Dan arewacin Najeriya da ya zama malamin harshen Indiya

Bayanan bidiyo, Dan arewacin Najeriya da ke koyar da harshen hindu

Ba’indiyen Bahaushe.

Duk da cewa Indiya ba bakon harshe ba ne a kasar Hausa amma ba kasafai ake samun wanda ya kware har yake koyar da shi ba a cikin al’umma.

Salman Muhammad Waddare ya shaida wa BBC cewa matukar sha’awar harshen ne ya kai shi ga wannan matsayi.