Manyan attajiran duniya sun hallara a Indiya don bikin auren ɗan wani attajiri

Iyalan Ambani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyalan Ambani a wajen baikon ɗansu da amaryarsa Radhika Merchant (na uku daga hagu) a watan Janairun 2023

Wasu daga cikin manyan masu fada a ji a duniya sun isa jihar Gujarat ta kasar Indiya domin halartar bikin auren mutum mafi dukiya a nahiyar Asiya.

Daga cikin bakin akwai shugaban facebook Mark Zuckerberg da shahararriyar mawakiya Rihanna da tsohon wanda ya fi kowa arziki a duniya Bill Gates.

Dukkanin su sun halarci walimar da Mukesh Ambani, shugaban rukunin kamfanonin Reliance Industries, kuma attajiri mafi dukiya a nahiyar Asiya ya shirya domin murnan bikin auren dan shi.

Matashi Anant Ambani, mai shekara 28 a duniya zai auri masoyiyarsa Radhika Merchant a cikin watan Yuli.

Shahararrun ‘yan wasan f na Indiya, Shah Rukh Khan da Amitabh Bachchan na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta kwana uku wadda ta gudana a birnin Jamnagar.

Yanzu haka Mukesh Ambani, mai shekara 66 a duniya shi ne mutum na 10 a jerin mutane mafiya kudi a duniya, inda dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 115, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

Mahaifin Mukeh Ambani ne ya kafa rukunin kamfanin Reliance Industries a shekarar 1966, wanda katafaren rukunin kamfanoni ne da ya kunshi hadawa da sayar da kaya daban-daban sai kuma harkar hada-hadar kudi da na sadarwa.

Anant Ambani shi ne dan’auta a cikin ‘yayan mahaifin nasa uku, wadanda dukkanin su suke cikin manyan shugabannin rukunin kamfanonin na Reliance Industries.

Matashin na aiki a bangaren kasuwancin makamashi na rukunin kamfanonin kuma yana cikin shugabannin da ke tafiyar da lamurran gidauniyar rukunin kamfanonin.

Wannan kasaitacciyar walimar aure ta ji da gani daya ce daga cikin irin su da iyalan na Ambani suka yi kaurin suna wajen shiryawa.

A 2018, shahararriyar mawakiyar Amurka, Beyonce na daga cikin wadanda suka cashe a walimar daurin auren ‘yar Mista Ambani, Isha Ambani, wanda aka yi a birnin Udaipur. Tsofaffin sakatarorin harkokin waje na Amurka Hillary Clinton da John Kerry na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta wancan lokaci.

Wani rahoto na kafar yada labaru ta Bloomberg a wancan lokaci ya kiyasta cewa an kashe kudi dalar Amurka miliyan 100 a lokacin bikin - sai dai wani ‘na kusa da iyalin Ambani’ ya musanta batun, inda ya ce kudin da aka kashe bai wuce dala miliyan 15 ba.

Walimar ta wannan karo ta fara ne daga farkon wannan mako, inda iyalin na Ambani suka raba abinci ga al’ummar garin Jamnagar.

Anant Ambani tare da amaryarsa Radhika Merchant
Bayanan hoto, Anant Ambani tare da amaryarsa Radhika Merchant a wajen bikin cin abinci da aka shirya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kimanin baki 1,200 ne ke halartar walimar wadda ke gudana a birnin Jamnagar, kusa da matatar mai ta Reliance.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewar cikin bakin da ke halartar walimar akwai manyan attajiran Indiya kamar Gautam Adani da Kumar Mangalan Birla.

Sannan ana sa ran halartar shugaban kamfanin Disney, Bob Iger, kuma hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kamfaninsa ya sanar da hade kadarorinsa da ke Indiya da na rukunin kamfanonin Reliance.

Zuckerberg, wanda yake wani rangadi a kasashen Asiya, ya isa wurin bikin ne a ranar Alhamis.

Shi kuma Bill Gates wanda ya isa kasar ta Indiya cikin kwanaki kadan da suka gabata, ya wallafa bidiyo yana shan shayi wanda ya saye a wurin masu hada shayin gargajiya - bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta.

Sauran wadanda aka gani sun hallara wurin walimar a ranar Juma’a sun hada da shahararrun yan wasan kurket Mahendra Singh Dhoni da Dwayne Bravo, sai kuma shugaban kamfanin BP, Murray Auchincloss.

Sauran bakin da aka gani wurin taron sun hada da maidakin tsohon shugaban Amurka, Ivanka Trump, da tsoffin firaministocin Canada da Autralia, wato Stephen Harper da Kevin Rudd.

Mark Zuckerberg and wife Priscilla

Asalin hoton, ANI news agency

Bayanan hoto, Mark Zuckerberg tare da matarsa Priscilla bayan isa Jamnagar

Ana sa ran bakin da za su halarci daurin auren za su kuma ziyarci wata cibiyar da ale ajiye dabbobin da aka ceto da ke birnin na Jamnagar, wanda rahotanni suka ce yana kunshe da dabbobi sama da 2,000.