Daga bakonmu na mako: 'Yadda kallon fina-finan Indiya ke ɗauke wa mata hankali a Najeriya'

Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙuwarmu ta mako: Aisha Ya'u Kura, marubuciya kuma tana karata Lissafi a Jam'iar Jihar Kaduna. Tan a da aure da ƴaƴa biyar.

Indian series

Asalin hoton, Zee World Facebook

Kallace-kallacen shiri mai dogon zango na Indiya ya zama ruwan dare a faɗin duniya.. Soyayyar su ta yi tasiri a zuƙatan manya da yara da mata da wasu mazan a Afrika, ya kuma ƙetaro Najeriya har ya zarto arewacin ƙasar, wanda har hakan ya daƙushe tasirin kallon fina-finan Hausa.

Da fari a wata tasha mai suna MBC Bollywood ita ce tashar da ta fi kawo shirye-shiryen fina-finan Indiya da ake cewa series da harshen Larabci.

Zuwan Zee world sai ya soma daƙushe kallon tashar saboda da yawa an fi fahimtar yaren Turanci a kan Larabci a wannan lokacin.

Ganin karɓuwar wadannan fina-finai ya sanya wasu tashoshi na arewa fara fassara su da harshen Hausa domin samarwa Hausawa saukin fahimtar abun da ake yi, kuma ake faɗi a cikin shirin.

Kowanne abu na duniya akwai alkhairin da ke cikinsa, kazalika akwai illolinsa..

Zan iya cewa illolin da wadannan fina-finai suke yi mana a arewacin Najeriya ya fi alkhairansu yawa.

Mu kawo Zee world a farkon fari, a yanzu ana fara shirye-shiryen Zee World tun daga karfe uku na rana har karfe 11 na dare. Da yawa, ban ce duka ba, akwai matan da ba sa barin gaban talabijin ɗinsu har sai wannan karfe 11 musamman idan an bar wutar lantarki ko da halin tayar da injin yayin da aka ɗauke wuta.

Wasu kuma in kaga sun dauke idanunsu daga gaban talabijin to an tafi talla ne, shi ne za su tashi a gurguje su je su yi abin da za su yi kafin a dawo, ciki har da gaida Allah SWT wanda ya halicce mu kuma ya ba mu aron rai da lafiyar da muke kallon da shi.

Wasu matan ko girki ba za su ɗora ba, wasu kuma su manta sun ɗora har sai ƙaurin abincin ya addabi hancinsu, komai za su yi a dan tsukukun mintinan tallan za su je su yi shi da sauri domin kar kallon ya wuce su ko da na daƙiƙa ɗaya ne.

Wasu kuma ba za su ɗora girkin ba, sun gwammaci su kwanta su yi ta kallon har mijin nasu ya dawo, a gaggauce su dafa masa indomie ta hanyar yin ƙaryar ba sa jin daɗin jikinsu ne.

Abu mafi muni a cikin illar shi ne; Daga wannan ƙarfe 11 da suka gama kallon shirye-shiryen, za su fara maimaici saboda wanda bai samu damar kallo ba ya kalla, wasu na iya fara maimaicin tun daga karfe 12 na dare har asuba sannan su kwanta.

Sannan a daren ranar Juma'a, tun daga 12 na dare za su fara maimaicin shirin satin, in ya wuceka za su hade maka shi ka kallesu baki daya, a daren da ya kamata mu miƙa wuya ga Allah, a wannan daren muke miƙawa fina-finan nan idanuwanmu da ruhinmu gangar jikinmu gurin kallon wasanninsu.

Aikin da babu lada a barshi a jingine shi yafi

indian series

Asalin hoton, Zee World

Bayanan hoto, Fina-finan kan dauke hankalin mata da dama har su bar girki ya dinga konewa

Allah bai kawo mu duniya domin wasa ba, amma mun shagaltar da kanmu gurin yin wasan har ta kai mu ga kwaikwayonsu.

Wadannan kallace-kallacen har wata mai alfarma bai bari ba, domin a lokacin ne ma shaidan ke sake sabon salo na kiɗansa, sai mu ƙi yin kallon a lokacin da ake yi, sai mu ce da daddare za mu yi kallon in muna Tahajjud.

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"

Ni din nan da nake wannan rubutun ni ma a da hakan nake, sai dai mu ce Allah ya tsare mana imaninmu.

Wannan layi ne

Illolin da wadannan shirye-shiryen suke yi a tsakanin ƙananan yara da matasa mata da al'umma baki daya

Mata su ne ginshiki, tubalin tarbiyar yaransu, mace ita ce tsani na tarbiyyar iyali, wanda masu iya magana kan ce, idan ka ilimintar da mace tamkar ka ilimantar da alumma ne.

