Daga baƙonmu na mako: Daɗin Kowa, Rimi Adon Gari

Dadin Kowa

Asalin hoton, Arewa24

Fim mai dogon zango sabon al'amari ne a harkar fina-finan Hausa, waɗanda galibi ake shiryawa a arewacin Najeriya.

Wannan nau'in fim ya ƙunshi labari mai tsayi sosai, saɓanin irin waɗanda aka saba gani a masana'antar Kannywood - wato gajerun fina-finai da akan iya kalla a lokaci guda su ƙare.

Galibin fim mai dogon zango yana da jigogi manya da ƙanana.

Daɗin Kowa yana ɗaya daga cikin fina-finan Hausa masu dogon zango na farko-farko.

Hasali ma, zan iya cewa, shi ne fim ɗin Hausa mai dogon zango mafi shahara da karɓuwa a wajen mutane kawo yanzu - musamman a baya-baya nan.

Fim ne mai cike da abubuwan barkwanci, da ban tausayi, da ban haushi da kuma darussa kan zamantakewar al'umma.

Wannan fim, ana nuna shi a tashar talabijin ta Arewa24, kuma a halin da ake ciki, ana cikin zango na uku mai taken: "Wasa Farin Girki".

Wannan ya biyo bayan "Daɗin Kowa" zangon farko da kuma "Sabon Salo".

Mece ce alkiblar fim din Daɗin Kowa?

Bayanan bidiyo, Bidiyon hirar BBC da Kamaye da Adama

Batutuwan watsi da al'amuran iyali da wasu iyaye kan yi, da son zuciya da kuma tsananin buri, su ne jigogin da marubuta fim ɗin Daɗin Kowa suka fi mayar da hankali a kai.

Malam Kabiru Makaho na fifita buƙatarsa ta tara kuɗi domin ya tafi aikin Hajji a kan komai.

Duk da bara yake yi, amma yana samun rufin asirin da zai iya riƙe iyalinsa idan da hakan ne a gabansa. Amma ga alama, burin zuwa aikin Hajji ya mamaye zuciyarsa fiye da buƙatun iyalinsa.

Babbar ƴarsa, Alawiyya, ita ke faɗi-tashin ɗaukar ɗawainiyar iyalin da ɗan abin da take samu daga aikatau da sana'ar kitso da take yi.

Shi ya sa cin abinci a gidan kullum ba tabbataccen abu ba ne. Amma duk da ƙoƙarin da Alawiyya ke yi, wata rana sai mahaifinta ya tilasta mata ba shi wani abu daga ɗan abin da take samu.

Malam Kabiru mutum ne mai tsananin son zuciya. Ya sangarta ɗansa namiji ɗaya tilo mai suna Aminu AK. Ya zamar da ƙananan ƴaƴansa mata ƴan jagora.

Duk ƙoƙarin da matarsa Ladingo, mai fama da jinya, da kuma Alawiyya suka yi, na hana yaran raka babansu bara da kuma saka su a makaranta ya ci tura.

Jigon soyayya yana da matukar tasiri a fim ɗin. Mun ga irin tirka-tirkar da aka yi tsakanin Nazir da Alawiyya. Sannan tsakanin Gimbiya da Ibrahim IB da kuma Bintu a tsakiya. Mun ga yadda Ɗantani mai shayi ya sha wahalar soyayya.

Dadin Kowa

Asalin hoton, Arewa24

Iyayen Nazir sun ce ba za su haɗa zuri'a da Malam Kabiru makaho ba saboda mugun halinsa. Shi kuma Malam Kabiru ya ce ba zai ba Nazir Alawiya ba saboda ya raina arziƙinsa.

A ɗaya ɓangaren kuma, IB na son Gimbiya, ita kuma Bintu, wacce ƴar kawun IB ce tana ƙaunarsa sosai.

Matsalar tsaro babban jigo ne a fim ɗin Daɗin kowa. Mun ga yadda ɗan ta'adda, Malam Rabe ya shiga garin Daɗin Kowa, ya yi amfani da kuɗi da wasu dabaru wajen janyo ra'ayin wasu matasa suka shiga ƙungiyar ta'addanci.

Daga cikinsu akwai Aminu AK da abokanansa. Mun ga yadda ƴan ta'adda ke shirya manaƙisar kai hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba su gani ba.

An yi amfani da su Aminu AK aka kai hari a wani gidan kallon ƙwallon. A irin waɗannan hare-haren ne Anaconda, abokinsu Aminu ya rasa ransa.

