Wane ne ke da haƙƙin mallakar Gaza?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Ethar Shalaby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Lokacin karatu: Minti 8
A ranar Talata,Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na ƙwace ikon Zirin Gaza kuma ya ce ƙasarsa '' za tayi abin da ya dace kan shi''.
Shirin nasa ya haɗa da sake gina zirin da kuma mayar da shi '' ƙayataccen wuri a Gabas ta tsakiya''.
Hakan na zuwa ne bayan a farko ya bada shawarar mayar da falasɗinawa Masar da Jordan na din-din-din.
Trump ya fadi hakan ne bayan ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a fadar White House, inda Netanyahu ya bayyana shawarar a matsayin 'wanda ya kai a mayar da hankali kanshi'' inda ya ƙara da cewa ''irin wannan tunanin ne zai sake fasalin Gabas ta Tsakiya ya kuma kawo zaman lafiya.''
Jim kaɗan bayan Trump yayi waɗannan kalamai, shugabannin duniya suka yi tir da kalaman nasa ciki harda Firaministan Birtaniya Keir Starmer, kuma aka fara ɗiga ayar tambaya kan ko waɗannan kalamai za su sake tada rikici a zirin da kuma tekun Bahar rum.
Wane ne ke iko da Gaza a yanzu?
Tun shekarar 2007, Hamas ta kasance wadda ta ke jagorantar yankin. Ta lashe zaɓen ƴan majalisu a yankunan da aka mamaye a shekarar 2006, kuma ta sake dawo da ikon ta a Gaza bayan korar abokin hamayyarsu Fatah daga zirin.
Ƙungiyar - wadda Isra'ila da Amurka da wasu ƙasashen yamma ke wa kallon na ƴan ta'adda- ita ke jagorantar zirin.
Zirin wani yanki ne da ƙasashen Ira'ila da Masar da kuma Bahar rum ke kewaye da shi, wanda ke da tsawon kilomita 41 da kuma faɗin kilomita 10.
A shekarun da suka biyo, Hamas da Isra'ila sun gwabza munana yaƙi da dama Ko wane yaƙin na kaiwa ga asarar rayuka a ɓangarorin biyu, akasarinsu Falasdinawan da ke Gaza ne.
A ranar 7 ga watan Oktoban 2023, mayakan Hamas sun ƙaddamar da wani hari daga Gaza wanda ya hallaka Isra'ilawa aƙalla 1,200 suka kuma yi garkuwa da mutane fiye da 250.
Harin ya kai ga hare haren martani daga sojojin Isra'ila a Gaza wanda aka shafe watanni 15 ana kaiwa.
Mutane fiye da 47,540 aka kashe, yawancin su mata da yara, a cewar hukumar lafiya da Hamas ke jagoranta.
A Janairun 2025, Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta - bayan shafe watanni ana tattaunawar bayan fage - domin dakatar da yaƙin.
Ana sa ran yarjejeniyar zata kawo ƙarshen yaƙin da kuma sako mutanen da Hamas ke riƙe da su a Gaza domin musayarsu da fursunoni falasɗinawa da Israila ke rike da su.

Asalin hoton, Reuters
Shin Trump zai iya ƙwace iko da Zirin Gaza?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Har yanzu ba a yi cikakken bayani kan yadda Trump ke shirin ƙwace Gaza ba.
Sai dai kalaman nashi sun sha suka a faɗin duniya, inda ƙasashen da dama kamar su Birtaniya da Faransa da Jamus da Brazil da Australia da Rasha da China sukayi Alla'wadai da shirin.
A yankin ƙasashen Gulf, Saudiyya ta yi watsi da duk wani yunƙuri na korar Falasɗinawa inda ta ce matsayinta 'a bayyana take'. ƙasashen Jordan da Masar ma sun fito fili sun bayyana rashin amincewarsu da ''raba falasɗinawa da muhallansu''.
A ƙarƙashin dokokin duniya, an haramta duk wani yunƙurin sauya wa wasu wuri ta hanyar tilastawa, kuma Falasɗinawa da ma ƙasashen larabawa za su kalli wannan yunƙuri a matsayin shirin kora da kuma kawar da Falasɗinawa daga ƙasarsu.
Gabanin lashe zaɓe da Trump ya yi, shiga rikicin ƙasashen waje bai kasance abu mai muhimmanci gareshi ba. Tattalin arziƙi da baƙin haure su ne manyan batutuwan da suka shafi magoya bayanshi. Bayanai sun nuna cewa kafin zaɓen shugaban ƙasa, Amurkawa sun buƙaci gwamnatin da za ta hau mulki ta mayar da hankali kan tsadar rayuwa.
