Jarumin Bollywood ya faɗi dalilin barin masana'antar a sirrance

Bollywood actor Aamir Khan posing for a picture during a screening

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Noor Nanji & Sadia Khan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 7

Sanannen jarumi a masana'antar Bollywood na Indiya, Aamir khan ya yi fice ne saboda wasu daga cikin finafinan Indiya da ya yi da suka shahara kamar su Lagaan da 3 Idiots.

Ya shahara sosai da ba ya wucewa a kan titi ba tare da masoyansa sun yi tururuwa kan shi ba.

Abun da mutane da yawa ba su sani ba shi ne ya bar yin finafinai a lokacin annobar Covid, domin ya kara samun lokaci tare da iyalinsa.

"Na fada wa iyalina na gama yin finafinai" kamar yadda ya shaidawa BBC.

"Ba na so in shirya wani fim ko ba da umurni ko fitowa a ciki. Abunda Kawai nake so shi ne in kasance da iyalina.

Za ku yi tunanin idan babban jarumi kamar Khan ya yanke shawarar zai fice daga masana'antar finafinai abu ne da zai girgiza Indiya, kasar da ke matukar son finafinai.

Sai dai ya yi bayanin cewa ba a lura da ficewarsa ba saboda a lokacin finafinai kalilan ake yi saboda annobar.

"Babu wanda ya sani" in ji shi.

Hoton Aamir Khan ya na halartar bude taron Red Sea International Festival na shekarar 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aamir Khan na daya daga cikin shahararrun masu yin finafinai a Bollywood.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai hankalin masoyan Khan zai iya kwanciya a yanzu.

Khan bai bar yin finafinai na lokaci mai tsawo ba. A yanzu ya dawo kuma yana tallata wani fim da ya shirya mai suna Laapataa Ladies. Fim din shi aka zaba a Indiya a rukunin fim din da ya fi kowanne a fadin duniya a bikin bayar da lambar yabo na masana'antar fim wato Oscars.

Khan ya ce ƴaƴansa ne suka jawo hankalinsa domin ya koma aiki.

" Suka ce ' amma ba za mu iya shafe sa'oi 24 tare da kai ba. Don haka ka je ka yi rayuwa.' Su suka tunzura ni na koma fim," a cewarsa.

A shekara 59, Khan ya yi aiki a matsayin mai yin finafinai, mai bada umurni da kuma mai shiryawa na tsawon shekara 30.

An san shi a cikin daya daga cikin "Khans din Bollywood" su uku - sauran su ne shahararrun yan fim Shah Rukh da Salman.

Finafinansa da aka san su da taɓo muhimman batutuwan da ke shafar alumma, jama'a da dama na yaba wa kuma finafinan suna samun masu kallo fiye da yadda ake tunani.

Hakazalika shi ba bakon lambar Oscars ba ne. Fim din sa mai suna Lagaan da aka shirya a kan wasan kricket (Cricket) a karni na 19 lokacin mulkin Birtaniya, na daga cikin wadanda a ka zaba domin samun lambar yabo a rukunin fim din da ya fi fice da ba na turanci ba a shekarar 2002.

A yanzu kuma Khan na kokarin kafa tarihi da fim din Laapataa Ladies. Idan ya yi nasara, fim din zai kasance fim din Indiya na farko da ya samu lambar yabon mai matukar muhimmanci. A ranar Talata ne zai tabbatar ko fim din ya samu shiga jerin finafinan da ke neman lambar yabon.

Khan ya ce bai san wani irin muhimmanci zai bai wa samun lambar yabo ba. "Masana'antar finafinai na cike da son rai" a cewarsa.

Sai dai ya yarda cewa samun lambar yabon zai kasance abu mai muhimmanci ga Indiya.

Aamir Khan Productions

Asalin hoton, Aamir Khan Productions

Bayanan hoto, The film Lagaan, starring Aamir Khan, was a massive hit

"A gani na yan Indiya na matukar son fim kuma mun dade muna so mu samu lambar yabo a fim din Indiya a Oscars, wanda har yanzu ba mu samu nasara ba. A don haka yan kasar za su yi farin ciki mara misaltuwa idan muka yi nasara" inji shi.

"Saboda yan kasar da kuma kasarmu, zan yi farin ciki sosai idan muka samu lambar yabon."

Fim din "Laapataa Ladies" wanda aka yi shi a kauye, yana ba da labarin wani matashi da ya yi kuskuren kai amaryar da ba tasa ba gida. A gefe guda kuwa matarsa ta bace, ta ƙare ita ke kula da kanta."

Fim din na barkwanci ne da ke nuna abubuwan da ake yi wa mata, kuma ya tabo batun nan mai jan hankali na cin zarafin mata a gidaje.

Khan ya ce fim din na nuna abubuwa ma su muhimmanci a kan matsalolin mata, yancin su, da kuma hakkin su na zaben ma kansu abunda su ke so su yi".

Ya bayyana cewa tun da farko wadannan batutuwan ne ma suka janyo hankalin sa ga fim din.

" A wasu lokutan kana samun dama a matsayinka na mai ƙirƙire ƙirƙire domin ka wayar wa mutane kai kan wasu matsaloli da ake fuskanta a cikin alumma, " inji shi.

" Mata a fadin duniya na fuskantar kalubale da dama a rayuwarsu. Mata na fuskanta matsaloli. Saboda haka na ji cewa ga wani labari nan wanda ya fito da hakan a yanayi mai kyau, shiyasa na so in shirya shi."

Kiran Rao da Aamir Khan sun halarci tantance Fim din Laapataa Ladies a ranar 27 ga watan Fabrairun 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kiran Rao da Aamir Khan sun cigaba da aiki tare bayan rabuwarsu.

