'Yadda gomman samari ke gudun aurena saboda rashin sadakin da zan ba su'

Asalin hoton, Gunjan Tiwari
Biyan sadaki a Indiya, batu ne da dokoki suka haramta tun shekarar 1961, to sai dai dangin amarya kan bayar da kyautar kudi da tufafi, da sarkoki ga dangin ango.
A yanzu, wata matashiya mai shekara 27 da ke tsakiyar birnin Bhopal ta fara wani korafi, inda take bukatar 'yan sanda su rika halartar wuraren daurin aure domin kame mutanen da ke gudanar da wannan laifi da ya saba wa dokokin kasar.
Gunjan Tiwari (ba sunanta na gaskiya ba) ta shaida wa BBC cewa korafin nata ya samo asali ne kan yadda gomman samari suka guje wa aurenta saboda sadaki.
Al'amari na baya-bayan nan, shi ne wanda ya faru cikin watan Fabarairu, lokacin da mahaifinta ya gayyato wani saurayi tare da iyayensa zuwa gidansu domin ganinta.
Bayan iyayenta sun gaisa da bakin, sai Gunjan ta shigo falo rike da faranti dauke da kofunan shayi da sinasir domin karrama bakin nata.
Ta bayyana wannan lokaci da "abin takaici".
"Kowa na kallonka, tare da aunaka da idanunsu," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Gunjan da iyayenta sun shirya wa zuwan bakin, domin kuwa sun tanadar mata kyawawan tufafi na kwalliya da za ta saka domin daukar hankalin bakin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mahaifiyarta ta saya mata koriyar riga, saboda koren tufafin ya fi yi wa 'yar tata kyau, musamman idan ta yi kwalliya.
Ta kuma gargadi Gunjan da kada ta yi dariya a gaban bakin saboda kar su ga hakoranta 'masu rakwasham'
Abu ne da da gunjan ta saba da shi - saboda wannan ne karo na bakwai da ta yi baki irin haka cikin shekaru masu yawa.
Tambayoyin da bakin ke yi mata kusan iri daya ne dangane da matakin iliminta da aiki, sannan za ta iya girki ko ba za ta iya ba?
Kafin shigarta falon ta ji iyayenta na tambayar dangin angon cewa nawa suke ganin za a ba su a matsayin sadakinta?
"Sun ce suna bukatar rupee miliyan biyar zuwa shida kwatantacin dala 61,000 zuwa dala 73,000, (kimanin naira miliyan 47 a kudin Najeriya), a lokacin da mahaifina ya tambaye shi.
Ya kuma yi wa mahaifina barkwancin cewa ''amma idan 'yar taka na da kyau zan yi maka ragi''.
Yayin da tattaunawar tasu ta ci gaba, Gunjan ta fahimci cewa ba za a yi ragin sadakin ba.
Bakin sun tambaye ta game da hakoranta da kuma halittar 'tusar jaki' da ke goshinta.

Asalin hoton, Gunjan Tiwari
Bayan ta ajiye musu shayin, an bai wa Gunjan 'yan mintuna domin ganawa da saurayin a kebence, ta gaya masa cewa ba don sadaki za ta yi aure ba.
"Ya yadda cewa batun karbar sadaki laifi ne," kamar yadda ta shaida wa BBC, ta ce batun ya sanya ta tunanin cewa wannan saurayin ya bambanta da samarinta na baya.
To sai dai daga baya Gunjan da iyayenta sun fahimci cewa dangin ango ba sa bukatar aurenta.
"Mahaifiyata ta dora min laifi saboda yadda nake adawa da batun biyan sadaki. Ta yi fushi da ni, sannan ta daina yi min magana na fiye da mako biyu,'' in ji ta.
Cikin shekara shida da ta wuce, Gunjan ta ce mahaifinta ya tuntubi iyalan samari 100 zuwa 150, sannan kuma ya gana da gommai daga cikinsu.
An kuma gabatar da Gunjan ga shida daga cikinsu. Kuma dukkansu ta ce sun kaurace wa aurenta saboda sadaki.
"Sakamkon guje min da ake yi, duka gwiwowina sun yi sanyi,'' in ji Gunjan, wadda ke da digiri na biyu a fannin lissafi sannan kuma take koyarwa ta intanet.
"Bayan na yi tunani mai zurfi, na fahimci cewa ba ni ce ke da matsala ba, matsalar ita ce yadda samari ke tsananin son sadaki mai gwabi.
''To amma a yanzu sai nake ganin kamar na zame wa iyayena wani karin nauyi''.
Duk da cewa bayarwa da karbar sadaki haramun ne fiye da shekara 60 a Indiya, wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa kashi 90 cikin dari na auren da ake yi a kasar ana biyan sadakin.
Iyayen 'yan mata kan daukar wa kansu dinbin basuka, ko ma su sayar da gonaki da gidajensu a wasu lokuta domin samun kudin da za su biya sadakin 'yarsu, duk kuwa da cewa ba lallai auren ya sanya 'ya'yan nasu cikin farin ciki ba.
Hukumar tattara alkaluman laifuka ta Indiya ta ce amare 33,493 aka kashe a kasar tsakanin shekarar 2017 zuwa 2022, kwatankwaci mata 20 a kowacce rana - sakamakon rashin biyan isasshen sadaki.
Masu gangami na cewa sadaki na daya daga cikin dalilan da ke sa iyayen rashin son haifar 'ya'ya mata.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa juna-biyu 400,000 ake zubarwa a duk shekara, idan aka gano cewa mata ne, saboda fargabar tsadar sadaki da iyayen ke yi.
A lokacin da take gabatar da korafinta gaban Harinarayan Chari Mishra, shugaban 'yan sandan Bhopal, Gunjan ta ce abin da zai magance wannan matsala, shi ne 'yan sanda su rika halartar wuraren daurin aure domin kama mutanen da aka samu da laifin biyan sadaki.
"Tsoron hukunci" zai taimaka "wajen dakatar da wannan mummunar al'ada" in ji ta.
Cikin makon da ya gabata ta gana da Mista Mishra domin neman taimakonsa a yakin da take yi.

