Su wane ne ƴanjaridar Al Jazeera da Isra'ila ta kashe a Gaza?

Wasu daga cikin ƴanjaridar yayain da suke tsaka da bayar da rahoto
Bayanan hoto, Babban editan Al Jazeera ya bayyana Anas al-Sharif a matsayin jajirtacce
    • Marubuci, Alys Davies
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ƴanjarida biyar na Al Jazeera aka kashe a wani harin Israʼila a birnin Gaza ranar Lahadi - a cikinsu akwai wakilin kafar yaɗa labaran mai shekara 28, Anas al-Sharif, wanda ya ba da rahotanni masu yawa game da yaƙin tun farkonsa.

Haka kuma kafar yaɗa labaran ta ce an kuma kashe sauran mutum biyu a harin.

Harin da aka kai tantin da ƴan jaridar ke amfani da shi ya janyo suka daga daga Majalisar Dinkin Duniya, da kuma Qatar, inda Al Jazeera take, da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ƴanjarida.

Israʼila ta ce Sharif ya "jagoranci wani reshe na ƙungiyar Hamas" amma ba ta kawo wata gamsasshiyar shaida game da hakan ba.

Sharif ya taɓa musanta zargin, kuma Al Jazeera da ƙungiyoyin ƴancin ƴanjarida sun yi watsi da zargin.

Haka kuma wasu daga cikin abubuwan da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta kafin ya mutu, ɗan jaridar ya soki Hamas.

Shugaban kwamitin kare ƴanjarida, Jodie Ginsberg ya faɗa wa BBC cewa babu wata hujja ta kashe Sharif.

Anas al-Sharif: 'Murya ɗaya da ta rage a Gaza'

Anas al-Sharif na sanye da rigar kare ƴanjarida yayin da yake duba wata ɓarna da aka yi a birnin Gaza.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Anas al-Sharif na cikin ragowar mutanen da ke aika rahoto daga birnin Gaza, a cewar Al Jazeera.

Anas al-Sharif ya zama ɗaya daga cikin sanannun wakilan Al Jazeera a Gaza yayin yaƙin.

An haife shi a yankin Jabalia mai yawan mutane, kuma ya yi wa Al Jazeera aiki tsawon kusan shekaru biyu, a cewar kafar yaɗa labaran.

"Ya yi aiki tsawon yaƙin da ake yi a Gaza kuma yakan yi rahoto a kullum game da halin da mutane ke ciki da kuma hare-haren da ake kai wa Gaza," kamar yadda Salah Negm, daraktan kula da yaɗa labarai a sashen Turanci na Al Jazeera ya faɗa wa BBC.

Sharif na da ɗiya ƴar shekara huɗu, Sham, da kuma yaro ɗan shekara ɗaya mai suna Salah, ya rabu da su tsawon lokaci yayin yaƙin daga arewacin Gaza bayan ya ƙi bin umarnin Israʼila na barin yankin.

Wani saƙo da ya wallafa tare da matarsa a Instagram a Janairun shekarar nan ya nuna Sharif yana murmushi tare da ƴaƴansa biyu.

Saƙon ya ce wannan ne karo na farko da ya haɗu da Salah bayan watanni 15 ana yaƙi.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sharif ya fito a labaran kai tsaye da dama, kuma ya yi rahotanni masu yawa game da halin da ake ciki a Gaza.

Ya ba da rahoto game da harin da aka kai kan wakilan Al Jazeera, Ismail al-Ghoul da Rami al-Rafi a wani harin Israʼila a Gaza cikin shekarar 2024.

An kashe mahafinsa a Disamban 2023 lokacin da Israʼila ta kai wani hari gidan iyayensa. Yan saʼoʼi kafin a kashe shi, ya wallafa wani saƙo game da zazzafan harin da Israʼila ke kai wa birnin Gaza.

Babban editan Al Jazeera Mohamed Moawad ya bayyana shi a matsayin "murya ɗaya da ta rage birnin Gaza" - wadda Israʼila ke shirin mamayewa a yanzu.

Babban jamiʼi a Sashen Larabci na Al Jazeera Raed Fakih ya faɗa wa BBC cewa Sharif jajirtacce ne mai kishi da son gaskiya - kuma hakan ne ya sa ya zama sananne mai ɗimbin mabiya a shafukan sada zumunta".

Fakih, wanda shi ne ke kula da ofisoshin kafar, ya ƙara da cewa: "Dagewarsa kan aiki ta kai shi wuraren da sauran wakilai suka kasa kai wa, musamman waɗanda suka ga kashe-kashen kiyashi. Gaskiyarsa ta tsayar da shi a kan aikinsa na jarida."

Fakih ya ce ya yi magana da Sharif lokuta dama dama yayin yaƙin.

"A maganarmu ta ƙarshe, ya faɗa min halin yunwar da yake ciki, da kuma yadda samun abinci ke da wahala."

"Ya ji cewa ba shi da wani zaɓi ban da ya yaɗa muryar ƴan Gaza. Ya yi rayuwar cikin wahalar da suke ciki, ya yi fama da yunwa, kuma ya rasa ƴan'uwansa''.

"Mahaifinsa ya mutu a harin Israʼila, ya zama tamkar sauran mutanen Gaza, ya rayu cikin rashi, ciwo da kuma jajircewa. Kuma kodayake yana fuskantar barazanar mutuwa, ya yi haƙuri, saboda dole ne a ba da labari."

