Yarima Andrew ya sasanta da matar da ta kai shi ƙara kan lalata

Yarima Andrew da Virginia Roberts da Ghislaine Maxwell a 2001

Asalin hoton, Virginia Roberts

Bayanan hoto, Yarima Andrew da Virginia Roberts da Ghislaine Maxwell a 2001

Dan Sarauniyar Ingila na uku, kuma mutum na tara a jerin masu jiran sarautar, Yarima Andrew ya sasanta da wadda ta kai shi kara a Amurka, Virginia Giuffre, a kan zargin cin zarafinta ta hanyar lalata, kamar yadda takardun kotun suka nuna.

Ms Giuffre ta dade tana karar Yariman (Duke of York), tana zarginsa da cewa ya ci zarafinta sau uku a lokacin da take shekara 17, zargin da ya sha musantawa.

Wata wasika da aka shigar a wata kotun Amurka ranar talata ta bayyana cewa Yariman da Ms Giuffre sun cimma sasanto a tsakaninsu (wajen kotu).

Wakilan Yariman sun ce ba su da wata magana da za su yi bayan sanarwar kotun.

Sanarwar da ke kunshe a wasikar wadda aka aika wa alkalin kotun a Amurka, Lewis A Kaplan, ta ce Yariman zai bayar da tallafi mai yawan gaske ga asusun tallafi na Ms Giuffre, na kare 'yancin wadanda aka ci wa zarafi ta hanyar lalata.

Sanarwar ta kara da cewa Yarima Andrew bai taba tunanin ya bata sunan Ms Giuffre ba, kuma ya yarda cewa ta sha wahala a matsayinta na wadda aka ci wa zarafi da kuma yadda jama'a suka rika sukarta ba tare da hakkinta ba.

Yariman ya kuma yi alkawarin nuna nadamarsa kan alaka da Jeffrey Epstein, wanda aka daur bisa laifukan lalata, ta hanyar bayar da goyon baya da tallafa wa yaki da kawalci da kuma taimaka wa wadanda aka ci wa zarafi ta hanyar.

Haka kuma ya yaba wa jarunta da karfin halin matar da wasu ire-irenta da aka yi kawalcinsu, kan yadda ta jajirce a kan kanta da sauran wasu.

Da aka tambayi lauyan matar, David Boies kan abin da zai ce game da wannan batu na sasantawa a bayan kotu sai ya ce : ''Ina ganin komai a bayyane yake a nan.''

Ms Giuffre, wadda a yanzu take shekara 38, ta yi zargin cewa Epstein ya yi kawalcinta tare kuma da cin zarafinta ta hanyar lalata tana shekara 16. Epstein ya mutu a gidan yari a 2019, yayin da yake jiran a yi masa shari'a a kan laifukan kawalci, inda yake kai 'yan mata kasashe da wurare daban-daban ana lalata da su.

ta ce daga irin cin zarafin da aka yi mata shi ne yadda aka rika bayar da hayarta ga manyan mutane, ciki har da Yarima Andrew.

Ms Giuffre ta yi zargin cewa Yariman mai shekara 61 a yanzu, ya ci zarafinta ta hanyar lalata sau uku.

Na farko a gidan Ghislaine Maxwell da ke London, sai wanda ya yi mata a katafaren gidan Epstein a New York da kuma karo na uku a wani gidan na Epstein da ke tsibirin Amurka na Virgin Islands.

Fadar Sarauniyar Ingila ta raba Yariman da wasu mukaman da yake rike da su.