Abin da ya sa Amita ya ƙi yin fim tare da Kareena

Asalin hoton, Facebook
Fina-finan Indiya na ƙayatar da mutane da dama a faɗin duniya saboda yadda labarinsu ke tafiya da kuma al'adu masu ban sha'awa.
Wannan ya sanya ƴan wasan fim na Indiya suka yi suna a faɗin duniya.
To amma duk da haka ba abin da kuke gani a fina-finai ne ke tabbatar da abubuwan da suke faruwa a fili ba.
Lamarin kan kai ga cewa wasu daga cikin taurarin kan ƙi amincewa su fito a fim ɗaya tare da wasu.
Mun ɗauko muku wasu abubuwa da wataƙila ba kun san sun faru ba a bayan fage tsakanin wasu taurarin na masana'antar Bollywood.
Ranbir Kapoor da Sonakshi Sinha

Asalin hoton, AFP
Ranbir Kapoor da Sonakshi Sinha na daga cikin sanannun taurari a masana'antar fim ta Indiya.
Kuma suna da magoya masu yawan gaske.
To sai dai rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa Ranbir ya daina shiga duk wani fim da ya ƙunshi jaruma Sonakshi Sinha, kuma hujjarsa ita: "ta tsufa da yawa."
An so a haɗa su a wani fim na ban-dariya amma sai Ranbir ya ce Sonakshi ba ta dace da rawar ba.
Sonakshi tauraruwa ce mai shekara 36 da haihuwa yayin da Ranbir yake da shekara 41, amma ya buƙaci a samu wata jaruma mai ƙarancin shekaru fiye da Sonakshi.
Sai dai masu shirya fim ɗin ba su ɗauki buƙatar tasa da muhimmanci ba.
Daga baya Ranbir ya yanke shawarar ƙin shiga fim ɗin.
A shekara ta 2014 an sanya Sonakshi a matsayi na biyar cikin jerin taurarin fim mata mafiya bajinta a Indiya.
Amitabh Bachchan da Kareena Kapoor

Asalin hoton, Reuters
A nasa ɓangaren, Amitabh Bachchan ya ƙi yin wani fim da jaruma Kareena Kapoor ta so su yi tare.
Abin da ya janyo hakan shi ne katsewar soyayyar Abhishek da Karishma Kapoor, wadda ƴar uwar Kareena ce.
Soyayyarsu ta watse ne a watan Fabarairun 2003.
Daga baya an maye gurbin Kareena da Rani Mukherjee a cikin fim ɗin mai taken Baabul, wanda aka saki a 2005.
Fim ɗin ya haska manyan taurari irin su Salman Khan da Hema Malini.
Aishwarya Rai da Abhishek Bachchan

Asalin hoton, AFP
Aishwarya ta taɓa ƙin amincewa ta fito a fim ɗaya da mijinta Abhishek Bachchan.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan aurensu, inda ta nuna ƙarara cewa ba ta son taka rawa a fim ɗaya da maigidan nata.
Fim ɗin da ta ƙi fitowa tare da shi shi ne Dostana, inda taurari irin su Abhishek da John Abraham da Priyanka Chopra, da kuma Bobby Deol suka ɓarje gumi.
Duk da cewa mashiryin fim ɗin, Karan Johar ya so Aishwarya ta zama babbar tauraruwar fim ɗin, daga baya ya amince Priyanka Chopra ta hau rol ɗin, kuma ta taka rawar yadda ya kamata har ta burge masu kallo.
Kareena Kapoor da Emraan Hashmi

Asalin hoton, Reuters
Fim ɗin Badtameez Dil wanda aka saki a 2015, wanda Ekta Kapoor da Karan Johar suka shirya, tun farko an tsara cewa Emraan Hashmi da Kareena Kapoor su ne manyan taurari a fim ɗin.
Sai Kareena ta janye daga shirin bayan da ta ce ba za ta iya ɗaukar wata fitowa ba inda suke sumbatar juna.
Kareena Kapoor tauraruwa ce mai shekara 43 kuma ita ce matar tauraro Saif Ali Khan.
Salman Khan da Aishwarya Rai

Asalin hoton, Reuters
An yi wa tauraro Salman Khan da takwarar aikinsa Aishwarya Rai tayin fitowa a fim ɗin Bajirao Mastani, wanda Sanjay Leela Bhansali ya shirya.
Sai dai an samu mummunan saɓani tsakanin jaruman biyu a lokacin da aka fara ɗaukar fim ɗin, inda ala tilas aka dakatar da aikin.
Daga baya an samu taurari irin su Ranveer Singh da Deepika Padukone da kuma Priyanka Chopra suka fito a fim ɗin.
An saki fim ɗin ne a watan Disamban 2015.
Katrina Kaif

Asalin hoton, AFP
Bayan sakin fim ɗinta wanda ya haska sosai, wato Tiger Zinda Hai a watan Disamban 2017, Katrina Kaif ta zama fitacciya a wurin masoya fina-finai.
Daga nan ne Aditya Roy Kapoor ya yi mata tayin taka rawa tare da shi a wani fim nasa, sai dai ta ƙi amincewa.
Daga baya, bayanai daga wasu na kusa da ita sun nuna cewa ta ƙi yin fim ɗin tare da shi ne saboda wasu abubuwa da jarumin ya yi a baya, waɗanda ta ƙi jini.