Ba a tabbatar ba ko za a buƙaci aika sojojin Amurka domin ƙwace ikon Gazan.
Da aka tambayeshi ko za a aika sojoji, Mista trump ya ce '' za mu yi duk abin da ake buƙata''.
Bisa doka, akwai buƙatar sai ƴan majalisun Amurka sun amince kafin za ayi amfani da ƙarfin soji.
A yanzu haka majalisar mai ɓangarori biyu, ƴan jamiyyar Repubican ne ke da rinjaye.
Hassan Mneimneh, farfesa a makarantar Gabas ta tsakiya da ke Washington ya shaidawa BBC cewa '' Ba sai Trump ya damu da majalisa ba saboda yanada goyon baya mai ƙarfi daga wurinsu''.
Trump bai yi magana kan kashe maƙudan kuɗi wajen sake gina gaza ba, a cewar Mneimneh, wanda ya ke ganin Trump na da nufin amfani da kuɗi daga ƙasashen larabawa domin sake gina Gaza da Gaɓar Yamma.

Wane ne asalin wanda ya mallaki Zirin Gaza a tarihi?
Gabanin kafa Isra'ila a shekarar 1948, Gaza na ƙarƙashin mulkin mullakan Birtaniya. Rana guda bayan Isra'ila ta ayyana ƴancinta, sojojin ƙasashen Larabawa biyar su kai mata hari tare da kewayeta.
A lokacin da yaƙin ya zo ƙarshe a 1949, Isra'ila ce ke da iko da yankuna da dama, kuma yarjejeniyar da akayi ya kai ga Masar ta mamaye zirin Gaza, Jordan ta mamaye Gaɓar yamma da gabashin birnin ƙudus, yayin da Isra'ila kuwa ta mamaye yammacin birnin Ƙudus.
An kori Masar daga Gaza a yaƙin 1967 kuma Isra'ila ta mamaye zirin wadda ta gina matsugunai ta kuma sanya Falasɗinawan Gaza ƙarƙashin mulkin soji.
A 2005, Isra'ila ta janye dakarunta da mutanen da ke matsugunan daga Gaza, duk da dai ta cigaba da iko da iyakokinta, da sararin samaniya da bakin teku, wanda ya bata damar lura da hada hadar mutane da kayyayaki.
Majalisar ɗinkun duniya na cigaba da kallon Gaza a matsayin yankin da ke ƙarƙashin mamayar Isra'ila saboda irin ikon da Isra'ila ke da shi kansu.
Hamas ta lashe zaɓen 2006, kuma ta kori abokan hamayyarta daga yankin bayan mummunar yaƙi a 2007.
Isra'ila da Masar sun tattare kan iyakokin a matsayin martani, inda isra'ila ke lura da akasarin abubuwan da ake bari su shigo yankin.
A shekarun da suka biyo, Hamas da isra'ila sun gwabza munanan yaƙi daban-daban - ciki har da wanda sukayi a shekarun 2008-2009, sai na 2012 da kuma 2014.
Wani babban rikici tsakanin ɓangarorin biyu a Mayun 2021 ya zo ƙarshe da matakin tsagaita wuta bayan kwanaki 11.

Asalin hoton, Reuters
Shin akwai albarkatun mai da iskar gas a Gaza?
A cewar MDD, alamu na nuna cewa akwai albarkatun mai da iskar gas danƙare a yankunan Falasɗinawa waɗanda har yanzu ba a fara ma haƙo su ba.
A shekarar 2019, wani rahoto da ƙungiyar cinikayya da cigaba na MDD (UNCTAD) ta fitar ya nuna bisa ƙiyasa, akwai gangar mai biliyan 3 a yankin.
Masana ilimin ƙasa da masana tattalin arziƙin albarkatun ƙasa sun tabbatar da cewa akwai ɗimbim albarkatun mai da iskar gas da ke yankunan Falasɗinawa da aka mamaye, a yankin 'C" na gaɓar yamma da gaɓar tekun bahar rum a gefen zirin Gaza,'' in ji rahoton.
Wannan na nuni ga yadda aka gano arziƙin ɗanyen mai da gas a yankin Levant, wanda ke cikin tekun meditaraniya, wanda ya kai tiriliyan 122 na ma'unin iskar gas na cubic, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 453 (A shekarar 2017) da kuma ganga biliyan 1.7 na ɗanyen man fetur wanda ƙimarsa ta kai kimanin dala biliyan 71.
