Abin da ɓangarori huɗu ke buƙata a tattaunawar da za a yi a White House

Hotunan Trump da Zalensky - Trump na sanye da shuɗiyar kwat da jar lakataye yayin da Zelensky ke sanye da baƙar kwat da ƙaramar baƙar riga a ciki

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Laura Gozzi and Tom Geoghegan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Taron shugabannin ƙasashen Turai da na Ukraine da za a yi a fadar shugaban Amurka na iya zama ranar da ba a taɓa ganin irinta ba a fadar White House, lokacin taron da ba kasafai ake irinsa ba domin tattaunawa kan Ukraine.

Abin da a baya ake yi wa kallon taro tsakanin shugabannin ƙasa biyu, Donald Trump da Volodymyr Zelensky, yanzu ya zama gagarumin taron shugabannin ƙasashen duniya.

Shugabannin ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya da Finland da Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar tsaro ta NATO sun ƙetare tekun Atlantika domin bayyana ra'ayoyinsu kan yadda ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin da aka kwashe shekara uku ana yi da Rasha da kuma sharuɗɗan da za su tabbatar da hakan.

Hakan na nuni ne da irin girman muradun da ake son a cimma da kuma ƙaruwar fargaba da ƙasashen Turai ke samu na cewa Amurka ta karkata akalarta zuwa kan wasu manufofi da ba za su iya taimaka wa Ukraine ba.

Mun yi fashin baƙi a kan abin da kowane ɓangare da kowa zai ɗauka a matsayin nasara lokacin da aka kammala tattaunawar.

Amurka - A yi yarjejeniya, ko ma wace iri ce

Alƙawarin da Trump ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe shi ne warware wannan rikici a ranar farko da ya hau karagar mulki, amma bayan watanni shida haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

Sharuɗɗan kowace yarjejeniya sun kasance kamar ba su da mahimmanci ga Trump idan aka kwatanta da yarjejeniyar ita kanta, don haka an samu sauyi a sharuɗɗan bayan wani lokaci.

Tun bayan ganawarsa da shugaban Rasha, Vladimir Putin a Alaska a ranar Juma'a, Trump ya yi watsi da sukar da ya yi wa Moscow da kuma barazanar ƙakaba ma ta takunkumi, kuma ya yanke shawarar ƙarin matsin lamba kan Zelensky.

A cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta a daren Lahadi, ya gargaɗi shugaban na Ukraine cewa dole ne ya yi watsi da fatan zama memba a ƙungiyar tsaro ta NATO, kuma dole ne ya haƙura da yankin Crimea, wanda Putin ya mamaye ba bisa ƙa'ida ba a shekarar 2014.

Wakilin Trump na musamman, Steve Witkoff ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa Washington za ta ba da tabbacin tsaro ga ƙasashen Turai da nufin daƙile duk wani mamayar da Rasha za ta iya yi nan gaba.

Amma ba a yi cikakken bayani kan yadda za a cimma hakan ba.

Zuwa yanzu, Amurka na ci gaba da yin watsi buƙatun ƙasahsen Turai da ta amince da tabbatar da tsaron Ukraine a nan gaba.

A yanzu kallo ya koma kan Fadar White House don ganin ko da gaske ta sauya matsaya kan wannan lamarin.

Ukraine - Ci gaba da riƙe yankunanta

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban Ukraine Volodymir Zelensky ya tsinci kansa a cikin wani mummunan yanayi na tsayawa tsayin daka domin fuskantar rashin hakurin Donald Trump, wanda alamu ke nuna cewa Putin ya shawo kansa.

Tuni dai har Trump ya fara zargin Zelensky da kawo cikas a yunƙurin da ake yi na samar da zaman lafiya.

Wataƙila Trump zai shaida wa Zelensky cewa dole ne ya amince ya haƙura da wasu yankunan ƙasarsa.

Wannan zai yi matuƙar wahala ga shugaban na Ukraine ya miƙa wuya domin hakan zai ƙunshi sallamar da Donetsk da Luhansk, yankunan da dubban sojojin Ukraine suka yi yaƙi kuma suka sadaukar da rayukansu domin karewa tun shekara ta 2022.

Har ila yau, zai bai wa Rasha damar samun iko da yankuna masu yawa da za ta iya amfani da su daga baya a matsayin sabbin cibiyoyin ƙaddamar da hare-hare.

Don haka Zelensky ba zai iya amincewa ya haƙura da wasu yankunan ƙasarsa ba tare da ya samu tabbacin ingatattun mataƙan tsaron da za su fara aiki idan Rasha ta sake kai wani harin.

Ƙungiyar tsaro ta NATO na iya samar da waɗannan, amma Trump ya bayyana ƙarara cewa Ukraine ba za ta shiga cikin ƙungiyar ba.

Akwai yiwuwar cewa har yanzu ba a fayyace wasu tsare-tsaren tabbatar da tsaro ba, kuma idan har ba a samu hakan ba, zai yi wahala Zelensky ya amince da duk wani abin da zai sa ya miƙa wasu yankunan ƙasarsa.

Har ila yau Ukraine ta damu da yadda Trump ya koma daga neman tabbatar da tsagaita wuta zuwa matsa ƙaimi domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Wannan na iya ɗaukar dogon lokaci, wanda hakan zai bai wa Rasha damar ci gaba da kai hare-haren da za su sanadiyyar mutuwar fararen hula.

Turai - Samun tabbacin tsaron Ukraine

Shugabannin ƙassahen Turai za su yi ƙoƙarin matsa wa Trump lamba kan ya bayyana irin tabbacin tsaron da Amurka za ta bai wa Ukraine.

Yanayin rashin tabbas na kalaman Amurka game da lamarin na matuƙar tayar wa ƙasashen Turai hankali inda su ke ganin tabbacin samun kariya daga Amurka ne kaɗai zai iya kawar da duk wani yunƙurin hari da Rasha za ta iya kai wa nan gaba.

Akwai kuma tashin hankali game da ra'ayin cewa Amurka na iya matsa wa Ukraine ta hakura da wasu yakunanta.

Nahiyar Turai dai na da daɗaɗɗen tarihin yaƙe-yaƙe kuma shugabanni na son kauce wa yanayin da zai tilasta a sake fayyace iyakokin wata ƙasa mai cin gashin kanta.

Wannan damuwar da ake da ita ta sanya dole aka ɗauki matakin da ba a taɓa ganin irinsa ba na gudanar da irin wannan babban taron gaggawa na shugabanni a fadar White House.

A makon da ya gabata, Akwai alamun cewa taron Amurka da Tarayyar Turai da aka yi gabannin taron na Alaska ya yi tasiri wajen ƙara zafafa sukar da Trump ke yi wa Rasha.

Yanzu da ake ganin ya sake karkata zuwa ɓangaren Moscow, shugabannin ƙasashen Turai za su yi ƙoƙarin nuna masa damuwarsu game da tsaron nahiyar na dogon zango bai sauya ba.

Rasha - Ƙara mamaye yankunan Ukraine

Ba za a samu wani wakilin Rasha a fadar White House a taron na yau ba.

Ba lallai ne hakan ya yi wani tasiri ba.

Alamu na nuna cewa Putin ya shawo kan Trump a ganawarsu ta makon da ya gabata da Moscow za ta iya samun ƙwarin giwiwar cewa za a kare mata muradun ta.

Trump ya riga ya yi iƙirarin cewa Ukraine ba za ta shiga ƙungiyar NATO ba - kuma Rasha ta na buƙatar a tabbatar da cewa hakan bai faru ba.

Ta na kuma son cikakken iko da yankin Donbas, wanda hakan zai tilasta wa Ukraine haƙura da yankunan da ta ke riƙe da su a Donetsk da Luhansk.

Wataƙila abu mafi mahimmanci shi ne Moscow ta yi nasarar sanya wa Trump tunanin cewa a yanzu ya rage ga Zelensky ne ya tabbatar da yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin - yayin da ya sani sarai ba zai iya yarda da miƙa iko da yankunan ƙasarsa kai-tsaye ba.

Nasarar da Rasha za ta buƙaci samu ita ce wannan taƙaddamar ta kai ga Trump ya fice daga kan teburin sulhu ya kuma bar Ukraine da sauran ƙasashen Turai su yi ta kan su.