Dalilan da suka sa dala ke rasa ƙimarta a duniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Julia Braun
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, De BBC News Brésil à Londres
- Lokacin karatu: Minti 8
A watanni shidan farko na shekarar 2025 ne kuɗin Amurka dala ya fuskanci mummunan koma-baya cikin fiye da shekaru 50 a ma'aunin da aka yi amfani da shi wajen duba ƙarfin kuɗin na Amurka.
Jumullar faɗuwar darajar kuɗin cikin watan Yuni ya kai kashi 11 cikin 100 a duniya wanda babban bankin Amurka ya samar kuma ya kwatanta dalar ta Amurka da wasu kuɗaɗen ƙasashe shida - Yuro da Yen da fan da dalar Canada da Krona na Sweden da kuma Swiss Franc.
An taɓa ganin irin wannan koma-bayan. Amma a wannan karon, faduwar darajar kuɗin ta zo ne a daidai lokacin da ake samun faruwar wasu lamura da ke zama abin damuwa ga masana tattalin arziki, lamarin da ke ƙara ɗisa ayar tambaya kan ƙarfin darajar ta dalar Amurka, a cewar wasu majiyoyi.
Daga cikin abubuwan damuwar da aka bayyana shi ne raguwar hannun jarin kuɗaɗe da ake gani a asusun ajiyar kuɗaɗen waje na manyan bankunan da ke faɗin duniya.
Manufofin haraji na gwamnatin Shugaba Donald Trump - da kuma raɗe-raɗin da ake game da yiwuwar raunana darajar kuɗin da gayya daga Fadar White House domin farfaɗo da masana'antun Amurka - suma sun janyo jita-jita
Amma yayin da wasu ke nuna damuwa, wasu kuwa suna ɗari-ɗari ne game da yanayin kasuwar ko ma ƙarfin kuɗaɗen wasu ƙasashen na kai wa matsayin da dalar Amurka ta kai.
Dalar Amurka ta zama kuɗin da ake amfani da shi a duniya bayan yaƙin duniya na biyu disa yarjejeniyar Bretton Woods.
Tun lokacin kuma, kuɗin ya zama wanda aka fi hada-hada da shi a duniya musamman a tsarin hada-hada na Swift da ke haɗa cibiyoyin kuɗi 11,000 da ke sama da ƙasashe 200.
To ya batun ƙaruwar rashin yarda da kuɗin da ya mamaye kasuwancin duniya? Kuma me waɗanda suka yi hasashen cewa dala za ta daɗe tana babakere a duniya suke cewa?

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa dala ta fara rasa karsashinta?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙaƙaba sabbin takunkumai da gwamnatin Amurka ta yi ba shi ne kawai dalilin da ya sa ƙwararru suka ce ya shafe tsaron da dala ke da shi.
Yadda gwamnatin Amurka ke amfani da kuɗin a matsayin hanyar ladabtar da masu kaucewa doka da oda ta hanyar ƙaƙaba takunkumi kan tattalin arziki, shi ne muhimmin dalilin da ya sa kuɗin ya fara rasa ƙwarin gwiwa daga wajen masu zuba jari, in ji Robert McCauley daga Jami'ar Boston wanda ya shafe galibin shekarun aikinsa a cibiyar kuɗi ta manyan bankunan ƙasashen duniya da kuma babban bankin New York.
Wataƙila a tsame ƙasashe da kamfanoni da bankuna ko ma ɗaiɗaikun jama'a da Amurka ta lafta wa takunkumi daga tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa amma ya danganta da matakin takunkumin.
Wannan ne abin da ya faru da Rasha, misali, bayan da ta mamaye Ukraine. Ko alƙalin Kotun Ƙoli Alexandre de Moraes, wanda aka zarga da take haƙƙoƙin bil adama da rashawa, sakamakon rikicin siyasa da Amurka.
A cewar manazarcin na jami'ar Boston, irin waɗannan matakan na iya ƙarfafa wa wasu gwiwa wajen yin ƙoƙarin karkatar da dala domin kaucewa samun kansu cikin irin wannan yanayin wata rana.

Asalin hoton, Getty Images
Wani dalilin da aka yi magana a kai shi ne ƙaruwar kuɗaɗen da gwamnatocin ƙasashe masu tasowa ke kashewa a shekara wanda bai kai kuɗaɗen da suke samu daga haraji ba a shekarun baya-bayan nan.