Wasu ƙwararru na ganin cewa akwai yiwuwar shirin Trump na da alaƙa da haƙo albarkatun mai da iskar gas. Sai dai wasu na ganin cewa nuna sha'awarsa kan Gaza siyasa ce ba don tattalin arziƙi ba.
Laury Haytayan, ƙwararriya kan makamashi da ke da sha'awa ta musamman kan makamashi a gabas ta tsakiya, ta shaidawa BBC cewa an gano mai da iskar gas a filayen kusa da teku da ke Gaza a shekarun 2000 kuma anyi ta tattaunawa kan yadda za a bunƙasa fannin.
Ta ce wannan 'zai iya zama ɗaya daga cikin dalilan' da Trump ke da su a lokacin da yake bayar da shawarar ƙwace ikon Gaza, amma ba shi kaɗai bane dalilin shi ba.
''Akwai babban aiki da za ayi domin gano yawan mai da iskar gas da ke Gaza, kuma ya kamata mu rage tsammanin mu,'' in ji ta.
Maher Tabaa, wani masanin tattalin arziƙi daga Gaza, ya ce '' Trump na da wasu ƙasashen da suka fi Gaza albarkatun mai da gas. Siyasa ce babbar dalilin da ke sa shi mayar da hankali kan Gaza''.
Da yake magana da BBC, tsohon jakadan Amurka a Isra'ila ya ce Donald Trump yana kallon rikicin da ke Gaza kamar ''matsala ce kawai ta gina gidaje''.
Dennis Ross ya ce: '' a ganina kamar abin da yake nufi shi ne: 'Za mu sake gina yankin da tun a baya yake fama da matsanancin talauci.'
Me Falasɗinawa ke cewa game da kalaman Trump?
Falasɗinawa na kallon shawarar Trump ɗin a matsayin korar su daga ƙasarsu.
Shugaban yankin falasɗinawa Mahmoud Abbas ya yi watsi da duk wani shiri na korar Falasɗinawa daga Gaza, inda ya bayyana shirin Trump a matsayin ' keta dokokin duniya'.
Ya ce: ''ba zamu amince da duk wanu yunƙuri na take haƙƙin mutanen mu ba, wanda mu ka sha gwagwarmaya na gwamman shekaru kuma muka sadaukar domin samun shi''.
Shugaban tawagar Falasɗinawa a MDD Riyad Mansour ya ce ya kamata a bar falasɗinawa su maido da abin da yake a baya gidajensu '' ga waɗanda suke so su mayar da falasɗinawa zuwa ''wuri ma kyau'', ku bar su su koma gidajensu na ainihi a wurin da a yanzu Isra'ila ne.
A zirin, Falasɗinawa na kallon wannan shiri a matsayin matakin azabtarwa.
Mahmoud Almasry, ɗan shekaru 43 a Gaza, ya shaidawa BBC cewa babu ko mutum ɗaya a Gaza da ya amince da abin da Trump ya ce. '' Ko da za mu zauna cikin ɓaraguzan gine gine, ba za mu taɓa barin gidajenmu ba. Shin Trump zai so wani ya ce wa Amurkawa su bar Amurka su koma zaman din-din-din a wani wuri? inji shi.
Sanabel Alghoul, mai shekaru 28 ta bayyana shirin Trump a matsayin abu mai ''matuƙar haɗari''. Ta ce trump na ganin cewa ' wahalhaunmu, da yunwa, da ɓarna da mace macen da muke fuskanta zai tunzuramu mu haƙura da ƴancinmu a Gaza cikin sauƙi''.
Youssef Alhaddad, wani lauya a yankin Falasɗinawa, ya shaidawa BBC cewa Trump na amfani da tunaninshi na sake gina Gaza a matsayin '' matsin lamba'' da ke da niyyar 'tilastawa ƴan Gaza su bar ƙasarsu ta gado'' wanda ya bayyana hakan a matsayin ''mugunta''.
Wasu Falasɗinawan kamarsu Nevin Abdelal ya ce za su fi so Falasɗinawa da kansu su sake gina yankin, inda ya ce ƴan Gaza za su iya zuwa '' wuraren da zasu iya zama a zirin har sai an gama gyaran, amma babu wanda zai tafi.''










