Daga baƙonmu na mako: Labarina Series; Ma'anar mai hakuri yakan dafa dutse ya sha romonsa

Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙonmu na mako: Hashim Abdallah Mallam-madori yana koyar da Turanci da Adabi a Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia, da ke jihar Jigawa a Najeriya. Dukkan abubuwan da ke cikinta ra'ayinsa ne ba na BBC ba.

Labarina Series shiri ne da Kamfanin Saira Movies na Malam Aminu Saira ya dauki naiyun shiryawa

Asalin hoton, Aminu Saira

Kallo ya koma sama, wato shaho ya suri giwa sama kamar yadda yake zarar dan tsako. Lallai Bahaushe ya yi hikima da fadin haka, domin dan tsako kadai shaho zai iya sura.

Kusan wata guda ke nan, tashar talabijin ta Arewa24 ta fara nuna wani shirin fim mai suna 'Labarina' wanda rubutu ne na wani labari wanda fitaccen marubuci Ibrahim Birniwa ya kago.

Hankali ya karkata ne saboda Arewa24 sun saba nuna sababbin shirye-shirye da suke fito da sababbin jarumai, sai shahara da kwarewa da kayan aikin zamaninsu da kuma iya karkatar da hankalin matasa, maza da 'yan matan cikinsu.

Abu na biyu wajen karkatar matasan ko a tsakankanin marubuta ita ce, shaharar marubucin wajen rubutun labari mai rike mai kallo wajen kawo rikita-rikitar da ke sakawa mai kallo son ganin ya za a karke ko ya za a warware a ko yaushe.

Abin da ya ja hankalina a kan yin wannan rubutun shi ne, tun a kashi na farko wasu masharhanta suka nuna karewar labarin - wanda maudu'insa shi ne juriya da hakuri - da watakila kashi daya kawai aka nuna daga kashi 12 ko 13 ko wajejen hakan da shi ne zango daya (season one) a fim mai dogon zango (series film).

Sun fadi hakan ne domin wani abin takaicin da ya yi barazanar faruwa a kan babbar tauraruwar shirin.

Sai dai shirin na biyu ya nuna lallai labarin ya tafi da masu wannan hasashen, domin hakan ba ta faru ba. Da ma ai sani ko camkar abin da zai faru ka iya zama nakasu ga marubuci, domin kunshiyar labarin da sako ko manufa ko sarrafa jigonsa na hannunsa kacokam, kuma rashin sanin me zai faru da jiran abin da zai faru din shi ne ke jan mai kallo ya ci gaba da yin kallon.

Wannan layi ne

Mene ne jigon labarin?

Nafisa Abdullahi

Asalin hoton, Aminu Saira

Bayanan hoto, Fitacciyar tauraruwa Nafisa Abdullahi ita ce ƙashin bayan fim din

Haƙiƙa ni ma ba na ganin don an yi amfani da talauci, kamar yadda yake a fim din, an tilasta wa babbar tauraruwa, an yi ma ta abu mai kama da fyade, shikenan labarin ya kare ba.

Watakila, an yi hasashen lalacewar labarin ne don tausayi ko burin abin da mai kallo yake so ya kasance a kan tauraruwar. Sai dai mai kallon ya manta shi ne yake son kasancewar abin, ba marubucin ba ne.

Abin lura ne, tunda an san kashi na 1 (episode 1) kawai aka nuna a lokacin da aka yi hasashen, saura wajen goma-sha, amma duk da haka aka bigi kirji aka iya cewa, idan wancan abu ya faru labari ya kare.

Watakila a ganin masu ra'ayin labarin ya kare a 'episode one' kadai suna nufin babu wani abin jan hankali, ko kuma ba za a iya ci gaba da jan zaren labarin ba ne ya gamsar, ko kuma suna nufin duk wani darasi ya kare.

Cewa labarin ya kare da afkuwar wancan cin zarafi ga tauraruwa, wannan ra'ayi ne kawai, domin watakila sannan labarin zai fara kamar dai yadda wata marubuciya, Hajiya Bilkisu Babandede ta fada.

Lallai, a ganina ni din ma, watakila sannan ne za a tsokano tsuliyar dodon labarin. Wato, idan zan ba da misali, sai in ce sannan 'fansa' za ta iya zama wani jigo a labarin idan marubucin haka ya kunso tun farko. Watakila ma wacce iftila'in cin zarafin ya fadawa ta haifi dan da zai zo ya kashe ubansa.

Bisa la'akari da sunan labarin, abu ne mai yiwuwa wacce aka ci zarafin ta mutu (in Marubucin ya so) sai a wayi gari, ashe labari ake ba wa mai kallo, sai a ga wanda ya yi fyaden shi ne shugaban kasa ko gwamna.

Kofofin marubuci na linkaya da kurda-kurda dai yawa ne da su, kuma suna kunshe a kirjinsa, ba a iya rufe su ko hasashen abin da zai faru. Domin idan har aka gane abin da zai faru, ba a bayar da tunanin mai kallo ba, to kallonsa ma ba zai yi dadi balle armashi ba.

Ko in ce ba zai ma yi amfani ba, kuma hakan rashin kwarewar dabaru ne, wadanda suna daga cikin matsaloli a nakasun marubutan Hausa da na sha ji ana fada. Kamar dai an fi so marubuci kar ya bar kofar gano me zai faru.

Ko a 'Labarina' din na Arewa24, iya gano abin da zai faru din ne ya sa aka ce labarin ya kare idan wancan abin takaici ya faru, amma sai aka waske, wanda ko ba a waske din ba, wadancan abubuwa da na zayyano wadanda akwai ire-irensu ba iyaka a kirazan marubuta, na iya faruwa, labarin ya zama sabo ko a samu fahimtar yanzu ma za a fara.