A ɓangaren Amurka, ƙasar ta ƙare shekarar 2024 da dala triliyan 35.46 na kuɗaɗen da gwamnati ke bin kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane, adadin da ya kai kashi 123 cikin 100 na arzikin da ƙasa ke samarwa, a cewar Baitul Malin Amurka.
A cewar Luis Oganes, masu hannun jari na fargabar cewa nan gaba, kuɗin zai shiga matsin durƙusar da darajar dala domin rage ko ma magance matsalar da za ta sa ƙasa ta fi kashe kuɗi wajen shigo da kayayyaki a kan abin da take samu daga kayayyakin da take fitarwa. Wasu masana tattalin arziki na ganin hakan zai sa kayayyakin da Amurka ke fitarwa su fuskanci gogayya saboda farashinsu zai fi arha ga masu saye daga wasu ƙasashen.
Mai binciken na bankin JP Morgan ya nuna cewa ana sa ran babban bankin Amurka zai sanar da ƙara rage kuɗin ruwa a watanni masu zuwa, wanda ka iya rage wa dala karsashi a wajen masu hannun jari.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ƙungiyar BRICS da rage amfani da dalar Amurka
Wasu na ganin cewa yin baya-baya wajen amfani da dala ya rigayi akasarin takunkumai ko haraje-harajen da aka lafta wa asashe da ma illolinsu.
"Ya soma ne a 2008 da 2009, lokacin da wata matsalar kuɗi da ta samo asali daga Amurka ta janyo tattalin arzikin duniya ya ɗan karaya kuma tun lokacin, ƙasashen da suka cigaba suka fuskanci cikas a tattalin arzikinsu," in ji Fernanda Brandao na Mackenzie.
"Matsalar na da muhimmanci saboda ta bayyana ko kuma nuna illolin da ke da alaƙa da yawan dogaro kan dala a matsayin kuɗin da ake hada-hada da shi a faɗin duniya."
A cewar Brandao, bayan nan, idon ƙasashen duniyar ya ƙara buɗewa cewa duk wani sauyi a manufofin tattalin arzikin Amurka da babban bankin ƙasa da Fadar White House suka aiwatar na iya haifar da matsalolin da za su shafi tattalin arzikin wasu."

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
A yanzu, ana ganin ƙungiyar tattalin arziƙi ta BRICS na kan gaba a wannan tafiya. Sai dai a baya-bayan nan, ƙungiyar da ta haɗa da Brazil da Rasha da Indiya da China da Afirka ta Kudu ta ƙara samun sabbin mambobi goma tun 2024.
Ga Fernanda Brandão, ganin yadda ƙasashe masu tasowa suka fuskanci ƙalubalen tattalin arziki a 2008, duk da cewa matsalar ta soma ne daga Amurka, ya sa BRICS ta rungumi tsarin rage dogaro kan dala tun da aka ƙirƙiri ƙungiyar.
"Tun daga lokacin, sai ta bayyana ƙarara cewa akwai illa a yawan dogaro da dala," in ji Brandão.
Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana burinsa na rage yawan amfani da dala a cinikayyar ƙasashen duniya a taron ƙarshe na BRICS da aka yi a Rio de Janeiro cikin watan Yuli.
"Ina tunanin akwai buƙatar ƙasashen duniya su bijiro da wata hanya ta tabbatar da alakar cinikayya ba ta dogaro kan dala ba. A Amurka, ana amfani da dala. Amma a Argentina ko China, ba lalle ba ne. Babu wanda zuwa yanzu ya yanke cewa dala ce karɓaɓɓiya. A wane taro aka yanke hakan? kamar yadda Lula ya tambaya.
Shugaban na Brazil ya kuma ce maye gurbin dala a cinikayyar ƙasa da ƙasa abu ne da "ba za a iya sauyawa ba."
Ƙasashen BRICS tuni suka faɗaɗa yin amfani da kuɗaɗen ƙasashensu musamman China, wajen gudamnar da harkokin kasuwanci na cikin gida. Rasha, a nata ɓangaren, tana neman ta samar da wani tsarin hada-hadar kuɗi domin rage tasirin takunkumin da ƙasashe ke ƙaƙabawa.
Ƙungiyar tana kuma tattauna hanyoyin samar da nata kuɗin. Ba a yi wata sanarwa ba zuwa yanzu, amma gwamnatin Amurka tuni ta fahimci akwai barazana a waɗannan batutuwan.
