, ciki har da hamshaƙan 'yan siyasa da 'yan kasuwa da 'ya'yan gidan sarauta, kamar Yarima Andrew, ɗan'uwan Sarki Charles.
Takardun sun hada da koken Johanna Sjoberg, wadda ta yi zargin cewa Yariman ya taɓa mata nono, a lokacin da take zaune a kan wata kujera, a gidan Eipstein na Manhattan a 2001.
A baya dai, fadar Buckingham ta ce zarge-zargen nata 'ba gaskiya' ba ne.
Ko a shekarar 2022, sai da dan sarautar ya biya miliyoyin kudi ga Ms Giuffre domin sasantawa kan wata ƙara da ta shigar ta zargin cin zarafinta, a lokacin da take 'yar shekara 17.
Baya ga Yariman, sunayen tsoffin shugabannin Amurka, Bill Clinton da Donald Trump su ma sun fito a takardun, duk da cewa babu wanda aka zarga da karya doka.
Wakilan Mista Clinton sun sake yin waiwaye kan wata sanarwa da ya fitar a 2019, da ke cewa "ba shi da masaniya' game da miyagun ayyukan Epstein.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Har wa yau, takardun sun yi bayani kan yadda Misis Sjoberg tana cewa Epstein ya fada mata cewa zai tuntuɓi Donald Trump, a lokacin da suke kan hanyar zuwa gidan cacarsa na New Jersey.
Sai dai kuma babu inda Misis Sjoberg ta alakanta wani laifi ga tsohon shugaban Amurkan, Donald Trump.
An tambaye ta cewa ko ta gan shi a wani lokaci yana aikata wani abin assha? Sai ta ce "A a".
Misis Sjorberg dai ta ƙara da bayar da shaidar cewa Eipstein ya hada ta da fitaccen mawakin nan, Michael Jackson da kuma mai gani har hanjin nan, David Copperfield.
Sai dai kuma, su ma ba ta san ko sun aikata wani aikin assha ba.
Takardun na shari’a sun hada da wadanda suka yi bayani kan zargin taɓa mata ‘da niyyar iskanci’ waɗanda aka yi wa Yarima Andrew, abin da ya musanta.
Wannan kundin mai shafi kimanin 900, ba wani sabon abu ya bayyana dangane da Epstein ba, wanda ya mutu a gidan yari a 2019, yayin zaman jiran tuhumar cin zarafin ƙananan 'yan mata.
To sai dai ana sa ran fitowar ƙarin takardun da za su yi ƙarin haske a kan badaƙalar cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
A kimanin mutum 100 da sunayensu suka bayyana, ana zargin wasunsu da aikata ba daidai ba, inda da dama kuma ke yin wasu zarge-zarge a kundin shari’ar da ke gaban kotu, sannan wasu kuma sun shaida lokutan da aka aikata laifukan.