Asalin hoton, Gunjan Tiwari
Gunjan ta ce shugaban 'yansandan ya gaya mata cewa "hakika biyan sadaki laifi ne, kuma mu ne za mu kawo karshensa. Na umarci duka ofisoshin 'yan sanda da ke wannan yanki da su taimaki duk matar da ta kai korafinta''.
To amma ya ce''yan sanda suna da iyakar abin da za su iya, ba za su iya kasancewa a kowanne wuri ba to amma muna bukatar wayar da kai game da batun, domin sauya tunani kan lamarin''.
Kavita Srivastava wata mai fafutukar kare 'yancin mata, ta ce 'yan sanda za su taimaka, to amma batun biyan sadaki wani abu ne mai sarkakiya a kasar.
"Indiya ba kasa ce ta mulkin karfa-karfa ba, to mma akwai dokar haramta biyan sadaki, don haka muna son a rika yin aiki da dokar yadda ya kamata''.
Sadaki ba abu ne da ake biya sau daya ba, musamman ga iyayen ango masu kwadayi, wadanda ke ci gaba da neman karin kudin sadaki a hannun iyayen amarya, har ya zuwa bayan aure, domin azurta kansu.
Misis Srivastava ta bayar da misalan matan da suka fuskanci cin zarafi a gidajen aurensu ko ma a sake su saboda kasa biyan abin da iyayen ango suka tambaya na karin sadaki.
Za a iya yakar dabi'ar biyan sadaki ne kadai, idan samari da 'yan mata suka fara kin biya da karbarsa.
Gunjan ta ce tana son yin aure saboda "lokaci na tafiya, kuma ba zan ci gaba da zama haka ba", to amma ta kafe cewa ba za ta biya sadaki ba.
Yayin da lokacin aurenta ke ci gaba da kurewa, iyayenta sun zaku su aurar da ita.
"A kauyenmu na Etawah da ke jihar Uttar Pradesh ana daukar budurwar da ta kai shekarar 25 ba ta yi aure ba a matsayin wadda ta yi kwantai.''
Don haka mahaifinta yake nema mata miji ido rufe, sannan ya gaya wa danginsa da su taimaka masa wajen nema mata mijin aure.
Ya shiga zauren Whatsapp mai dauke da mutum fiye da 2,000 wadanda ke da buri guda irin nasa na sama wa 'yayansu mijin aure.
"Mafiya yawan auren alfarma kan lakume fiye da rupee milyan biyar ko fiye a kasar.
Rabin wadannan kudi ne kawai mahaifina zai iya biya'', in ji ta.
Sannan kuma ta ce matsayin da ta dauka na yin aure ba tare da biyan sadaki ba, ya jefa rayuwar iyayenta cikin mahuwacin hali.
"Mahaifina ya ce ya kwashe shekara shida yana nema min miji.
Ya kuma gaya min cewa ko da zai kai shekara 60 ba zai daina nema min miji ba''.











