Ko kun san su wa da kuma me aka gano a takardun sirri na Epstein?

Hoton Micheal Jackson, da Bill Clinton, da Diana Ross

Asalin hoton, US Department of Justice

Lokacin karatu: Minti 3

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta saki wasu daga cikin takardun bayanai da ke da alaka da mutumin da aka kama da laifuka na lalata Jeffrey Epstein - wanda ya kashe kansa a kurkuku.

Fayil-fayil din sun kunshi dubban takardu da hotuna.

Amma kuma 'yan majalisar jam'iyyar Democrat sun ce sakin wadannan takardu da hotuna bai kai ainahin abin da doka ta bukata ba - ta neman ma'aikatar ta wallafa dukkanin abubuwan da aka fitar zuwa ranar Asabar din nan.

Haka kuma 'yan Democrat din sun nuna fushinsu kan yadda, ba a bayyana komai da ke cikin wasu daga cikin takardu ko hotunan ba - an sakaya wasu sosai.

Ma'aikatar shari'ar ta dangantaka jinkirin fitar da su ga yawansu da kuma bukatar kare sirrin wasu daga cikin wadanda aka ci wa zarafi a badalar.

Wadanda suka tsira daga cin zarafin na Epstein sun zargi gwamnatin Amurka da keta dokar tarayya ta hanyar kasa buga duk abubuwan da ke cikin kundin bayanan a kan lokaci.

Wasu daga cikin kundin bayanan da aka fitar sun hada da na kyamarar tsaro da aka saka a wajen kurkukun da Epstein ya mutu a shekarar 2019 wanda ba wani sabon bayani ne ba ne saboda a kwanakin da suka gabata ne aka fitar da bayanin a bainar jama'a.

Kodayake an samu sababbin bayanai wadanda suka hada da wani hoton tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton yana ninkaya da daddare tare da Ghislaine Maxwell.

Akwai kuma wani hoton na Mista Clinton a cikin abin da ya yi kama da bahon wanka kusa da wani mutum da aka rufe fuskarsa.

Mista Clinton ya sha musanta aikata ba dai dai ba

Haka kuma takardun sun kunshi hotunan mariyagi Micheal Jackson - mawakin pop da Diana Ross da Mick Jagger wadanda suma fitattun mawaka ne

Akwa kuma hoton tsohon yarima Ingila watau Duke of York wanda yanzu ake kira Andrew Mountbatten

Kasancewar wadannan mutane a cikin hotunan ba wai yana nufin sun aikata laifi ba ne.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai sakin wani bangare na kundin bayanan Epstein ya karfafa zarge-zargen yin rufa-rufa domin kare masu hannu da shuni da kuma masu karfin fada-da-a-ji.

An rika samun kiraye-kirayen tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin da 'yan majalisun dokokin tarraya suka zartar da kudurin wanda Shugaba Trump ya sanya wa hannu.

Dokar ta ba ma'aikar sharia damar rike wasu bayanai da suka shafi binciken da ya gudana a halin yanzu da kuma bayanan da suka shafi cin zarafi ta hanyar lalata.

Maikatar shari'ar ta ce tana rike da wasu bayanai sai dai wannan matakin ya ba ta wa wasu rai, Marina Lacerda wadda shekararta 14 a lokacin da Jefrrey Epstein ya ci zarafinta ta hanyar lalata ta kuma nuna rashin jin dadinta.

Ta ce: ''Mun rika jiran wannan rana, da wannan lokacin. Ba mu ji dadi ba a kan yadda suke dagewa da wasu abubuwa da kuma yadda suke raba mana hankali da wasu abubuwa. Wasu daga cikin wadanda al'amarin ya shafa sun nuna shakku a kan yadda za su saki sauran bayanan .

Ma'aikatar shari'ar Amurka dai ta ce za ta ci gaba da aiki kan sauran bayanan da ke hannunta kuma za ta saki karin takardu a kwanaki masu zuwa.