Duk da halin rashi da iyalan Malam Kabiru ke ciki, sun iya bai wa ƴan gudun hijira, Gimbiya da Sa'adatu mafaka. Wannan na nuna duk kashin mutum, ya fi wani.

Ƙarin labarai masu alaƙa

Wannan layi ne

Talauci da Tawakalli da Almajirici

Marubutan fim ɗin sun nuna yadda talauci ke taimaka wa wajen taɓarɓarewar tarbiyya. Kamaye ya yi ƙoƙarin daidaita tarbiyyar ƴaƴansa, amma matarsa Adama ta hana, saboda ta raina masa arziƙi.

Daga ƙarshe, sai da ya rasa ɗaya daga cikin ƴaƴan nasa, sakamakon rashin lafiya mai nasaba da cikin shege da ta yayibo musu.

Sai dai kuma an nuna tasirin tawakkali da nuna juriya. Tsananin talauci da faɗawa iftila'i akai-akai da Kamaye ke fama da shi, bai sa ya yanke ƙauna da rahamar Allah ba.

Duk da Malam Tsalha ya yi ta ƙoƙarin ingiza shi ya kauce hanya, amma ya kafe kan imanin cewa Allah ne ya saka shi a halin da yake ciki, kuma shi zai fitar da shi idan ya ga dama.

Dadin Kowa

Asalin hoton, Arewa24

Babban jigon zango na biyu na fim ɗin Daɗin Kowa, da aka yi wa laƙabi da "Sabon Salo" shi ne almajiranci da yadda yake shafar rayuwar al'umma.

Malam Hassan da Malam Na-Ta'ala duk suna da tsangaya cike da ɗalibai, galibinsu ƙananan yara. Malam Hassan na tafiya bisa tsarin killace almajiransa waje guda ya dinga ɗaukar ɗawainiyarsu, da kuɗin da iyayensu ke ba shi don wannan manufar.

Shi kuma Malam Na-Ta'ala ya bar nasa ɗaliban kara-zube, suna tafiya bara. Sanadiyyar haka wani ɗalibinsa ya zama dillalin wiwi, har ya ja matarsa Azumi cikin harkar Malam bai sani ba. Wani ɗalibin nasa kuwa ɗan ta'adda ya zama.

A wannan karon, an ƙara fito da matsalolin da ƴan gudun hijira ke fuskanta a fili. Ƙuncin rayuwa ya jefa Gimbiya da Sa'adatu cikin mawuyacin hali, har ta kai ga sun miƙa kansu ga Madam Gloria ta yi safararsu zuwa ƙasar waje neman kuɗi.

A nan, marubutan sun nuna hatsarin da ke tattare da tafiya ci rani ta haramtacciyar hanya.

Marubutan, har wa yau, sun nuna yadda mummunar ɗabi'ar shaye-shaye ke yaɗuwa tsakanin mata, musamman ƴan mata. Da ƙyar Bintu ta sha, bayan ta biye wa ƙawarta sun zama ƴan maye.

A zangon da ake ciki yanzu, wato "Wasa Farin Girki", batun cin hanci da rashawa a matakai daban-daban na al'umma shi ne babban jigo. Malam Barau ''Headmaster'' ya baje kolinsa, yana ci da ci da gumin ɗaliban makarantar gwamnati.

Mustapha manajan hukumar wutar lantarki tare da muƙarrabansa suna ta harƙallarsu. Haka shi ma Kofur Audu ke amfani da matsayinsa na ɗan sanda ya dinga karɓar toshiyar-baki a wajen masu laifi.

Nasir ɗan Malam Hassan, ya kammala karatunsa, har ya yi aure. Amma ya zauna a gida yana jira lallai wai sai ya samu aikin ofis maimakon ya nemi duk wani aiki da zai rufa wa kansa da iyalinsa asiri.

Matsalar rashin abinci a gida ta sa matarsa ta yi yaji. Wannan matsala ce da galibin matasa ƴan boko ke fama da ita.

Marubutan suna ƙoƙarin fito da wata matsala da ta addabi Najeriya, musamman Arewaci. Wannan matsala kuwa ita ce rashin yarda da gani-gani da Musulmi da Kirista ke yi wa junansu.

Mun ga yadda Bintu da Malama Ladi Musa ƴar yi wa ƙasa hidima suka samu saɓani. Sai dai ina ganin sun fara fahimtar junansu yanzu.

Ƙarin maƙaloli daga baƙinmu na mako

Wannan layi ne

Daɗin Kowa, hantsi leka gidan kowa

Dadin Kowa

Asalin hoton, Arewa24

Babu shakka marubutan Daɗin Kowa sun nuna ƙwarewa sosai wajen tsara labari da kuma fito da jigo ɗaya bayan ɗaya. Fim ɗin labari ne mai ilimantarwa da nishaɗantarwa.