Wannan layi ne

Matsayin jan hankali a labari

Labarina Series shiri ne da Kamfanin Saira Movies na Malam Aminu Saira ya dauki naiyun shiryawa

Asalin hoton, Aminu Saira

Bayanan hoto, Labarina Series shiri ne da kamfanin Saira Movies na Malam Aminu Saira ya dauki nauyin shiryawa

Masana kuma masu sharhi ko kawo sukar nakasu ko duba ga kyawun labari ko kiyaye da cewar sakon makagin labari ya isa ko akasin haka, sun hadu a kan labari ba ya samuwa sai dole da wani sabani 'irony' wanda za a iya kiransa da rikita-rikita ko rudani 'conflict', ko da a labarin ban dariya ne kuwa.

Sannan labari yana yin dadi 'exciting', ya yi fice, ya yi tasiri har a kira shi da 'classical' idan ya iya sa mai kallo 'viewer' ko mai karatu 'reader' ko mai sauraro 'listener' a cikin zakuwa/damuwa da aka fi sani da 'suspense', musamman a yanayin ban tausayi ko takaici ko damuwa ko da-na-sani, 'tragedy'.

Irin wannan, ta yiwu ya janyo tausayi musamman saboda rashin sani ko fargaba na al'amarin da zai faru a gaba, ko kuma yayin tunkarowar hatsari ko al'amari mai daure kai, musamman idan mai kallon ya kwallafa kaunarsa ga tauraro. Kuma ga shi da gangan marubucin labarin ya cusa so da tausayin tauraron.

Sai dai, wani shahararren malamina na jami'a, Farfesa Ibrahim Bello-Kano (IBK), wanda ya yi tsiri a iya nakadin Adabi da falsafar magana da sharhi ko binciko nakasu, ya ce wani Bajamushe marubucin labarin ban takaici mai suna, Franz Kafka, ba ya so ma ake tausayawa irin wannan tauraro duk irin halin da ya shiga a wani labari, The Trial.

A irin wannan zubi, mai kallon yakan samu kansa yana son cimma buri ko kubuta ko yin galabar tauraron a kan makiyansa, wato 'antagonist(s)' ko duk wani cikas. Hakan na iya kasancewa a tafiyar tauraron uwa-duniya 'adventure', musamman don wani buri ko alwashi 'mission'.

Mai kallon ko sauraro ko mai karatu yakan zama kuma ya rika ji kamar shi ne al'amarin ke faruwa da shi.

Mun sha ganin mai sauraro yana ba wa tauraro shawara duk da ya san ba ji yake ba. Na taba ganin dan kallo a silima ya duka kasa don gocewa harsashin bam da aka harbo lokacin da ya nufo fuskar talabijin ya ga kamar zai fito. Na sha ganin mai karatu yana kukan tausaya wa tauraron labarin da ke gabansa. Kuma watakila kun sha gani.

Wannan layi ne

Abin da mutane suka yi ta tsinkaye a wannan shiri shi ne an yawaita fitattun jarumai a shirin ko kuma an ba su manyan wurare. Yana daga ra'ayin wasu masharhantan fina-finai cewa, saka sabon tauraro ya fi ratsa mai kallo domin in bai san tararon ba ya fi yi wa labarin kallo a sabon labari, domin in da ya san shi, zai ke masa kallon sani da kwatancen dab'iunsa da na fim dinsa na baya.

Ga sabon tauraro kuma, duk abin da ya bayyana zai ke ganin gaske ne.

In aka ce ka gama ganin tauraro da sunaye ba adadi, da iyaye daban-daban fiye da ashirin a fina-finai kusan dari ko fi, watakila ya mutu sau 3 mafi karanci. Komai nasa dai ka hakkake ba gaske ba ne, shiri ne bayan an san koyaushe so ake ake koyaushe ake kaddarawa al'amarin wata kirkirar Adabi zahiri ne.

Wanda hakan ne yake sa dan kallo ko mai karatu ko sauraro yake sha'afa da al'amarin shiri ne ya zubar da hawayensa.

Abu na gaba game da sanya sababbin jarumai, wanda shi ma muhimmi ne, shi ne fito da su, su nuna irin tasu baiwa da kwarewar. Domin ba wani abu da ya fice shahara ko yin fice ko kawarewa da ke sa ake ci gaba da sa tsofaffin jarumai ana maimaitawa. Ai kuwa sai an ba wa sabon jarumin dama ya taka rawa har za a ga kwarewar tasa. Shi ma fitaccen da guda daya ya fara, ko in ce dama aka fara ba shi ya gwada.

Dadi da kari, zan iya cewa dadin sabo shi ne, yakan dage ya ba da iya iyawarsa saboda yana son fitowa. Ga shi ba ya tsada, balle yanga ko saka sharadi. Ta kai ta kawo, shaharar wasu tana sa suna iko kuma masu shirin, tun daga darakta zuwa kan furodusa suna dari-dari da juya su yadda suke so, hakan kuwa, ba karamin nakasu zai kawo wa shirin ba.

A sababbin kuwa, akwai wanda zai yi a kyauta, yana rawar jiki don kawai sunansa ya fito.

Mutane da yawa, musamman matasa suna da baiwarwaki da Ubangiji ya huwace musu, sai dai rashin samun dama. In suka samu damar za a gano da magani a gonar yaro.

Wannan layi ne