Jarumin Bollywood Saif Ali Khan ya tsallake rijiya da baya bayan daɓa masa wuƙa

Asalin hoton, Getty Images
An yi wa fitaccen jarumin fina-finan Bollywood ɗin nan, Saif Ali Khan tiyata kuma yana samun sauƙi bayan daɓa masa wuƙa a lakarsa da wani mutum ya yi bayan ya kutsa cikin gidan jarumin, kamar yadda masu taimaka masa suka ce.
Harin dai ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar da jarumin da iyalansa ke zaune a wajen birnin Mumbai.
Ƴansanda sun shaida wa BBC cewa an dai kai wa jarumin harin ne sakamakon wata hatsaniya da ta ɓarke tsakaninsa da wani mutum da ba a san kowane ne ba wanda ya kutsa har cikin gidan jarumin da tsakiyar dare.
Zuwa yanzu ba a samu cikkaken bayani kan harin ba.
'' Daga nan sai gardama ta ɓarke tsakanin Khan da maharin, '' kamar yadda mataimakin kwamishinan ƴan sandan Mumbai Dixit Gedam ya shaida wa BBC.
An garzaya da Khan asibitin Lilavati da ke birnin Mumbai da safiyar Alhamis.
Niraj Uttamani, wani babban jami'i a asibitin ya shaida wa BBC cewa an daɓawa khan wuƙa sau shida, amma biyu ciki sun fi muni.
Masu taimakawa Khan sun ce lamarin 'ƙokarin yin sata ne'' sai dai ba su bayyana wasu ƙarin bayanai ba.
'' Mu na buƙatar ƴan jarida da magoya bayansa su yi haƙuri su kwantar da hankalinsu. Lamarin ya na hannun ƴan sanda,'' a cewar su.
Ƴansandan dai sun haɗa wata tawagar da za ta binciki al'amarin.
"An yi wa Khan tiyata kuma ya fito lafiya. Yanzu haka yana murmurewa kuma likitoci na sa ido kansa,'' a cewar masu taimakawa Khan cikin wata sanarwa.
Da yake magana da manema labarai bayan tiyatar, Dakta Nitin Dange na asibitin Lilavati inda aka kwantar da Khan, ya ce jarumin ya samu mummunan rauni a laƙarsa sakamakon daɓa masa wuƙa a lakar.
'' An gudanar da tiyata domin cire wuƙar da kuma gyara tsiyayewar lakar. Tawagar masu tiyata sun kuma yi aikin gyara munanan ciwuka biyu da ke hannunsa na hagu da ɗaya a wuyansa, '' inji shi.
Khan na auren jarumar Bolloywood Kareena Kapoor kuma ma'auratan na da ƴaƴa biyu.
Zuwa yanzu ba a ji ta bakin iyalinsa ba, sai dai masu taimakawa Khan sun tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya.
Wane ne Saif Ali Khan?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Khan, wanda ya fara fitowa a finan-finan Bollywood a shekarar 1993, yana aiki ne a masana'antar finafinan Indiya, kuma ya shahara ne saboda barkwancinsa.
Wasu daga cikin fitattaun finafinansa sun haɗa da finafinan soyayya da barkwanci kamar Dil Chata Hai da fim ɗin Kal Ho Naa Ho, sai kuma finafinan faɗa da yayi a baya-bayan nan kamar su Tanhaji da Devara: kashi na 1.
Rawar da ya taka a fim din Omkara da aka fitar a shekarar 2006, wanda aka kwaikwayi labarin fitaccen marubuci Shakespear mai suna ' Othello', ya samu karɓuwa sosai.
Khan ya fito ne daga gidan sarauta na Nawab, waɗanda su ka mulki Pataudi- wani ƙaranin yanki a wajen Delhi- kuma ya yi aure a cikin iyalin jaruman fina finai.
Mahaifinsa Mansoor Ali Khan Pataudi ɗan wasan kirket ne wanda ya riƙe matsayin kaftin na tawagar ƙasar a shekarun 1960.
Mahairfiyarsa Sharmila Tagore kuwa ƙwarariyyar jarumar finafinai ce wadda ta fito a finafinan yaren Hindi da Bengali tun tana shekara 14.
Ƴar uwarsa Soha Ali Khan ita ma ta fito a wasu finafinai na wasu ƴan shekaru.
Matarsa Kareena ta fito ne daga halin sannanun jarumai, da masu bayar da umurni, da masu shirya finafinai waɗanda suka daɗe a masana'antar Bollywood har na kusan shekara 100.