Kowanne dan adam a hannun mace ya taso, kuma a hannunta zai ƙare rayuwarsa, amma a wannan lokacin da kallace-kallace suka yi yawa sam mun manta da tarbiyyar ƴaƴanmu, mun miƙa musu ragamar komai su yi da kansu yayin da muke kallo, sai ka ji wasu na cewa, "Ku tashi ku je dakinku ku yi kallo, ko ku fita waje ku yi wasa".

Ko kusa ba ma bibiyar rayuwarsu, mu dai su bar mu mu yi kallonmu su kuma su je su yi wasansu wanda mu kanmu ba mu san wane iri wasa suke yi ba, daga haka sai ka ga yaro ko ya je makaranta ba shi da wani sukuni sai na bai wa abokan karatunsa labarai a kan fina-finai.

Sai ka ga yara da ƙananan shekarunsu sun yi gungu suna fadin: "Jiya Mayank ya ce yana SON Gunjan, au ba ku ga wurin ba?

Nan za su fara ba da labarin irin abun da suka gani wanda su masu shirya fim ɗin a gurin su suke ganinsa ba komai ba ne, to daga nan shikenan tarbiyya ta tafi a haka, yara sun taso sun saba da kallace-kallace wanda har za su dinga aiwatar da shi a tsakanin su da sunan wasa.

Aisha Ya'u Kura

Asalin hoton, Aishatu Kura

Bayanan hoto, Bakuwarmu ta wannan makon ita ce Aisha Ya'u Kura, marubuciya kuma tana karanta Lissafi a Jam'iar Jihar Kaduna. Tana da aure da ƴaƴa biyar

Wannan ma babban sakaci ne a garemu iyaye mata, domin tarbiyyarsu da tamu ba daya ba ce, su a gurinsu raina iyaye ba komai ba ne, to in yaro ya tashi da shi shi ma zai ga ba koman ba ne.

Sannan ga ƴan mata matasa masu tasowa, za ka ga sun raina duk wani namiji da zai zo gurin su, duk abin da zai yi mata da niyyar burgewa sai ta ga sam bai kamo kafar SIDDART KHURANA ba.

A nan fa yarinya za ta shiga bulayi har ta tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi mata kafa, daga nan sai a shiga damuwa a ce ai wance ba ta yi aure ba, ko dai aljanu ne suka shafe ta.

Abin da ba mu sani ba shi ne lokacin da budurci ya tatsowa mace, in har ta tsaya ruwan ido to tabbas za ta shiga jerin matan da suka yi kwantai wanda za su yi auren a ƙagauce ba tare da tantacewa ba.. SIDDART da SALIHU akwai banbanci, haka "Indiya da Najeriya" ban ga ta inda harafi ko furuci ya haɗa su ba.

A yadda wasu fina-finan suke zuwa da zallar makirce-makirce hakan yana sa yara mata koyon wadannan salon ba tare da duban illarsu ko halaccinsu a addininmu ba, mu dai mun ga wasu a ciki sun yi sun ci riba, mu ma bari mu gwada.

Mukan manta cewa su ma shirya shi suka yi, tsara labarin aka yi, mu dai kawai tun da an yi, bari mu ma mu yi, wanda hakan sai ya jefa mutum cikin da na sani marar amfani.

Ko a cikin al'umma wadannan shirye-shiryen sun yi tasiri ta hanyar koyar da salon sata da satar mutane don kudin fansa da mugunta da salon makirci da dai sauran su.

Wannan layi ne

Ƙarin labarai masu alaƙa

Shawara ga mata

zee world

Asalin hoton, Zee World

Illoli da sharrance-sharrancen fina-finan nan yawa ne da su, alkhairansu bai wuce dauke mana hankali daga gulmace-gulmace da surutai marasa amfani wanda shi ma illa ce babba a garemu.

Shawara garemu mata, ko za mu yi wadannan kallace-kallacen ya zam mun sauke duk wani hakki da ya rataya a wuyanmu, sannan mu ragewa ƴaƴanmu yawan yinsa, mu kuma cire wa Ubangijinmu lokacinsa, domin lokacin Ubangiji ya fi duniya da abun da ke cikinta, mu yawaita yin istigfari da hailala yayin kallon, mu kanmu a cikin zukatanmu za mu ji nutsuwa yayin yin hakan.

Allah ya tsaftace zukatanmu ya tsayar da mu a kan addinin Allah na gaskiya, kuma ya dauwamar da zukatanmu gurin bauta masa.

Wannan layi ne