Su wane ne sauran ƴan jaridar da aka kashe?

Wata takarda mai hotunan ƴan jarida Anas al-Sharif, Ibrahim Zaher, Mohammed Noufal, Moamen Aliwa da Mohammed Qreieh a hannun wani mutum.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Yan jaridar na Al Jazeera biyar na cikin bakwai da aka kashe a wani harin Israʼila yayin da suke hutawa a wani tanti na ƴan jarida a birnin Gaza ranar Lahadi, a cewar Al Jazeera.

Mohammed Qreiqeh, mai shekara 33, mahaifi ne yara biyu ne daga birnin Gaza.

Kamar Sharif, Qreiqeh ya rabu da iyalinsa tsawon watanni lokacin yaƙin yayin da yake kai rahoto daga filin daga a arewacin Gaza.

Rahotonsa na ƙarshe shi ne wanda ya yi kai tsaye da yammacin Lahadi, ƴan mintuna kafin a kai masa hari, a cewar Al Jazeera.

Kafar ƴaɗa labaran ta ce an kashe mahaifiyarsa a watan Maris na 2024 lokacin da sojojin Israʼila suka kai farmaki asibitin al-Shifa a birnin Gaza.

Ya samu gawarta bayan ya kwashe mako biyu yana nemanta.

An kuma kashe ɗan'uwansa a wani harin Israʼila a Gaza cikin watan Maris, a cewar Al Jazeera.

Islam Bader: Wakilin Al Araby TV na kawo rahoto daga Gaza, kuma ya ce ya yi aiki da Qreiqeh tsawon shekaru.

A wani saƙo da ya wallafa a Instagram ya bayyana Qreiqeh a matsayin "mutum mai sanyin rai".

Ibrahim Zaher: Mai ɗaukar hoton, mai shekara 25 ma ɗan Jablia ne, a cewar Al Jazeera.

Bader ya kasance ɗanjarida tun farkon yaƙin, kuma mai aikin lafiya na sa kai.

Moamen Aliwa: An bayyana mai ɗaukar hoton a matsayin "mai sauƙin muʼamalla, da taimako da kuma iya magana".

Ya wallafa a Instagram cewa Aliwa ya karanci injiniyanci amma sai ya zama ɗan jarida lokacin yaƙin.

Mohammed Noufal: Wanda shi ma aka bayyana a matsayin mai ɗaukar hoto, kuma direban tawagar, shi ma ɗan asalin Jabalia ne.

Al Jazeera ta ce an kashe mahaifiyarsa da ɗan'uwansa a hare-haren Israʼila lokacin yaƙin.

Mohammed al-Khaldi: Ɗanjaridar mai zaman kansa ya wallafa bidiyoyi da dama a dandalin sada zumunta da ke nuna rayuwarsa da ta sauran mutane a Gaza.

Bidiyonsa na ƙarshe a Instagram cikin ƙarshen mako ya nuna wata yarinya ƴar shekara takwas na fama da yunwa tare da neman mutane su taimaka mata.

Mohammed Qreiqeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mohammed Qreiqeh ya bayar da rahotonsa na ƙarshe ranar Lahdi mintuna kafin kashe shi

Sharif na jagorantar wani reshen Hamas - Isra'ila

Rundunar sojin Israʼila ta zargi Sharif da yin amfani da rigar ƴan jarida, inda ta ce ya yi "aiki a matsayin jagoran wani reshe na Hamas" kuma yana da hannu wajen kai hare-haren makamin roka kan ƴan Israʼila - amma ba ta ba da wata shaida mai ƙarfi kan hakan ba.

A wani saƙo, IDF ta ce tana da takardun da ke nuna "cewa yana da alaƙa ta soji" da Hamas, ciki har da "bayanan mayaƙanta, kwasa-kwasan ba da horo, da kuma lambobin waya, da kuma bayanan biyan albashi".

Ta fitar da wasu bayanai da ke nuna waɗanda aka ce ƴan Hamas ne daga arewacin Gaza, wadda ke nuna rauni da kuma wani ɓangare da ke nuna lambobin waya na bataliyar ƙungiyar a gabashin Jabalia.

Israʼila ta zargi Sharif a baya da kasancewa mamban reshes soji na Hamas - zargin da shi daAl Jazeera suka musanta.

Ƙungiyar kare haƙƙin ƴanjarida ta 'Reporters Without Borders' (RSF), ta bayyana ce zarge-zargen da ake masa a matsayin mara tushe kuma ta yi kira ga ƙasashen duniya su shiga maganar.

Kusan ƴan jarida 200 aka kashe a yaƙin da Israʼila ta ƙaddamar bayan harin Hamas na 7 ga watan Oktobar 2023, a cewar ƙungiyar ta RSF.

Sharif ya san cewa Israʼila za ta iya kai masa hari bayan da mai magana yawunta na Larabci ya wallafa wani bidiyonsa a watan Yuli da ke zargin sa da kasancewa ɗan Hamas.

A wani saƙo da ya wallafa a safinsa na X, wanda ya rubuta ko da a ce ya mutu, Sharif ya ce ya yi "duk wani ƙoƙari kuma na yi duk wani abu na zama muryar mutanenan... Kar a manta da Gaza."