Rahama Sadau: 'Na ji kamar zan mutu lokacin kullen korona'

Rahama Sadau

Asalin hoton, @artssassin/Pixel Pitch

Bayanan hoto, Rahama ta ce mutane da dama suna son ta da aure
Lokacin karatu: Minti 3

Fitacciyar tauraruwar Rahama Sadau ta ce ta ji kamar za ta mutu lokacin kullen korona saboda yadda take zaune wuri guda na tsawon watanni.

Ta bayyana hakan ne a hira ta musamman da Nasidi Adamu Yahaya a shafinmu na Instagram.

"Lokacin kullen sai dai mutum ya yi ta yin kame-make. Ka yi karatu ya ishe ka, ka yi kallo ya ishe ka, ka yi chatting ya ishe ka," in ji ta.

Ta ce kullen ne ya sa ba a jin duriyarta kwana biyu.

Har ila yau Rahama ta ce ta ji babu dadi a lokacin kuma ta ji "kamar za ta mutu."

Ta ce sana'arsu tana bukatar tara jama'a kuma yanzu an hana yin hakan saboda wannan annoba saboda haka a cewarsa korana ta fi shafar su fiye da kowa.

Rahama Sadau

Asalin hoton, Pixel Pitch

Bayanan hoto, 'Ban daina yin fina-finan Nollywood ba'

Rahama ta ce ta kammala karatunta, inda ta karanta fannin Human Resource Management a kasar Syprus.

Ta ce karatun ne ya sa ba ta iya ci gaba da harkokin fina-finanta ba gadan-gadan.

Tauraruwar ta ce tana iya magana da harshe uku Hausa, Turancin Inglishi da kuma Indiyanci.

Rahama ta ce mutane da dama suna son ta da aure,"yawanci sai dai na yi dariya ko kuma na ce na gode," in ji ta.

Sai dai ta ce ita ba ta da wani saurayi a Kannywood a halin yanzu.

Ce-ce-ku-ce

Rahama Sadau

Asalin hoton, @artssassin/Pixel Pitch

Dangane da yadda take yawan jawo ce-ce-ku-ce, Rahama ta ce hakan yana faruwa ne saboda yadda "duk abin da na yi duk kankantarsa mutane sai sun yi magana a kai."

Rahama ta ce hakan ba ya sa ta damuwa "saboda mafiyawanci ban cika gani ba."

"Idan na ga mutum daya ya fara magana mara dadi, fita nake yi gaba daya. Ba na ganin sauran, sai komai ya yi sauki. Wani lokacin kuma ina gani ban zan iya sa abu ya dame ni ba, abin da bai kai ya kawo ba,"a cewarta.

Fyade

Ta ce ba ta jin dadin yadda matsalar fyade take ci gaba tabarbarewa, tana mai cewa abin yana daure mata kai.

"Nakan tambayi mutane wannan abin da ke faruwa da gaske ne... wasu za ka ga 'ya'yansu suke wa. Wai duk na mene ne," in ji ta.

Ta ci gaba da cewa "wannan abin bacin rai ne ba kadan ba."

Ta bukaci hukumomi da su dauki manyan matakai don dakile matsalar kuma ta ce ya kamata kowa ya tashi tsaye kan batun.

Siyasa

Tauraruwar ta ce ita ba ta siyasa, ta ce ita 'yar Najeriya ce kamar kowa duk abin da ta ya yi mata za ta iya magana a kai.

"Ni na san wanda na zaba ba sai zo na nuna haka ba, cewa ni na zabi wane ba. Ban sani ba ko a nan gaba zan fara siyasa, amma a yanzu a'a," in ji ta.

Ta ci gaba da cewa "idan na jefa maka kuri'a, amma sai ka ki yin abin da ya kamata to zan fito na yi magana."

Karin labarai masu alaka da wannan: