Yadda Isra'ila ke hana ƙungiyoyi shigar da agaji Gaza

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyoyin agaji fiye da 100 sun ce har yanzu Isra'ila na ci gaba da hana su shigar da kayan agaji cikin Gaza.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, ƙungiyoyin Oxfam da Save the Children da Care da kuma MSF sun ce ƙa'idojin da Isra'ila ke sanyawa na neman rikiɗewa zuwa haramcin kai agaji Gaza baki ɗaya, duk da cewa sun tattara ɗimbin kayan tallafin da suke fatan rabawa jama'ar da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Ƙungiyoyin agaji da dama sun ce tun daga watan Maris da Isra'ila ta fara ɗaukar matakin hana shigar da kayan agaji Gaza, kawo yanzu ko terela ɗaya ta kayan agaji ba su samu ikon shigarwa ba.
Ƙungiyoyin sun ce ko alƙawarin baya-bayan nan da aka yi na bayar da damar shigar da kayan agaji Zirin Gaza bai canza mummunan halin da ake ciki ba.
Oxfam ta ce tana da ɗimbin kayan tallafi da suka haɗa da abinci da saura kayan buƙatun yau da kullum da ta ke jiran izini kafin shigar da su Gaza.
Ita ma ƙungiyar Care ta ce tana da kayan rabawa mata da ƙananan yara masu yawan gaske da ke jiran a tantance kafin ta shigar da su Gaza. Ta bayyana cewa yanzu haka kayan sun shiga wata na biyar ba tare da an basu damar shiga da rabawa masu buƙata ba.
Sun dai yi zargin cewa wannan matakin farko ne na wani shiri na hana ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa gudanar da ayyukan jin ƙai a Gaza.
Chris Lockyear jami'I ne a ƙungiyar MSF.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce: ''Taƙaita kai agaji ya zarce batun shigar da kayyaki cikin Zirin Gaza kaɗai, a'a, ya kuma ƙunshi samun ƴanci da goyon bayan doka da kuma tabbacin tsaro domin gudanar da ayyukanmu. Taƙaita kai agaji abu ne mai zuwa ta fuskoki da dama, don haka ko ganin ana shigar da motoci ɗauke da kaya a ciki ba ya tabbatar da cewa ana bari a shigar da tallafi ga mabuƙata.''
Isra'ila ta bullo da wani sabon salo na tantance masu shigar da agaji Zirin Gaza kuma daga cikin bayanan da suke tambaya harda zurfafa bincike kan ma'aikatan ƙungiyoyin agaji na duk wata ƙungiya da ke shirin shigar da kayan tallafi cikin Gaza.
Duk wata ƙungiya da bata bayar da haɗin kai ga wannan bincike ba tana rasa damar shiga domin gudanar da ayyukanta a Gaza.
A cikin watan Yuli kaɗai, Isra'ila ta hana ƙungiyoyi fiye da 60 damar shigar da kayan agaji ga jama'ar da ke tsananin buƙata a Zirin Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila dai ta sha musanta zargin cewa ta na hana shigar da kayan agaji Gaza.














