Radhika Merchant: Matar da za ta auri ɗan mutum mafi arziƙi a Indiya

..

Asalin hoton, ANI

Bayanan hoto, Radhika Merchant za ta zama suruka a cikin iyalin Ambani, mutum mafi arziƙi a Indiya

"Ina ganin Radhika na ji zuciyata ta tsaya cak duk da cewa mu kasance tare na tsawon shekaru bakwai, amma gani nake yi kamar jiya-jiya ne.

Ba karamin sa’a na yi ba kasancewar na hadu da Radhika."

An gudanar da bukukuwan walima a shirye-shiryen auren Radhika Merchant da Anant Ambani ne a Jamnagar, da ke jihar Gujarat a ƙasar Indiya.

A wajen bikin ne Anant Ambani ya bayyana abin d ke zuciyarsa game da matashiyar wadda ke gab da zama matarsa.

Shaharraru mutane, ciki har da irin su Bill Gates, da Mark Zuckerbag da Rihanna sun halarci bikin na kwana uku da aka yi.

Radhika za ta kasance suruka a cikin iyalin Ambani, wadanda suka fi kowa kudi a Indiya.

Anant Ambani shi ne auta a cikin ‘ya’yan Mukesh Ambani. Radhika ta shahara ne yayin da ta yi wani bikin rawa a watan Disamban 2022.

An gudanar da rawar ne a katafaren wurin taro na Zia World Centre da ke Mumbai. Shaharrarun mutane da dama sun hallara a wajen.

..

Asalin hoton, ANI

Bayanan hoto, Radhika Merchant, Anant Ambani

Wace ce Radhika Merchant?

Radhika ɗiya ce ga Veeren Merchant, shugaban kamfanin haɗa magunguna na Encore Healthcare.

Radhika ta yi karatu ne a makarantar Cathedral and Joan Conan, da kuma makaranta Ecolo Modern, a birnin Mumbai

Ta kamala digirinta a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar New York. Ta yi aiki a matsayin shugaban sashen kula da cinikayya a kamfanin hada-hadar gine-gine na Isprava.

A halin yanzu kuma, tana cikin manyan daraktoci a kamfanin mahaifinta na Encore Healthcare.

..

Asalin hoton, ANI

Bayanan hoto, Rawar da Radhika a watan Disamban 2022 ne ya kara fito da ita

Karo na farko a watan Disamba 2022..

Baya ga neman ilimi a makaranta, ta kuma taɓa shiga harkar rawa na Bharata Natyam. Inda ta kwashe shekaru tana yi.

Radhika ta yi suna ne a lokacin da ta taka rawarta ta farko a shekarar 2022.

Radhika ta bayyana a shafinta na LinkedIn cewa baya ga kasuwanci tana kuma sha'awar batutuwa na kare hakkin dan'adam, da ƙarfafa tattalin arziƙi da samar da ilimi da kiwon lafiya.

Anant Ambani, Radhika Merchant

Asalin hoton, ANI

"Zuciyata ta tsaya cak a lokacin da na gan ta"

An yi baikon Anant da Radhika a wurin bauta na Srinathji da ke a jihar Rajasthan.

Amma ana tunanin su biyun sun haɗu ne tun lokacin suna makaranta.

Anant Ambani ya ce sun san junansu na tsawon shekara bakwai. An ga Radhika tare da iyalin Ambani a lokacin bikin auren Isha Ambani.

A ranar asabar ne Anant ya bayyana yadda yake ƙaunar Radhika a zuciyarsa inda ya ce “Ina ganin Radhika na ji zuciyata ta tsaya cak, duk da cewa mun kasance tare na tsawon shekaru bakwai, amma gani nake yi kamar jiya-jiya ne muka haɗu."