Zargin cin zarafin lalata ya tayar da hankali a kwalejin rawa ta India

G

Asalin hoton, Getty Images

Daya daga cikin manyan cibiyoyin da ake ɗabbaƙa al’ada a India, Kalakshetra, ta samu kanta cikin tsaka-mai-wuya, game da zargin cin zarafin lalata kan wasu mambobi uku da ke koyar da rawa da ke zuwa a matsayin malaman da ke aiki lokacin da aka buƙata a kwalejin koyar da rawar.

Wannan rikici ya shafi kwalejin da Kalakshetra ke kula da ita, kwalejin Rukmini Devi, kwalejin da ta yi suna wajen koyar da rawar Bharatanatyam.

A makon jiya ‘yan sanda suka kama wani Farfesa kuma kwararren mai rawa Hari Padman bayan wani tsohon ɗalibi ya shigar da ƙorafin cin zarafinsa da ya yi ta hanyar lalata.

Hakan ya faru ne bayan kwanaki da wasu ɗalibai sama da 200 suka kwashe suna zanga-zanga a cibiyar – wadda take a birnin Channai na jihar Tamil Nadu da ke kudancin India.

Sun yi zargin suna fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata shekaru da dama kuma sun zargi hukumomin makarantar da yin ko in kula da ƙorafe-ƙorafen da suke shigar wa.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta Gidauniyar Kalakshetra ya dda ke cin gashin kanta ƙarƙashin ma’aikatar al’adu ta India ta yi zargin “akwai muradin mutane da dama cikin zanga-zangar” kuma suna neman bata sunan gidauniyar ne.

Amma bayan wannan rikici ya ta fita a kanun labarai, Gidauniyar ta kafa wani kwamiti na mutum uku waɗanda dukansu tsafaffin alƙalai ne da su yi bincike kan lamarin.

Ta kuma dakatar da Hari Padman, ta kuma ce an dakatar da aikinsu “har sai lokacin da aka gama bincike”.

“Yayin da ake ci gaba da binciken, ba daidai ba ne a yi bayani kan wannan saƙon email din da kuka aiko,” suka gayawa BBC.

Kwamishinar mata ta Tamil Nadu ta bayar da umarnin a fara gudanar da bincike kan zarge-zargen.

G

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gabanin kamun da aka yi masa, Hari Padman ya musanta zarge-zargen da aka yi masa a wani taron masu ruwa da tsaki na hukumomin. Ya kuma shaida wa wani gidan talabijin cewa yace zai yi duk abin da zi yi don nemawa kai wa kansa adalci.

“Akwai daruruwan ɗalibai da ke karatu a Kalakshetra. A tambaye su idan na taɓa neman tozarta wani ko yi wa wani maganar banza cikinsu. Ban taɓa zagin kowa ba. Na tabbatar da abin da nake fada kuma babu mai wata hujja a kaina,” ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta News18, yana cewa ya dogara kan kyamarar CCTV ta zamar masa hujja.

Matarsa ta kare shi, ta kuma shigar da ƙara kan waɗanda suka yi ƙorafi a kansa da kuma wasu malaman Kalakshetra biyu, tana zarginsu da ɓata masa suna saboda mijinta “suna kishi da shi da kuma hassada irin ta abokan aiki”.

Divya Hari ta ce tuhumar da ake yi wa mijin nata wani “mataki ne na ramuwa” saboda ya ja wa ɗalibai da ba su da kunya kunne, kuma waɗannan malaman biyu su ne suka “zuga” tsihin shugaban ɗalibai ya shigar da ƙara a kansa.

“Kalakshetra na taimakawa dalibanta wajen yin suna da kuma samun kuɗi kazalika tana ba su damar samun yin suna a faɗin duniya.

Da yawan ɗalibai sun shaida wa BBC rawa itace babban burin da suke da shi tun suna yarinta, shi yasa ma suka shiga wannan kwaleji, kuma lokacin da suka samu gurbin karatu a wajen sun ji su kamar sun fi kowa a duniya.

Amma yanzu matsalar cin zarafi da suke fuskanta daga wasu malamai ya sa suk kansu suna tsoron ko mafarkinsu zai cika.

BBC ta tattauna da gwamman ɗaliba da malamai da kuma tsofaffin ɗalibai da sauran jami’ai kuma ta ji iƙirari mai yawa kan yadda ƙananan masu koyon rawa ke shan wuya.

Dukkansu sun nemi a boye sunayensu saboda waɗanda ke cin razafin fitattu ne kuma waɗanda suka iya rawa.

G

Asalin hoton, Getty Images