Trump, a baya, ya ayyana cewa ƙungiyar a matsayin "hari kan dala" inda ya yi amfani da kasancewar Indiya cikin ƙungiyar a matsayin dalilin ƙaƙaba ƙarin haraje-haraje kan kayayyakin da ƙasar ke fitarwa zuwa Amurka.
"Suna da BRICS, wadda ƙungiya ce da ke adawa da ƙasashen Amurka," in ji Shugaban Amurka a ƙarshen watan Yuli. "Wannan hari ne kan dala, kuma ba za mu ƙyale kowa ya far wa dala ba."
Me Trump ya shirya?
A gwamnatin Trump, akwai ra'ayoyi mabambanta kan ma'anar kaka-gidan da dala ta yi ga buƙatun Amurka na siyasa, in ji masu sharhi.
Wata doka da aka zartar a Amurka a watan Yuli, wadda ke sa ido kan kuɗin intanet idan aka kwatanta da dala, da alama yana biyan buƙata.
An tsara waɗannan kuɗaɗen intanet ɗin domin tabbatar da daidaito da dala. Kan haka ne, wasu masana tattalin arziki suke ganin za su iya ƙarfafa kaka-gidan da kuɗin Amurka ya yi a tsarin hada-hadar kudi ta duniya.
A wani ɓangaren kuma, manufofinsa kan haraji na ƙara raunana ƙarfin dala, a cewar Fernanda Brandão na Mackenzie.
Kafafen yaɗa labarai da kasuwannin hada-hadar kuɗi na jita-jitar hakan na iya zama manufarsu, bayan furucin da White House ta yi cewa ƙarfin dalar Amurka na iya kawo cikas ga masana'antun Amurka, kamar yadda aka bayyana a wata muƙala da cibiyar Atlantic Council ta wallafa.
A cewar wasu masana, ƙaruwar neman dala na ƙara darajarsu, abin da ke sa kayayyakin da aka sarrafa a Amurka ke ƙara tsada, hakan kuma na ƙarfafa wa masu ƙera abubuwa su koma yinsu daga ƙasashen waje, abin da kuma zai illata ayyukan yi a ƙasar.
Wasu mashawartan Trump sun bayyana cewa idan darajar dala ta yi rauni kuma, hakan zai sa kayayyakin da Amurkar ke fitarwa su fuskanci ƙarin gogayya a ƙasashen duniya saboda za su yi arha ga masu saye daga wasu ƙasashen. Sannan kuma farashin kayayyakin da ake shigar da su Amrka zai tashi.
"Trump ba ya son dala ta yi ƙarfi saboda za ta ƙara kayayyakin da ake shigar da su ƙasar." in ji Gabriela Siller, daraktar nazari kan tattalin arziki a kungiyar BASE.

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu dala na da daraja
Wasu abubuwa da suka faru a baya-bayan nan ba sa nuna alamar kawo ƙarshen darajar dalar Amurka, in ji masana.
Wasu masanan da sashen BBC na Brasil ya tuntuɓa na ganin har yanzu ba a kai ga zuwan durƙushewar dala ba.
Duk da cikas ɗin da ake gani a wasu ɓangarorin, dala na ci gaba da babakere a cinikayya tsakanin ƙasashe. Kuma a cewar akasarin masu sharhi, babu kuɗin wata ƙasa da a yanzu zai iya maye gurbinta.
Ko kuɗin China, wanda ke samun karɓuwa kuma manyan bankunan ƙasashe da dama ke amfani da shi asusun ajiyar kuɗaɗen waje, bai yi ƙarfin da zai maye gurbin kuɗin Amurka ba, in ji ƙwararru.
Wasu na ganin ko da ƙasashe irin su Rasha da China, waɗanda ke tallata manufar rage yawan amfani da dalar Amurka, suna fuskantar kalubale wajen daina amfani da dalar Amurkar.
Robert McCauley ya yi mamakin jan ƙafar da ake yi wajen rage yawan dogaro kan dala a Rasha duk da burin gwamnati shi ne ta yi hakan.
Ya bayyana cewa "ina tunanin hakan na faruwa ne saboda abu ne mai sauƙi aiya karkatar da ra'ayin kamfanoni masu zaman kansu su daina amfani da dala a matsayin hanyar ba da rance da kuma hada-hada."