Khan ya kuma bukaci cewa tsohuwar matar sa Kiran Rao ce zata bayar da umurnin fim din.

Aamir da Kiran wadanda suka yi aure a 2005, sun sanar da rabuwar su a shekarar 2021. Amma sun kasance tare, a aiki da kuma lokutan da ba na aiki ba.

" Ina tunanin dalilin da ya sa na zabi Kiran shi ne, na san cewa za tayi aikin cikin gaskiya, kuma abun da na so kenan," inji shi.

" Abubuwan mu sunzo daya sosai. Muna son junan mu sosai, mu na mutunta juna.

" Alaƙar mu ta dan sauya- amma hakan ba ya nufin abunda mu ke ji kan junan mu ya ragu ba ko wani abu makamancin haka."

Sai dai kuma ba wai hakan na nufin komai na tafiya ba gargada bane.

Khan ya ce su na dan samun gardama a wurin shirya fina-finai.

" Ba ma iya shirya fim ba tare da munyi gardama ba. A kowani mataki muna gardama kuma duk mu na da ra'ayi mai karfi," a cewar shi.

'' Sai dai kuma ba ma daukan abu da zafi. Kawai mu na kokarin shawo kan ɗaya a cikin mu ne kan hanyan da ya fi dacewa a yi wani abu.''

Yadda ake kallon Bollywood a duniya

Hoton amare biyu da Angon da ke cikin rudani a Laapataa Ladies

Asalin hoton, Aamir Khan Productions

Bayanan hoto, Amare biyu an sauya su bisa kuskure a Laapataa Ladies

Masana'antar Bollywood na shirya daruruwan finafinai duk shekara, kuma suna da mabiya masu dimbin yawa a cikin ƴan India da ke fadin duniya.

Ba za a iya misalta irin shauƙin da fina finan da kuma taurarin Bollywood ke sanya wa mabiyan su ba.

A na samun nasarori a baya bayan nan a bikin Oscar, inda wakar RRR mai suna Naatu Naatu ta samu lambar yabon wakar da tafi kowacce, sai kuma Elephant Whisperers da ya samu lambar yabon gajeran fim din tarihi da yafi kowanne.

Sai dai har yanzu an gaza samun nasara a rukunin fina-finan duniya, wani abu da Khan ya alakanta da gasar da akeyi a rukunin.

" India ta shirya fina finai masu kyau sosai a shekarun baya baya. Wasu lokutan a kan samu matsalar fim din da ya kamata ba shi aka aika ba, ko kuma fim din da yafi kowanne ba shi a ka aika ba." inji shi.

"Banda haka kuma, Ya kamata muyi la'akari da cewa fina-finan da ake gasar tare da su, ba wai fina-finai biyar ko shida ba ne, kuna gasa ne da fina finai akalla 80 ko 90, wanda su ne su ka shahara a duniya.

A kan batun cewa ko wata rana fim din Bollywood zai samu nasarar samun lambar yabo na fim din da yafi kowanne a duniya, Khan ya ce abu ne da zai yiwu.

Ya kara da cewa sai dai akwai bukatar masu shirya fina finai su fara shirya fina finai ma kasuwan duniya.

" Ban taba la'akari da masu kallon mu na fadin duniya ba," a cewar shi. " Mu na da mabiya yan kasar mu ma su dimbim yawa da yasa ba ma la'akari da sauran.

" Hakan zai iya faruwa ne idan yan India suka fara yin film saboda mabiyan mu na duniya. Ba na tunanin dai munada karfin yin hakan a yanzu."

'Ba na aiki bayan karfe shida'

A yanzu dai, Khan ya mayar da hankali kan wasu fina-finan baya ga fim din Laapataa Ladies, cikin su har da fim dinsa mai zuwa nan gaba mai suna Sitaare Zameen Par wanda za a saki a shekarar 2025.

Daga bisani kuma, ya na fatan shirya fim daya duk shekara, yayin da kuma aikin da yake burin yi shi ne sabunta fim din Mahabharat- wani tsohon fim din India da yayi fice.

Sai dai tun sanda ya dawo bayan ya bar fim, ya kudiri aniyar yin abubuwa daban da yadda a ka saba yi. Kuma, ƴaƴansa ne su ka janyo ra'ayin sa kan hakan.

''ɗa na ya ce, ' kai mutum ne mai tsanani'.

'' Ya ce, ' kai wani irin mutum ne na daban . A baya ka yi fim, fim, fim. yanzu kuma kana so ka kaɗa zuwa dayan bangaren ka daina fim ka koma iyalinka, iyalinka, iyalinka. Akwai wani wuri da ke tsakiya idan ka yi tunani.

Khan ya ce ɗansa ya faɗa mishi cewa ya yi ƙoƙarin kawo daidaito a rayuwarsa.

'' Kuma nayi tunani na ga ya na da gaskiya. Saboda haka tun daga nan na ke kokarin daidaita rayuwata kuma inyi aiki sosai, hakikanin gaskiya ma a yanzu ina aikin da ban tabayi a baya ba, sai dai a yanzu, ba na aiki bayan karfe 6.

Khan ya kuma ce ya fara neman waraka a shekarun baya bayan nan, wanda ƴar sa Ira ta bashi shawarar yi, wacce ke aiki a fannin lafiyar kwakwalwa.

'' A gani na, hakan abu ne da ya taimaka min sosai. Ya taimaka min fahimtar kaina sosai.''

'' A gaskiya na fara samun daidaito tsakanin aiki da rayuwata. Ina ganin na kai wannan matakin.''