Har wa yau, marubutan suna yin la'akari da kowane rukuni na jama'a wajen isar da sakon. Shi ya sa maza da mata manya da ƙananan suka raja'a wa fim ɗin.

Haƙiƙa ƴan wasan sun yi ƙoƙari wajen isar da saƙon cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki. Yin amfani da fitattun jarumai irin su Lubabatu Madaki da Tijjani Asase da kuma Umar Mulumfashi tare da waɗanda ba su shahara sosai ba, ya ba ƴan kallo damar ganin tsofaffin hannu da sababbin hannu a fim ɗaya.

Su kuma sabbin zuwan suna samun damar koyon wani abu daga wurin gogaggun jaruman.

Sai dai ina ganin ci gaba da kasancewar Sallau a fim ɗin ba shi da wani tasiri, domin labarin ya nuna ba shi da sauran amfani.

Idan ma an dawo da shi domin barkwanci ne, ina ganin barkwancin nasa ya ƙare. Shi ma Wizzy ya bi sahun abokansa da su kai ɓatan dabo aka daina maganarsu.

A wannan zangon aka fara gabatar da TK, don samar da wani nau'i na barkwanci. Amma bisa ga dukan alamu ƴan kallo sun fara gundura da shi.

Malam Musa tsohon soja, da Kofur Audu, da Malam Na-Ta'ala, da Ɗantani da Ɗanbayaro da kuma Kyauta Dillaliya suna da nasaba kai tsaye da ci gaban labarin; sannan suna samar da barkwanci da nishaɗin da ake buƙata.

Emma, sangartaccen ɗan gidan Madam Gloria, ya ɓata ɓat, ba wani bayani a kansa. Masu kallo za su so a dinga ambaton sunansa, a nuna har yanzu yana nan. Kamar yadda ake yi wa Malam Ayuba Mai gadi a duk lokacin da aka nuno gidansa.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya tsakanin Kyauta Dillaliya, wacce ta yi haramar farauto zuciyar Kamaye da kuma ƙawarta Adama, tsohuwar matar Kamaye, wacce ta yi auren kisan-wuta da Malam Na-Ta'ala, domin ta dawo wajen Kamaye.

Wannan layi ne

Tasirin Dadin Kowa kan zamantakewar iyali da al'umma

Dadin Kowa

Asalin hoton, Arewa24

Ban da matsin-lamba da magidanta kan fuskanta wajen iyalansu, na su saka musu tauraron ɗan adam mai tashar Arewa24, don su dinga kallon fim ɗin Dadin Kowa, su ma mutane masu injin wutar lantarki na janareta a gidajensu, dole suke haƙuri da masu zuwa kallon fim ɗin Daɗin kowa, idan aka ɗauke wutar lantarki a lokacin nuna shi.

Ana taruwa a kalli fim ɗin Daɗin kowa a wuraren taruwar jama'a kamar wajen mai shayi da shagon aski. Wani lokaci a kan biya kuɗi a kalla a gidan kallon ƙwallo.

Mutane na amfani da sunayen taurarin fim ɗin su siffanta wasu ko ɗabi'unsu. Misali, idan ana son siffanta talaka futuk sai a ce da shi Kamaye. Idan kuma mutum ya cika gulma da gutsiri-tsoma sai a kira shi da Malam Tsalha.

Attajiri ɗan jari-hujja, mai rowa da maƙo ana kiransa Alhaji Buba. Mata, musamman matasa a cikinsu, suna salon ɗaurin ɗankwali da suka yi wa laƙabi da Kyauta Dillaliya, saboda koyi da yadda tauraruwar ke ɗaura ɗankwalinta.

Idan mutum ya kalle shi da idon basira, fim din yana cike da manyan darussa kan rayuwa ta fuskoki daban-daban, imma ga talaka ko mai kuɗi ko ma shugaba.

To amma duk da farin jini da kuma darussan da ke cikin fim ɗin na Dadin Kowa, masu sukar shi na cewa yakan shagaltar da iyali, musamman wasu mata, ta yadda sukan bar wasu daga cikin muhimman ayyukansu domin su kalle shi.

Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙonmu na mako: Umar Yunus, ɗan jarida mai zaman kansa a Jos, babban birnin jihar Filato da ke Najeriya. Dukkan kalaman da ke cikinta, ra'ayinsa ne ba na BBC Hausa ba.

Wannan layi ne